Labarai da dumi-dumi, Masar ta kai zagayen yan 16 bayan doke Australia a bugun fenariti, Bugun Fenariti - Australia 2-4 Egypt

Asalin hoton, Getty Images
Masar ta kai zagayen yan 16, bayan da ta fitar da Australia a bugun fenariti.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya
Daga Ibrahim Yusuf Mohammed, Muslim Muhammad Yusuf da Ahmad Kabo Idris.

Asalin hoton, Getty Images
Masar ta kai zagayen yan 16, bayan da ta fitar da Australia a bugun fenariti.
Wata kotu a Birtaniya ta yanke wa wasu ‘yan ƙasar Romania hukuncin ɗaurin kurkuku bayan an same su da laifin daɓa wa wani ɗanjarida wuƙa a madadin Iran.
Rahotanni sun bayyana cewa mutanen biyu sun kai hari kan Pouria Zeraati a birnin London a watan Maris 2024, lamarin da ya sa aka sai da aka ɗinke masa raunuka uku a ƙafarsa.
Zeraati na aiki ne da tashar Iran International, kafar yaɓa labarai ta harshen Farisanci wadda ke sukar gwamnatin Tehran.
Kotun ta ce an shirya harin tun kusan shekara guda kafin aiwatar da shi, inda aka riƙa bibiyar gidan Zeraati da ke yankin Wimbledon a hankali domin tattara bayanai.
Daga bisani, an yanke wa ɗaya daga cikin maharan hukuncin shekaru 12 a gidan yari, yayin da ɗaya kuma aka yanke masa shekaru takwas.

Asalin hoton, Getty Images
Kotun ɗaukaka ƙara a Najeriya ta soke hukuncin da babbar kotun jihar Oyo ta yanke, wanda ya bai wa ɗalibai mata Musulmi damar sanya hijabi a makarantar International School Ibadan (ISI) ta Jami'ar Ibadan.
Kotun ta yanke hukuncin ne a ranar Juma'a, inda alƙalai biyu suka goyi bayan soke hukuncin, yayin da alƙali ɗaya ya nuna rashin amincewa.
Shari'ar ta samo asali ne tun a shekarar 2018, bayan makarantar ta hana ɗalibai mata Musulmi sanya hijabi tare da kayan makaranta.
Ɗalibai 11, tare da goyon bayan ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi MURIC, suka shigar da ƙara kan zargin take musu ƴancinsu na addini.
A ranar 22 ga Mayun 2024, babbar kotun jihar Oyo ta yanke hukuncin cewa hana sanya hijabi ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya, tun da makarantar na ƙarƙashin gwamnati ne. Sai dai makarantar ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin.
Da yake karanta hukuncin, Mai shari'a Biobele Georgewill ya ce makarantar ISI ba makarantar gwamnati ba ce, makaranta ce mai zaman kanta.
Ya kuma bayyana cewa hukuncin da Kotun Ƙoli ta yanke kan sanya hijabi a makarantun gwamnati na jihar Legas bai shafi makarantu masu zaman kansu ba.
Kotun ta kuma ce ɗaliban sun amince da dokokin makarantar, ciki har da tsarin shigar makaranta, lokacin da suka rattaba hannu kan takardar bin ƙa'idojin makarantar.
Sai dai ɗaya daga cikin alƙalan, Mai shari'a Fadawu Umar, ya nuna rashin amincewa da hukuncin, yana mai cewa ya kamata a bar hukuncin babbar kotu ya ci gaba da aiki.

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa matsalar jin-ƙai na ƙara taɓarɓarewa a arewacin Sudan, yayin da yaƙin basasar ƙasar ke ci gaba da ƙamari.
Babban Kwamishinan Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da kare haƙƙin ɗan Adam, Volker Türk, ya ce hare-haren da ɓangarorin da ke yaƙi ke ci gaba da kai wa juna sun sa hanyoyin shiga birnin El Obeid suka zama masu haɗari.
Ya ce hare-haren, haɗe da ƙarancin man fetur, sun jefa fararen hula cikin mawuyacin hali, inda suke fuskantar matsaloli wajen samun ruwan sha da sauran muhimman buƙatun yau da kullum.
Volker Türk ya yi kira ga ƙasashen duniya da su ɗauki matakin gaggawa domin taimakawa wajen shawo kan matsalar.

