Me ake ciki kan yiwuwar cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Amurka?

Asalin hoton, Getty Images
Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Marco Rubio ya ce za a iya yin sanarwa a ƴan kwanaki masu zuwa da za ta kawo ƙarshen yaƙi a Gabas ta Tsakiya.
Donald Trump ya ce tattaunawar da ake da Iran ta shiga mataki na ƙarshe.
Rubio ya faɗa a wani taron manema labarai da aka yi a Indiya cewa yarjejeniyar da za a iya cimma za ta iya warware damuwar Amurka kan Mashigar Hormuz tare da kare Iran daga mallakar makamin nukiliya sai dai jami'in bai bayar da cikakken bayani ba.
Jami'an Iran zuwa yanzu ba su yi magana kan abin da yarjejeiyar da za a iya cimma ta ƙunsa ba amma Shugaban Iran Masoud Peshkeskian ya ce: "Ba za a ɗauki matsayar da ta saɓa da tsarin babban kwamitin tsaro na Iran ba kuma dole a nemi haɗin kai da izinin Jagoran addini."
A gefe guda kuma, an wallafa rahotannin da ba a tabbatar da su ba da suka yi bayani dalla dalla kan yarjejeniyar da za a iya cimma tsakanin Tehran da Washington.
Kafar yaɗa labarai ta Axios ta ruwaito cewa wani jami'in Amurka na cewa Tehran da Washington sun kusa ƙulla yarjejeniya da za ta tsaiwata yarjejeniyar tsagaita wuta da kwana 60, a buɗe Mashigar Hormuz sanan a bai wa Iran damar sayar da mai tare kuma da tattaunawa kan taƙaita shirin Nukiliyar Iran da kuma kawo ƙarshen yaƙi a Lebanon.
Kamfanonin dillancin labarai a Tasnim da Fars da ke da kusanci da sojoji da jami'an tsaro, sun ruwaito bayanan yarjejeniyar da za a iya cimma waɗanda suka zo kusan ɗaya da bayanan da Axios ta ruwaito.
Abin da ka iya kasancewa a yarjejeniyar - Axios
Jami'in Amurkar ya shaida wa Axios cewa yarjejeniyar fahimtar da Amurka da Iran suka sanya wa hannu za ta yi aiki ne tsawon kwana 60 kuma za a iya tsawaita ta ta hanyar yarjejeniya tsakanin ƙasashen biyu.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Cikin kwana 60 na yarjejeniyar, za a buɗe Mashigar Hormuz ba tare da an karɓi haraji daga wajen jiragen ruwa ba sannan Iran za ta yi alƙawarin bayar da dama jirage su yi zirga-zirga a mashigar.
A nata ɓangaren kuma Amurka za ta janye matakin da ta ɗauka na toshe tashoshin jiragen ruwa Iran tare da bai wa ƙasar damar sayar da mai tare kuma da tsame ta daga takunkumi.
A cewar Axios, Iran za ta yi alƙawarin "ba za ta taɓe neman ta mallaki makamin nukiliya ba" tare da tattauna batun dakatar da shirin bunƙasa nukiliyarta.
Wasdu majiyoyi biyu da suka fahimci batun sun shaida wa Axios cewa Iran ta hannun masu shiga tsakaninta ta yi bayanin abubuwan da za ta iya amincewa da su game da dakatar da shirinta a nukiliya da kuma miƙa sinadaran uranium da ake haɗa nukiliya.
A cewar Axios, Amurka ta amince ta tattauna kan janye takunkumai da dawo da kadarorin Iran da aka ƙwace cikin kwanaki 60 na yarjejeniyar duk da cewa za a aiwatar da hakan ne a wani ɓangare na yarjejeniyar ƙarshe da za a iya cimma wadda kuma za a iya tantancewa lokacin aiwatarwa.
A cewar jami'in na Amurka da ya yi magana da Axios, Iran na neman a janye dukkanin takunkuman da aka ƙaƙaba mata da kuma gaggauta dawo da kadarorinta da aka ƙwace sai dai Amurka ta ce hakan zai faru ne idan Iran ta amince ta yi sadaukarwa mai ma'ana.
A cewar rahoton, dakarun Amurka da aka tura zuwa yankin a watannin baya-baya za su ci gaba da kasancewa na tsawon kwana 60 sannan su janye da zarar yarjejeniyar ta tabbata.
A cewar Axios, daftarin yarjejeniyar fahimtar ya kuma nuna cewa yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah a Lebanon zai zo ƙarshe.
Zuwa yanzu Isra'ila ba ta mayar da martani ba kan rahotannin sai dai Axios ta ce Firaiminista Benjamin Netanyahu ya bayyana damuwa a wata waya da ya yi da Shugaba Donald Trump kan faɗaɗa yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin US da Iran ta taɓo yaƙin Lebanon.
Jami'in Amurka ya shaida wa Axios cewa Mista Netanyahu ya bayyana damuwa game da wasu ɓangarorin yarjejeniyar sai dai ya yi tsokacin cikin mutuntawa.

