Yadda kura ta turnuke a jam'iyyar NDC a Kano

Asalin hoton, NDC
A jihar Kano, ga alama har yanzu ƙurar da ta turnuƙe a jam'iyyar NDC ba ta lafa, kasancewar babu taƙamaimai cikakken bayani game da matsayar da aka cimma yayin wata ganawar da ƙusoshin jam'iyyar suka yi.
Wannan na zuwa ne bayan da shugabancin jam'iyyar na shiyar arewa maso yamma ya zargi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, da ƙoƙarin ƙwace ragamar jam'iyyar, abin da ya haifar da tattaunawa tsakanin bangarorin biyu, to amma babu tabbas ko an samu fahimtar juna.
Bayanai na cewa korafe-korafe da 'yan tsohuwar NDC din suka gabatar ne yasa aka shiga tattauna tun cikin karshen makon da ya gabata da bangaren Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da wasu shugabannin jam'iyyar don ganin yadda za a warware takaddamar da ta so wadda ke da alaka da batun tsayar da 'yan takara a Kano.
Wani ɗan jam'iyyar ta NDC Hassan Sa'eed daga jihar Jigawa, ya shaida wa BBC cewa an kai korafi ne gaban jagran jam'iyya wato Saraki Dickson, inda wadanda suke ƙorafin ma'ana 'yan tsohuwar NDC suka ce ba a bawa wadanda suke so takara ba
Ya ce," masu ƙorafin sun ce akwai ƴan takarar da suke so a bawa takarar 'yan majalisar wakilai a kananan hukumomin Kano Municipal da Gwale da Kumbotso da kuma Nasarawa, amma ba a basu ba, to shi ne suke cewa a taimaka musu a basu takarar."
" To sanata Dickson ya karbi korafinsu, har ma ya ce zai gana da sanata Rabi'u Musa Kwankwaso domin a samu mafita." In ji shi.
To sai dai a tattaunawar da BBC ta yi da Usaini Isa Mairiga, shugaban jam'iyyar NDC na jihar Kano, ya ce babu wata rigima a cikin jam'iyyarsu a Kano.
Ya ce," Duk wata jita-jita da muka ana yadawa akan rikici a cikin jam'iyyarmu mun je mun zauna da sanata Kwankwaso da shi kansu jagoran jam'iyyar mun warware duk wata matsalarmu."
Wata majiya da BBC ta tuntuba, ta ce bangaren Kwankwaso ba za su bayar da kujera ko daya ba, saboda acewarsu da bazarsu ake rawa kasancewar shigar jagoran Kwankwasiyya ce tasa jam'iyyar ta yi farin jini, inda ta ce idan kuma aka matsa musu za su nemi mafita.