Asalin hoton, Aminu Dahiru Ahmad
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, ya sake jaddada cewa yana nan daram a jam'iyyar mai mulki, yana mai cewa shi ba ɗan siyasar da ke yawo daga wannan jam'iyya zuwa wata ba ne domin biyan bukatun kansa.
Tsohon gwamnan jihar Kano ya bayyana haka ne yayin da yake musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke ikirarin cewa ya koma jam'iyyar ta New Democratic Congress (NDC).
A wata sanarwa da tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Kano kuma tsohon shugaban ma'aikatansa, Muhammad Garba, ya fitar a madadinsa ranar Juma'a, Ganduje ya ce hotunan da ake yaɗawa na ƙage ne da aka shirya domin yaudarar jama'a, da tayar da rudani a tsakanin magoya bayan APC.
Sanarwar ta ce Ganduje ya kasance mai tsayawa kan akidarsa ta siyasa, kuma bai taɓa tunanin ficewa daga jam'iyyar APC ba, wadda ya taba jagoranta a matsayin shugaban jam'iyyar na ƙasa.
"Ba gaskiya ba ne, kuma babu wata hujja ta siyasa ko ta hankali da za ta nuna cewa Ganduje ya koma jam'iyyar NDC" a cewar sanarwar.

Jami'an gwamnatin Taliban da kuma shugabannin 'yan adawar Afghanistan sun halarci jana'izar Ali Khamenei a birnin Tehran na ƙasar Iran.
Kafofin yaɗa labarai na Iran sun wallafa hotunan shugaban ƙungiyar ƴan turjiya ta National Resistance Front of Afghanistan, Ahmad Massoud, da shugaban jam'iyyar haɗin kan Musulmin Afghanistan, Mohammad Mohaqiq, yayin da suke yi wa Ali Khamenei da iyalansa ta'aziyya.

Asalin hoton, IRNA
Tawagar wakilan gwamnatin Taliban ƙarƙashin jagorancin mataimakin firaminista Abdul Ghani Baradar Akhund da ministan harkokin wajen ƙasar Amir Khan Muttaqi, ita ma ta halarci masallacin da ake gudanar da jana'izar domin girmama marigayin.

Asalin hoton, IRNA
A gefe guda kuma, mataimakin ministan harkokin wajen Saudiyya, Walid Al-Khuraiji, tare da tawagarsa, sun halarci wajen jana'izar a Tehran domin miƙa ta'aziyyarsu.

Asalin hoton, District Administration Sherani
Aƙalla mutum 32 ne suka mutu, yayin da wasu 16 suka samu raunuka, bayan wata motar bas mai dauke da fasinjoji da dama ta faɗa cikin wani kwari a yankin kudu maso yammacin Pakistan.
Motar na kan hanyarta daga Quetta zuwa Peshawar ne lokacin da ta yi hatsari a yankin tsaunukan Dana Sar, wanda ke kan iyakar jihohin Balochistan da Khyber Pakhtunkhwa.
Wani jami'in gwamnati a asibitin Zhob ya shaida wa BBC cewa, mutane bas ɗin naɗauke da 48— ciki har da mata da yara ƙanana—a lokacin da hatsarin ya auku.
Ana ci gaba da binciken musabbabin hatsarin, amma rahotannin farko na nuna cewa motar ta ƙwace wa direban ne a lokacin da ya ke ƙokarin saukowa daga kan tsaunin.
Hotunan wurin da lamarin ya faru sun nuna yadda motar ta lalace matuƙa bayan ta faɗa kasan kwarin.
Jami'ai sun tabbatar da cewa an kai waɗanda suka ji rauni zuwa asibitin hedikwatar gundumar da ke Zhob, kimanin kilomita 68 daga wurin da hatsarin ya faru.
An kuma kai gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibiti, kuma bayan an tantancesu, za a kai su garuruwansu ta motar daukar marasa lafiya.

