Mene ne kalaman ɓatanci, mene ne kuma hukuncinsa a addinin Musulunci?

An sha samun yanayin da ya janyo aka kashe wasu mutanen bisa zarge-zargen sun furta kalaman ɓatanci ga Annabi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An sha samun yanayin da ya janyo aka kashe wasu mutanen bisa zarge-zargen sun furta kalaman ɓatanci ga Annabi
    • Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 5

A Najeriya ana yawan samun yanayin da jama'a ke zargin wasu da furta kalaman ɓatanci mafi yawanci ga Annabi Muhammad (S.A.W) ko kuma ma ga addinin musulunci.

Ko a makon nan, an ga wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta inda a cikinsa akwai cincirindon matasa da ke zanga-zanga domin nuna ɓacin rai game da abin da suka zarga da ɓatanci ga Annabi da wani matashi ya yi.

Bidiyon ya nuna yadda suke ta neman a ɗauki matakin a mutumin ko kuma su ɗau mataki da kansu.

A baya ma an sha samun yanayi irin wannan da ya janyo aka kashe wasu mutanen bisa zarge-zargen sun furta kalaman ɓatanci ga Annabi.

Hakan ne ya sa BBC ta yi nazari kan haƙiƙanin abin da kalaman ɓatanci ke nufi a addinin musulunci, sannan wane hukunci aka tanadar ga wanda ake zargi da furta kalaman. Kuma wane ne ya kamata ya zartar da hukuncin?

Ma'anar kalaman ɓatanci a addinin Musulunci

Sheikh Mansur Ibrahim Sokoto, sanannen malamin addinin Islama ne kuma Farfesa a fannin Hadisi a Jami'ar Usman Danfodiyo ya yi wa BBC cikakken bayani kan kalaman ɓatanci.

"Abin da ake nufi da kalaman ɓatanci a addinin Musulunci shi ne izgili, ko nakasawa ko habaici ko jingina duk wasu kalamai da za su rage matsayi ko keta mutunci da alfarmar Ma'aiki S.A.W.."

Shehin Malamin ya ƙara da cewa ko a al'adance duk abin da gama garin mutane suka ɗauke shi a matsayin zagi, "idan mutum ya yi wa annabi SallalLahu Alaihi Wasallam, za a ɗauke shi a matsayin ɓatanci"

Siffofin kalaman ɓatanci

Sheikh Mansur Sokoto
Bayanan hoto, Farfesa Mansur Sokoto
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Akwai sarƙaƙiya a kan yadda mutane suke fahimtar kalamai na ɓatanci, lamarin da ya sa a wasu lokutan ake jirkita maganar wani mutum sai a ayyana su a matsayin na ɓatancin.

Farfesa Mansur ya ce Sheikh Alqadi Iyadh mai As-Shifa ya lissafa abubuwa guda 20, waɗanda duk mutumin da ya aikata ɗaya daga ciki, za a iya aiwatar da hukuncin ɓatanci a kansa.

"Duk wanda ya zagi manzon Allah - zagi ɓaro-ɓaro kenan - ko ya aibanta shi, ko ya riskar da wata tawaya ga halittarsa, wato ya yi suka ga halittarsa, ko cikin nasabarsa wato dangatakarsa ta iyayensa da kakanni, ko kuma ga addininsa, ko wata ɗabi'a daga cikin ɗabi'unsu, ko ya la'ance shi, ko ya yi masa ɓakar addu'a, ko ya yi wata fatar wata cuta ta samu manzon Allah, ko ya jingina masa wani abin da bai dace da matsayinsa ba."

Haka kuma za a iya zartar da hukuncin kalaman ɓatanci ga duk wanda ya "jefa masa wani zargi, ko ya munana magana a gare shi, ko ya shammace shi a kan wata cuta da same shi ko wani abu, ko ya soke shi game da wani da yake faruwa da mutane," in ji Sheikh Mansur.

Hukuncin wanda ya furta kalaman ɓatanci

Kai tsaye malaman musulunci sun yi ijma'i a kan cewa duk wanda ya yi ɓatanci ga manzon Allah S.A.W, "ya kafirta idan Musulmi ne", kamar yadda Sheikh Alqadi Iyadh ya bayyana a cikin littafin As-Shifa da kuma Shaykh-ul-Islam Ibn Taymiyyah a cikin littafin As-sarimul Maslul, in ji Sheikh Mansur Sokoto.

"Idan kuma "kafiri" ne [wanda ba musulmi ba], to babu amana tsakaninmu [Musulmi] da shi," in ji shi.

