Me ya sa manyan ƙungiyoyin Ingila ke shan wahala a hannun 'ƙanana'?

Wasu fitattun ƴanwasan manyan ƙungiyoy

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 4

Har yanzu magoya bayan Manchester United na cikin alhinin rashin nasara da ƙungiyar ta yi a wasanta da Leeds United ranar Litinin da maraice.

Nasarar da Leeds ta samu da ci 2-1 ta sa ƙungiyar ta koma ta 15 a kan teburin Premier.

Wannan ce nasara ta farko ta Leeds ta samu kan United a Premier tun shekarar 2002, kuma ta farko da ta samu a Old Trafford tun 1981.

Kocin ƙungiyar Daniel Farke ya bayyana wa manema labarai irin farin cikin da ya ji sakamakon nasarar.

A wata hira da Sky Sports, Farke ya ce "wannan ne karon farko da muka ci United a gidansu cikin shekara 40, tabbas wannan babbar nasara ce''.

Illar da ƙananan ƙungiyoyi ke yi wa manyan

Declan Rice

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A ƙarshen mako ne Arsenal ta sha kaye a hannun Bournemouth da ci 2-1

A lokuta da dama manyan ƙungiyoyin Ingila kan sha kaye a hannun ƙananan ƙungiyoyi.

Ko a ƙarshen mako Arsenal - wadda ke kan teburin gasar Premeir - ta sha kaye a hannun Bournemouth da ke mataki na 11 a kan teburin.

Ga kuma ƙungiyar Tottenham da a bana ke cikin barazanar faɗuwa daga gasar Premier League.

Ko a watan Agustan 2025 ma wata ƙaramar ƙungiyar Grimsby Town FC da ke buga gasar League mai daraja ta huɗu a Ingila, ta fitar da United daga gasar Carabao a bugun fenareti.

Anas Sani Tukuntawa Ɗanjarida mai sharhin wasanni a jihar Kano da ke Najeriya ya bayyana dalilan da ke sanya manyan ƙungiyoyi shan wahala a hannun ƙanana a Ingila.

Amfani da salon wasa ɗaya

Bruno

Asalin hoton, Getty Images

Anas Tukuntawa ya ce matsalar daga masu horas da manyan ƙungiyoyin ne.

''Galibi masu horas da manyan ƙungiyoyin salo ɗaya kawai suka iya amfani da shi a duka wasanninsu, wannan ya sa ƙananan ƙungiyoyin ke saurin gane dabararsu'', in ji shi.

Ya bayar da misali da kocin Manchester United Michael Carrick, wanda a cewarsa salon wasan gudu kawai yake amfani da shi.

''Sannan shi kuwa Mikel Arteta salon tiki-taka kawai ya iya, kodayake wani lokaci yakan yi amfani da salon gudu, to wannan na taimaka wa ƙananan ƙungiyoyin gano su da wuri'', in ji shi.

Ƙwarewar ƴanwasan ƙananan ƙungiyoyin

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Anas Tukuntawa ya kuma ce wani dalilin shi ne ƙwarewar wasu ɗaiɗaikun ƴan wasa a ƙananan ƙungiyoyin.

''Premier, gasa ce da ta fita daban tsakanin takwarorinta gasannin Turai, a Premier ne za ka samu ɗan wasa ɗaya da ke bugawa a wurare daban-daban a cikin fili'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

Ɗanjaridar ya bayar da misali da ɗan wasan Brighton & Hove Albion, Fabian Hürzeler da ya ce yana iya buga salo daban-daban a cikin fili da suka haɗa da tiki-taka da gudu da kuma saka ƙarfi, sannan kuma ƙungiyarsa ta ƙware a salon tiki-taka da na gudu.

''Haka ma idan ka ɗauki Andoni Iraola na Bournemouth, wanda in dai gudu ne in ya zari ƙwallo to sai an yi da gaske, haka kuma idan ana salon tiki-taka nan ma sai ka bar shi'', in ji shi.

Anas tukuntawa ya kuma bayar da misali da ƙungiyar Brentford, wadda ya ce tana da ƙwarewa a duka salon wasannin tiki-taka da na gudu, inda kuma hakan yake taimaka mata, idan ta haɗu da ƙungiyoyin da ba su iya ɗaya daga cikin waɗannan salailai ba.

Virgil van Dijk

Asalin hoton, Getty Images

Yawan sauya masu horaswa

Wani ƙarin dalilin a cewar Anas Sani Tukuntawa shi ne yawan sauya masu horaswa da manyan ƙungiyoyin ke yi.

Galibi dai manyan ƙungiyoyin kan sauya masu horaswa idan suka fara fuskantar matsaloli, duk da cewa wasu lokutan ma matsalar ba ta masu horaswa ba ce.

Ɗanjaridar ya bayar da misali da ƙungiyar Tottenham, wadda ya ce ta sauya masu horaswa da yawa a baya-bayan nan.

''Tun bayan Mauricio Pochettino da ya shekara uku a ƙungiyar, an kawo José Mourinho, shi ma ya kasa taɓuka abin kirki, aka kawo Antonio Conte, wanda shi ma bai yi wani ƙoƙari ba aka sallame shi''.

Ricalisson

Asalin hoton, Getty Images

''Bayan Conte aka ɗauko Ange Postecoglou, duk da shi ya ci Europa an sallame shi, aka kuma ɗauki Nuno Espírito Santo, shi ma dai ba-ta-canza-zani ba, aka ɗauko Thomas Frank, wanda shi kuma yanzu ka ga halin da ƙungiyar ke ciki'', kamar yadda ɗanjaridar ya bayyana.

Yanzu haka dai Tottenham na matsayi na 18 a kan teburin Premier da maki 30 yayin da ya rage wasa shida a ƙarƙare gasar.