Asalin hoton, Dikko Radda/FB
Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ya sha alwashin sallamar duk wani ma'aikaci da aka samu ya na amfani da takardun bogi.
Gwamnan ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi a wajen wani taro da ya gudana a jihar, inda ya ce idan aka bar irin waɗannan ma'aikatan, musamman a fannin ilimi, za a ɓata jihar da mayar da ita baya.
Ya ce ba zai ɗaga ƙafa wajen aiwatar da wannan mataki ba, ko da mutum zai "zaɓi Fir'auna" ne a madadinsa.
"Wanda ya yi cuwa-cuwar takarda aka ɗauke shi aiki, ba shi ba aiki...siyasa kuma idan ya ga dama ya je ya zaɓi Fir'auna," in ji Gwamna Radda.
"In ba da ka da takarda aka kore ka aiki sai me?...ko gobe muka kama wanda ba shi da takarda korar shi za mu yi".
Cikin wani gajeren bidiyo da Katsina Post ta wallafa a shafin Facebook, Radda ya mayar da martani kan abin da ya kira "siyasantar da sha'anin ilimi" da wasu ke yi a jihar.
Kalamansa na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da ƙorafi kan abin da suka bayyana yawan gudanar da ayyukan tantance ma'akata a jihar tun bayan hawan gwamnan.

Asalin hoton, Reuters
Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta sanar da cewa an fara gwajin maganin nau'in ƙwayar cutar cutar Ebola mai saurin kisa da ke ta ɓarke a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
An yi wa majiyyaci na farko rajista a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, in ji shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus a ranar Alhamis.
An tabbatar da cewa cutar ta kama sama da mutum 1,400 da kuma mutuwar mutane 438 a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo.
A cewar WHO, babu alluran rigakafi ko magani da aka amince da su ga nau'in ƙwayar cutar Bundibugyo, wadda ke da saurin yaɗuwa.
WHO ce ke ɗaukar nauyin gwajin na yanzu a ƙarƙashin kulawar masana kimiyya a na cibiyar binciken magunguna ta 'Institut National de Recherche Biomédicale' da ke Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo, da cibiyar sarrafa magunguna ta ƙasar Belgium, da kuma Jami'ar Oxford da ke Burtaniya.
An samu ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo ne a watan Mayu, kuma WHO ta ayyana ta a matsayin bala'in lafiya da ke buƙatar kulawar gaggawa.

Asalin hoton, IRNA
Mataimakin shugaban majalisar tsaro ta Rasha kuma tsohon shugaban kasar, Dmitry Medvedev, ya isa birnin Tehran domin halartar jana'izar Ali Khamenei, tsohon shugaban addinin Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
Nasser Hemmati, Gwamnan Babban Bankin Iran, ya tarbe shi a filin saukar jirgin sama na Imam Khomeini.

Asalin hoton, Kano Pillars/X
Hukumar gudanarwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta naɗa Daniel Ogunmodede a matsayin sabon kocin ƙungiyar gabanin fara kakar wasa ta 2026/2027 a gasar firimiyar Najeriya.
A cewar sanarwar da daraktan yaɗa labaran ƙungiyar Isma'el Abba Tangalash ya fitar a ranar Juma’a a Kano, ƙungiyar ta naɗa Ogunmodede—wanda aka fi sani da “Ijaball”—domin ya jagoranci harkokin ƙungiyar yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen sabuwar kakar wasa.
Sanarwara ta ƙara da cewa, wannan naɗin na daga cikin tsarin sake fasalin da ake gudanarwa domin inganta rawar da ƙungiyar ke takawa a gasannin cikin gida da na nahiyar.
Ogunmodede, tsohon kocin ƙungiyar Remo Stars, ya maye gurbin Muhammad Babaganaru.
Kano Pillars dai ta kammala kakar wasan da ta gabata a matsayi na 15, inda ta tara maki 48 daga wasanni 38.