Farfesan ya ce a tsarin shari'ar musulunci za a yanke wa duk wanda ya aikata kalaman ɓatanci ga Allah da ManzonSa hukuncin kisa.

"Zagin Allah da Manzon Allah duk hukuncin su ɗaya ne, shi ne kisa. Wannan shi ne ƙarshen hukunci a dokar shari'ar musulunci," in ji Farfesa Mansur.

Ya ƙara da cewa: "Za a iya kwatanta shi [kalaman ɓatanci] da juyin mulki ga gwamnati. Shi ne ƙarshen laifin da za ka yi wa gwamnati".

Ana iya tuba idan aka yi kalaman ɓatanci?

A taƙaice duk wanda ya zagi manzon Allah ɓaro-ɓaro da hujjoji bayyanannu, za raba shi da duniya "kamar yadda gwamnati take raba duk wanda ya yi yunƙurin juyin mulki da duniya", in ji Sheikh Mansur.

Malamai sun ce zagin Allah, laifi ne babba kuma kafirici a fili, amma zagin manzon Allah kafirci ne da ƙari.

"Allah ya shelanta cewa duk abin da ka yi idan ka roƙe shi zai yafe maka, amma tun da manzon Allah ba ya raye, al'umma ba za su iya yafe masa ba," saboda haka malamin ya ce idan har mutum ya aikata laifin sai an zartar masa da hukunci.

Farfesa Mansur ya ƙara da cewa idan hukunci ya tabbata mutum ya yi kalaman ɓatanci ga manzon Allah, za a ba shi damar ya musulunta idan ba musulmi ba ne.

"Idan kuma Musulmi ne za a umurce shi ya tuba, amma dole a zartas masa da hukuncin [kisa]."

Wane ne ke da alhakin zartar da hukunci?

Sai dai Farfesa Mansur Sokoto ya ce addinin musulunci bai amince mutane su zartar da hukuncin kisa dan an ce mutum ya yi kalaman ɓatanci ba.

Ya ce dole sai an gabatar da mutum ga hukumomi sannan an gabatar da gamsassun hujjoji da za su tabbatar da mutum ya aikata abin da ake zargi.

"Addinin musulunci bai yarda gama garin mutum ya ɗauki doka a hannu ba," in ji Farfesa Mansur.

"Shari'a abin da ta ce a tabbatar da laifi, sannan masu zartaswa su aiwatar".

Farfesan ya ce hakan zai yiwu ne kawai idan hukumomi suna zartar da hukuncin da ya dace kan mutanen da suka aikata laifin mutane za su samu natsuwar an musu adalci.

Kalaman ɓatanci a dokokin Najeriya

A tsarin dokokin Najeriya, kalaman ɓatanci ga addini laifi ne babba, amma hukuncinsa ya dogara da nau'in kotu da kuma yankin da laifin ya faru saboda kasar tana amfani da tsarin dokoki har guda uku.

Akwaia dokar Gwamnatin Tarayya (Criminal Code), dokar Shari'ar Musulunci (Shari'ah Penal Code), da kuma Kundin Tsarin Mulki.

Sashe na 38 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 ya bai wa kowane ɗan ƙasar ƴancin yin addinin da yake so. Sashe na 39 kuma ya ba da ƴancin fadin albarkacin baki.

Sai dai, waɗannan ƴanci suna da iyaka domin dokar ba ta amince mutum ya yi amfani da damarsa wajen rura wutar gaba, barazana, ko cin zarafin addinin wasu da zai iya kawo ruɗani a cikin al'umma ba.

Barista Hamza Nuhu Dantani, ƙwararren lauya ne a Najeriya, ya shaida wa BBC cewa dokar Najeriya ta ayyana duk wasu kalamai da za su ƙasƙantar da wani ko wulaƙanta abin da ya aminta da shi a matsayin abin bauta ko addininsa a matsayin kalaman ɓatanci.

"Dokar Najeriya ta tanadi hukunci mai tsauri kan kalaman ɓatanci, musamman abin da ya shafi addini," in ji shi.

Barista Dantani ya ce sashe na 399 na Penal Code ya ayyana hukuncin ɗaurin shekaru biyu zuwa uku.

Shi ma sashe na 204 na dokar Criminal Code da ake amfani da shi a kudancin Najeriya ya tanadi irin waɗannan dokoki da suka shafi ƙasƙantar da addini ko abin bautar wasu mutane, in ji Baristan.

Sai dai ya ce babu wasu dokokin Najeiriya da suka ayyana zartsa da hukuncin kisa kan mutumin da ya furta kalaman ɓatanci.