Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Jihohin Najeriya da suka fi samun ƙaruwar masu cutar HIV a 2025
Wani rahoto da ma'aikatar lafiya da walwalar jama'a ta Najeriya ta wallafa ranar Talata ya nuna cewa an samu ƙarin cuta mai karya garkuwar jiki 102,25 a faɗin ƙasar a shekarar da ta gabata.
Rahoton mai taken rahoton yanayin lafiyar ƴan ƙasar na 2025 wato "The State of the Health Nation Report", ya bayar da bayani dalla-dalla kan irin ƙarin da kowacce jiha daga cikin jihohin ƙasar 36 da Abuja suka samu a 2025.
Rahoton ya kuma nuna damuwa kan yadda alƙaluman cutar suka ƙaru duk da irin ƙoƙarin da hukumomi ke yi wajen ganin an rage yaɗuwar cutar da mace-mace mai alaƙa da ita.
Alƙaluma daga hukumar da ke daƙile yaɗuwar cutar mai karya garkuwar jiki ta Najeriya, NACA sun nuna cewa a yanzu haka akwai masu ɗauke da cutar HIV/AIDS miliyan 1.9.
Jihohin da suka fi yawan masu HIV
- Lagos - 10,430
- Rivers - 6,287
- Kano - 6,106
- Akwa Ibom - 5,413
- Taraba - 4,854
- Benue - 4,804
- Anambra - 4,468
- Kaduna - 3,659
- Adamawa - 2,989
- FCT - 2,764
Jihohi masu karancin masu HIV
- Ekiti - 462
- Bayelsa - 982
- Gombe - 1,083
- Osun - 1,093
- Kwara - 1,371
- Enugu - 1,429
- Yobe - 1,483
- Katsina - 1,541
- Kebbi - 1,572
Alamomin cutar HIV
Mafi yawan mutanen da su ka kamu da cutar HIv kan ji alamomin mura musamman makonni biyu zuwa shidda bayan daukar cutar. Bayan wannan, bincike ya nuna ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba har sai bayan shekaru masu yawa.
Alamomin da aka fi gani a masu fama da cutar sun hada da:
- Zazzabi
- Ciwon wuya
- Kuraje a jiki
- Kasala
- Ciwon gaɓoɓi
- Kaluluwa a wasu sassan jiki
Bayan waɗannan alamomin na farko-farko sun ɓace, ba lallai a sake ganin wasu alamomi ba.
A wannan lokaci, ƙwayar cutar tana ci gaba da lalata garkuwar jiki.
Da zarar garkuwar jiki ta durƙushe, alamomin da za a iya ji su ne:
- Rama
- Gudawa ba ƙaƙƙautawa
- Zufa cikin dare
- Yawan ƙuraje a jiki
- Manyan cututtuka masu haɗari
Gano cutar HIv a kan kari na rage yiwuwar lalacewar garkuwar jiki.
Sannan a shekarun baya, kwararru sun samar da magungunan da ke hana kwayoyin cutar HIV bunkasa a jikin mai dauke da ita.