Bayan da babbar kotun tarayya a Najeriya da ke zama a Abuja ta tabbatar da shugabancin jam'iyyar hamayya ta ADC, ƙarƙashin tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark, ɗayan ɓangaren da ke jayayya a ƙarƙashin Nafiu Bala ya bayyana cewa har yanzu suna ƙalubalantar shugabancin na Mark a gaban kotu.
Da yake mayar da martani kan hukuncin kotu na baya-bayan nan, Nafi'u Bala Gombe ya shaida wa BBC cewa za su ci gaba da ƙalubalantar shugabancin David Mark a gaban kotu kasancewar suna jayayya game da sahihancin kasancewar su halastattun ƴan jam'iyyar.
Jam'iyyar ADC, wadda a baya manyan ƴan adawar ƙasar suka zaɓa a matsayin wadda za su yi amfani da ita domin ƙalubalantar jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen ƙasar na 2027, ta faɗa cikin ruɗani tun bayan da wani ɓangare ya fara ƙalubalantar shugabancin David Mark.
Lamarin ya kai har kotun ƙoli, inda kotun ta yi watsi da wani hukuncin kotun ɗaukaka ƙara wanda ya buƙaci hukumar zaɓe da ta daina amincewa da shugaban na Mark, tare da buƙatar a koma babbar kotun tarayya domin ci gaba da shari'a ta farko da aka shigar.
Sai dai hukuncin da kotu ta yanke a ranar Alhamis ya girgiza ɓangaren Nafiu Bala, bayan da kotu ta kori shari'ar da Leke Ajibade ya shigar.
A martanin nasa, Bala ya ce ''Mu halastattun shugabancin jam'iyya ba mu san da wannan ba, kuma muna da ƙarar da ke ƙalubalantar wannan, da kuma sahihancin cewa ba ƴaƴan jam'iyya masu rajista ba ne,'' in ji shi.
A hukuncin da kotu ta yanke, mai shari'a Musa Liman ya ce rikicin jam'iyyar na cikin gida ne kuma Leke Abejide ba ya da hurumin shigar da ƙara saboda ya kasa nuna yadda ake take masa haƙokƙinsa sakamakon shugabancin jam'iyyar ta ADC na yanzu.

Babban Hafsan Sojojin Pakistan, Field Marshal Asim Munir, ya isa birnin Tehran domin halartar jana'izar Ayatollah Ali Khamenei, tsohon jagoran Addinin Iran.
Asim Munir ya je Tehran ne tare da wata babbar tawagar manyan jami'an gwamnatin Pakistan.
Mista muni ya samu tarba daga ministan tsaro da ministan harkokin cikin gida na Iran da kuma wasu manyan jami'an gwamnati da na soji.
Pakistan - wadda ta taka muhimmiyar rawa wajen shiga tsakani tsakanin Iran da Amurka domin cimma Yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙin ƙasashen biyu - na daga cikin ƙasashen da suka aike da manyan tawagogi domin halartar jana'izar.
Firaministan Pakistan, Shahbaz Sharif, da mataimakinsa da kuma ministan harkokin wajen ƙasar, Muhammad Ishaq Dar, na cikin tawagar.

Asalin hoton, Presidency NG
Ƴan Najeriya sama da 260 sun isa birnin Legas a safiyar Juma'a yayin da gwamnatin ƙasar ke ci gaba da kwashe mutanenta da ke zaune a Afirka ta Kudu sanadiyyar zanga-zangar ƙyamar baƙi da ta ɓarke a baya-bayan nan.
Yanzu yawan ƴan Najeriya da gwamnatin ƙasar ta kwashe daga ƙasar ta Afirka ta Kudu ya kai 700.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin waje ta Najeriya Kimiebi Imomotimi Ebienfa ya shaida wa BBC cewa mutane 266 ɗin da suka isa Najeriya a yau sun sauka birnin Legas ne da ƙarfe 10:40 na safe.
Najeriya ta fara kwashe mutanenta daga Afirka ta Kudu ne bayan jerin zanga-zangar da wasu ƙungiyoyi suka riƙa yi, inda suke far wa baƙi, lamarin da ya sa ƴan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu suka riƙa kira ga gwamnatinsu da ta kwashe su zuwa gida.
Wannan ne jirgi na huɗu na ƴan Najeriya da ya isa gida a ƙarƙashin shirin.
Hukumomin Najeriya sun kuma ce akwai wasu jiragen ɗauke da ƴan Najeriya da ake sa ran za su sauka a ƙasar a ranakun 6 da kuma 9 ga watan Yuli.
Haka nan gwamnatin Najeriyar ta shawarci ƴan ƙasar nata da ake mayarwa gida su tantance dukiyoyinsu da suka bari a baya, inda hukumomin ke sa ran neman gwamnatin Afirka ta Kudu ta biya diyya.

