Tarihin yadda bugun fenariti ya samo asali a wasan ƙwallon ƙafa

Collage of pictures from the Watney Cup 1970 - the matchday programme and action shots from the game

Asalin hoton, Hull City

    • Marubuci, Phil Jones
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sporting Witness
    • Marubuci, Sonia Oxley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport
  • Lokacin karatu: Minti 6

A wani yammacin ranar 5 ga watan Agustan 1970 ne, Manchester United ta kammala wasa ana kunnen doki 1-1 tsakaninta da Hull City, har aka je ƙarin lokaci aka tashi ba wanda ya yi nasara a filin wasa na Boothferry Park a gasar cin kofin Watney.

Bayan makonni shida, mahukunta harkar ƙwallon ƙafa suka yanke shawarar fitar da wanda zai yi nasara, ta hanyar zaɓar ƴanwasa biyar daga ko wane kulob, domin su yi bugun tazara daga mita 11, daga su sai mai tsaron ragar da zai yi ƙoƙarin bugewa.

"Blimey," in ji wani magoyi bayan Hull City. "Georgie Best. Shi ne mutum na farko da zai fara buga fenaritin".

Wannan wasar ta cancanci a kalle ta.

Babu wanda ya san cewa wannan matakin zai zama mizanin yanke hukuncin wasa, idan aka shiga yanayin sarƙaƙiyar da ba ko wane magoyi baya ne zai iya kalla ba.

Hull City and Manchester United in action in their Watney Cup semi-final

Asalin hoton, Hull City

Kafin wannan lokacin, ana yanke hukunci kan wasar da aka gaza samun wanda ya yi nasara ne hanyar sake buga wasar ko kuma a jefa ƙwandala.

A lokacin gasar cin kofin nahiyar Turai a shekarar 1968, Italiya ta tsallaka zuwa wasan ƙarshe bayan an yi kacici-kacici sakamakon tashi 0-0 da Tarayyar Soviet. A wasan ƙarshe da Yugoslavia kuma an tashi da ci 1-1 inda a ƙarshe Italiya ta yi nasara da ci 2-0 bayan kwanaki biyu inda ƙungiyoyin suka sake fafatawa a wasar.

Ga waɗanda ba su goyon bayan hanyoyin da ake bi don warware irin wannan sarƙaƙiya, a kan ɗauki tsawon watanni huɗu kafin sanin matsaya.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ran hukumomin wasannin Isra'ila ya ɓaci a lokacin da kyaftin ɗinta ya ɗauki takardar rashin nasara a lokacin da aka yi canki-canki da ta sa suka rasa damarsu a wasan kwata fainal a gasar Olympic a shekarar 1968, bayan da suka tashi wasa 1-1 tsakaninta da Bulgaria.

Wani jami'in hukumar wasannin Isra'ila Yosef Dagan, ya ce ya kamata a samu wata hanya da ta fi wannan wajen yanke hukunci kan lokuta masu sarƙaƙiya irin wannan, wanda ba zai dogara da sa'a ba.

Bayan da Dagan da Michael Almog suka zama shugabannin hukumar wasannin Isra'ila ne suka aika wasiƙar buƙatar gabatar da tsarin bugun fenariti zuwa ga hukumar wasanni ta duniya Fifa a shekarar 1969. An wallafa wasiƙar a mujallar hukumar.

A cikin wasiƙar, Almog ya ba da shawarar "dakatar da wannan hanyar yanke hukuncin wanda ya yi nasara ta hanyar kaɗa kuri'a, da bai dace ba kuma rashin adalci ne ga ƙungiyar da ta yi rashin nasara kuma babu ƙima ga wadda ta yi nasara".

Ya ɓukaci a sauya tsarin da bugun fanareti da ƴanwasa biyar daga kowanne bangare. Idan aka yi hakan ma ba a samu ƙungiyar da suka yi nasara ba, to za a ci gaba har sai ɗaya daga cikinsu ya yi rashin sa'ar zura ƙwallo.

An tafka muhawara mai zafi game da wannan shawarar kafin daga bisani ƴan majalisar hukumar ƙwallon kafar ta duniya irinsu Ifab suka amince da ita, a taronta na shekara-shekara a Inverness a ranar 27 ga Yuni 1970.

Baya ga kaɗa kuri'a, ko jefa ƙwandala ko sake buga wasa, akwai wasu hanyoyin da ake amfani da su tun da daɗewa, da suka haɗa da lissafa yawan bugun ƙusurwa, ko kuma kyaututtukan da kowane kulob ya samu, duk da yake ana bugun fenariti a wasu ƙananan wasanni a lokacin.

BBC ta tuntuɓi Fifa domin ta tabbatar da ko bugun fenariti da aka yi a gasar Watney shi ne karo na farko a hukumance, ta ce "ba za ta iya tabbatar da hakan ko musanta iƙirarin ba".

Sai dai hukumar adana bayanan tarihin ƙwallon ƙafa tana lissafa wannan a matsayin bugun fenariti na farko a Birtaniya.

A yawancin gasa daban-daban, ciki har da gasar cin kofin FA sai da aka shafe kakar wasanni biyu ana amfani da tsarin sake buga wasa. Sai a 1990-91 ne gasar FA ta gabatar da bugun fenareti idan kungiyoyin suka kasa yin nasara bayan karin lokaci a karawar.