Asalin hoton, ISNA
An fara gudanar da tarurrukan jana'izar shugaban Iran a birnin Tehran, tare da halartar baƙi da manyan jami'ai daga ƙasashen waje.
Tun da farko an wallafa hotunan He Wei, mataimakin shugaban babban majalisar Jama'ar China wanda ya isa Tehran domin halartar taron da za a gudanar a yau.
A farkon ziyararsa, ya kuma gana da Mohammad Bagher Qalibaf, kakakin majalisar dokokin Iran.
Ya zuwa yanzu, shugaban ƙasar Turkmenistan da kakakin majalisar dokokin Iraƙi, da shugaban kasar Iraƙi, da shugaban yankin Kurdistan na Iraki, da firaministan Armenia na daga cikin waɗanda za su halarci taron jana'zar.
Za a ci gaba da gudanar da tarurrukan jana'izar, wanda ƴan ƙasa da masu jimami za su halarta, a ranar Litinin a Tehran, da ranar Talata a Qom da ranar Laraba a Iraƙi, da kuma ranar Alhamis a Mashhad.

Asalin hoton, IRIB
Shugaban ƙasar Tajikistan, Emomali Rahmon, ya isa birnin Tehran da safiyar ranar Juma'a domin halartar jana'izar Ali Khamenei.

Asalin hoton, Getty Images
Najeriya ta tabbatar da janyewar akasarin sojojin Amurka da aka tura ƙasar a farkon wannan shekarar don taimakawa wajen yaƙi da ƙaruwar ayyukan ta'addanci daga ƙungiyoyin masu iƙirarin jihadi.
Kakakin rundunar sojin Najeriya, Michael Onoja, ya shaida wa BBC ranar Juma'a cewa "ba zai shafi yadda muke tafiyar da harkokinmu ba ." Ya kuma ce "Za mu ci gaba da musayar bayanan sirri", yana mai maimaita kalaman da kwamandan rundunar sojin sama ta Amurka a Afirka, Janar Dagvin Anderson, wanda ya yi a lokacin wani taron manema labarai a ranar Alhamis.
Najeriya na fuskantar ƙalubalen tsaro da dama, ciki har da ƙungiyoyi masu dauke da makamai masu iƙirarin jihadi da ƴan fashin daji da kuma tashe-tashen hankulan da suka bazu daga arewa zuwa sassan tsakiya da kudancin Najeriya.
Haɗin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka ya ƙaru bayan da Washington ta zargi hukumomin Najeriya da rashin yin abin da ya dace don kare ƙungiyoyi masu rauni, kuma ta yi zargin cewa ana yi wa "kiristoci kisan ƙare dangi" a ƙasar - ikirarin da Najeriya ta miusanta, tana mai cewa tashin hankalin yana da sarkakiya kuma yana shafar mutane a dukkan al'ummomi.
Tun daga watan Disamba na shekarar da ta gabata, ƙasashen biyu sun ce dakarunsu sun gudanar da ayyukan haɗin gwiwa don kai hari kan maɓoyar ƴan bindiga a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa tsaro a Najeriya.

Asalin hoton, Ap
An ceto wani mutum da ransa bayan ya maƙale na tsawon kwanaki takwas a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin da ya ruguje bayan girgizar ƙasa ta biyu da aka yi a ƙasar Venezuela.
Ma'aikatan aikin gaggawa sun sami nasarar zaƙulo Hernán Gil sama da sa'o'i 100 bayan da suka gano shi a ƙarƙashin tan 140 na tarkace.
Shugabar riƙo ta ƙasar Venezuela Delcy Rodríguez ta ziyarci Gil a asibiti a ranar Alhamis.
Ya zuwa yammacin Alhamis, an tabbatar da mutuwar mutum 2,595 a girgizar ƙasar da ta afku a Venezuela a ranar 24 ga Yuni, kuma har yanzu akwai dubban mutane da ba a gano inda su ke ba.
Da ta ke magana a wani taron manema labarai a ranar Alhamis, Rodríguez ta bayyana girgizar ƙasar a matsayin "wani bala'i mai munin da bamu taba tsammani ba".
Ta yi watsi da sukar da da ake yi cewa gwamnatinta ba ta gaggauta ɗaukar matakai bayan girgizar ƙasar ba, tana mai cewa an tura dubban jami'ai bayan aukuwar bala'in.

Asalin hoton, Getty Images
Sojojin Rasha sun kai wani mummunan harin makami mai linzami kan Kyiv cikin daren Alhamis, inda suka kashe aƙalla mutum 30, abin da magajin garin ya bayyana a matsayin "hari mafi muni" da aka kai babban birnin Ukraine.
Mutum 91 sun ji rauni, in ji shugaban gwamnatin sojin Kyiv, Timur Tkachenko.
Magajin gari Vitaly Klitschko ya ce wata tashar motocin asibiti na daga cikin wuraren da abin ya shafa.
Duk da cewa hare-haren da aka kai a baya sun yi sanadiyar mutuwar mutane da dama, wannan harin shi ne wanda ke da mafi yawan bama-bamai da aka zazzaga a babban birnin ƙasar.
An kwashe mutane daga unguwanni da dama yayin da aka kai hare-hare a birnin sa'o'i bayan shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya gargaɗin cewa Rasha na shirin kai hari.
Moscow ta ce dakarunta sun kai hari kan abin da ta kira masana'antar soji a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da ake kai wa farar hula a Rasha.
Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya shaidawa manema labarai jiya Alhamis cewa, Rasha za ta ci gaba da ƙara matsawa gwamnatin Kyiv lamba har sai ta cimma muradunta.

Asalin hoton, Reuters
Iran ta fara gudanar da zaman makoki na gama-gari yayin da ake shirin fara jana'izar tsohon Jagoran addinin kasar, Ayatollah Ali Khamenei, bayan fiye da watanni huɗu da aka kashe shi a hare-haren da Amurka da Isra'ila suka kai.
Za a ajiye gawar tsohon Ayatollah din a babban ɗakin taro na 'Grand Mosalla' da ke birnin Tehran tun daga ranar Juma'a, kafin a kai shi garinsu na Mashhad domin binne shi a ranar Alhamis mai zuwa.
Jami'ai sun ce jana'izar na iya samun halarcin masu makoki miliyan 20 daga sassan Iran, a cewar AFP.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Iran da Amurka ke tsagaita wuta a tsakaninsu bayan sanya hannu kan yarjejeniyar farko ta dakatar da faɗan da suke yi a watan Yuni.
Za a ajiye gawar Khamenei a Grand Mosalla na tsawon kwanaki uku, tare da gawarwakin sauran yan daginsa da aka kashe a harin da Amurka da Isra'ila suka kai a watan Fabrairu.
Za a yi wani taron jana'iza a hukumance a birnin Tehran ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa hukumomi sun umarci ofisoshin gwamnati da na masu zaman kansu da ke Tehran da su rufe daga Asabar zuwa Litinin, yayin da aka kafa dokar takaita zirga-zirga a sassan tsakiyar birnin.

Asalin hoton, Reuters
Kafafen yaɗa labaran gwamnatin Syria sun ce wani bam ya tashi a wani gidan shan shayi mai cike da jama'a a tsakiyar birnin Damascus, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum shida tare da jikkata wasu 22.
Ma'aikatar harkokin cikin gida ta ce an dasa wani abu mai fashewa a cikin gidan shayin, wanda ke da nisan mita 100 kacal (ƙafa 330) daga ginin ma'aikatar Shari'a, wani babban ginin gwamnati a gundumar Hejaz da ke babban birnin ƙasar.
Babu wata ƙungiya da ta yi ɗauki alhakin kai harin nan take. Wannan shi ne harin bam mafi muni da aka kai a birnin Damascus tun bayan harin ƙunar baƙin wake da aka kai a wani coci a watan Yunin 2025 wanda ya kashe mutane 25.
Wata kungiyar masu iƙirarin jihadi mai suna Saraya Ansar al-Sunnah, ta ce ita ce ta kai harin, amma hukumomi sun dora alhakin harin kan ƙungiyar IS.
Mohammed al-Dahabi, mamallakin wani shagon sayar da gilashi da ke kusa da gidan shayin, ya ce harin bam ɗin na ranar Alhamis ya yi kama da wanɗnada aka riƙa gani a Damascus a lokacin yaƙin basasar Syria.
A yayin ziyarar da ya kai wurin da lamarin ya faru, Gwamnan Damascus, Maher Marwan Idlibi, ya ce za a hukunta waɗanda ke da hannu a kitsa harin.