Bayan wannan hukuncin na Ifab a 1970, ba a daɗe ba sai aka sami dama ta farko da aka yi amfani da bugun fanariti don yanke shawarar wasa irin wannan.

Shin wanda ya samu nasara a jefa ƙwandala zai ji daɗi?

Wannan wasar cin kofin Watney da aka buga da Hull, ita ce amsar.

Black and white action shot of Ian Butler scoring Hull City's second penalty in the Hull City v Manchester United Watney Cup match in 1970

Asalin hoton, Hull City

"Na kasa yarda cewa kulob ɗi na Hull City ne suka yi nasara a kan irin su Georgie Best, Bobby Charlton da Denis Law. Hakan na nufin kamar fafatawa ne da irinsu Messi, Ronaldo da Mbappe a kulob ɗaya," Kelly yana tuna yadda ya kalli wasar a hirarsa da BBC.

Tsohon ɗanwasan Hull City, Frankie Banks, ya ce: "Wasa ce babba, bugawa da Manchester United, wadda shekaru biyu da suka gabata ta lashe kofin Turai."

"Yanayi ne mai cike da shauƙi"

Ƴanwasan Man United su ne zakarun mu. Duk ba su yi nasara a kacici-kacici ba. Mun so mu yi nasara, mun so nuna wa duniya cewa duk a su ne shahararru amma kuma za mu iya fafatawa da su,"

Wannan kuma shi ne abin da suka yi, sun mamaye wasar tun a mituna 11, kafin daga bisani a cire ɗanwasan United a mintuna na 78, inda har aka je ƙarin lokaci. Bayan da aka shafe wasu mintuna 30 ne ƴanwasan suka gane cewa za su kafa sabon tarihi.

An buƙaci ƴanwasan su fara bugawa amma kowa yana ja da baya, domin babu wanda yake da ƙwarin gwiwar zai iya ci.

"Babu wanda ya ke so ya yi rashin nasara"

Kuma, babu wanda ke son zama ɗan wasa na farko da ya taɓa rasa bugun na fenariti.

Sai dai duk da haka, Best ya ce bari ya fara gwadawa inda ya kuma ci.

A Hull City kuma, Neill ne ya fara bugawa inda ya sa wasar ta koma 3-3.

Sakamakon yadda ake fafatawa da manyan ƴanwasa da suka shahara, Law daga United ya buga ƙwallo a hankali, inda Ian McKechnie ya buge.

"A tarihi ba za a taɓa mancewa da Law a matsayin mutum na farko da ya fara ɓarar da bugun fenariti, shi kuma McKechnie za zama gola na farko da ya fara buge fenariti," in ji Banks

Shi ma Ken Wagstaff da Hull ya ɓarar inda Willie Morgan ya ci wa United, inda kuma wannan ita ce damar bugu ta ƙarshe ga Hull.

A wannan lokacin ne McKechnie ya tashi zai buga, inda ya zama gola na farko da ya buga fenariti.

"Dan Allah kada ya buga," Kelly yake tuna abin da ya faɗa. "Na kasa yarda, mahaifiya ta ma ta kasa yarda, shi kansa Alex Stepney, kocin Man United yana mamakin me ya kai shi wajen. Ɗora hannu a kai kawa na yi!"

McKechnie kuwa ya buga ƙwallon da karfi... inda ta fita waje. Hakan ya sa ya zama gola na farko da ya fara ɓarar da bugun fenariti.

"Har yanzu ina ganin Ian McKechnie a matsayin zaɓi mai kyau. Ƙwallo ta zauna ƙafar sa kuma yana da ƙwarin gwiwar bugawa. Na sa kuɗi na a kan shi," in ji Banks.

"Ɓarar da bugun fenaritin zai kasance a tarihinsa har ƙarshen rayuwarsa."

Black and white photo shows goalkeeper Ian McKechnie diving to his right

Asalin hoton, Hull City

Tabbas, akwai irinsu Laws da McKechnies da yawa tun lokacin. Hasali ma, alƙaluma sun ce kashi 24 cikin 100 na fanareti an ɓarar da su.

Bugun Fenariti ta sasanta wasu manyan gasa, har a gasar cin kofin duniya an yi bugun fanareti sau uku a wasan ƙarshe - a 1994, 2006 da 2022.

Babbar gasar duniya ta farko da aka yanke hukunci a bugun fanareti ita ce Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai a 1976 - inda aka yi wa bugun wa lakabi da Antonin Panenka.

A cikin shekaru da dama, ƴan Ingila sun sha wahala sosai a bugun fenariti, inda suka yi rashin nasara sau bakwai a manyan gasa ta wannan hanyar.

Kwanaki biyu da suka gabata, Bosnia-Herzegovina ta kawo ƙarshen fatan Wales na taka leda a gasar cin kofin duniya ta bana bayan da aka yi bugun fanareti.

Kafin ranar wasan Hull, babu wanda ya yi tunanin abin da zai faru kenan.

"Ko wacce bugun fenariti akwai fargaba," in ji Kelly

Sama da shekaru 60 kenan, har yanzu ana amfani da wannan tsari.