Asalin hoton, AFP via Getty Images
Tun da farko, Shugaba Donald Trump na Amurka ya ce ya yi magana da Benjamin Netanyahu game da Iran kuma an yi tattaunawar fahimta.
"Bibi Netanyahu0 yana da nashi buƙatun sai dai ya kamata Trump ya yi tunani kan buƙatun Amurka da kuma tattalin arzikin duniya," in ji wani jami'in Amurka da ya yi magana da Axios.
Jami'in Amurkar ya jaddada cewa yarjejeniyar tsagita wuta a Lebanon ba za ta kasance ta ɓangare guda ba inda ya ce za a bai wa Isra'ila damar yin martani idan Hezbolla ta ɗauki matakan kai hari.
Me kafafen yaɗa labaran Iran suka ce?

Asalin hoton, Getty Images
Kasancewar jami'an Iran ba su yi magana a hukumance ba kan bayanan yarjejeniyar da za a iya cimma, kamfanonin dillancin labarai kamar Tasnim da Fars da ke da kusanci da ɓangarorin tsaro sun wallafa wasu bayanai.
Waɗannan kamfanonin dillancin labaran sun wallafa bayanan da suka zo daidai da na Axios sai dai bayanan nasu cike suke da mummunan fata ga Amurka.
Fars ta wallafa cewa: "Yayin da akeƙoƙarin cimma yarjejeniya, majiyoyi sun ruwaito yiwuwar Amurka ta koma tsarinta na baya na saɓa wani ɓangare na yarjejeniyar. Wannan ne karo na biyu da Amurka ta saɓa ƙa'idojin yarjejeniyar.
Kamfanin dillancin labaran ya ruwaito wasu daga cikin mambobin tawagar Iran masu shiga tsakani suna cewa "ba mu yarda da Amurka ba kuma rashin yardar shi ne maf munin al'amari."
Kamfanin dillancin labarai na Tasnam ya yi rubutu kan damuwar da Iran ta nuna game da yadda Amurka ta gaza cika alƙawari kan kadarorinta da aka ƙwace.
"Bayanai sun nuna cewa a makonnin baya-bayan nan Amurka na ta ƙoƙarin jingina batun sakin kadarorin ga yarjejeniyar da za a iya cimma kan batun nukiliya sai dai Iran ta jaddada cewa ya kamata a saki wasu daga ciki a farkon sanarwar yarjejeniyar fahimta. Sannan ya kamata a yi bayani dalla dalla kan tsarin sakin kadarorin yayin tattaunawar sannan idan Amurka ta ƙi yadda da haka, Iran za ta yi nazari a kai a tattaunawar da za a yi a gaba."
Kamfanin dillancin labaran ya kuma wallafa cewa: "Har yanzu akwai rashin fahimta tsakanin Iran da Amurka kan wasu ɓangarorin yarjejeniyar fahimtar kuma har yanzu ba a cimma matsaya ba saboda matsala daga Amurka."
A cewar Tasnim, an sanar da mai shiga tsaki na Pakistan cewa ba za a cimma yarjejeniya ba idan ba a warware waɗannan batutuwan ba, har da sakin kadarorin.

Asalin hoton, NurPhoto via Getty Images
Wani batu da aka jaddada a kafofin yaɗa labaran Iran shi ne ɗage tattaunawar nukiliya har sai bayan yarjejeniyar farko.
Fars ya rubuta cewa "majiyoyi da suka fahimci tattaunawar sun jaddada cewa daftarin yarjejeniyar da za a iya cimma tsakanin Iran da Amurka ba ta shafi alƙawuran Iran kan nukiliya ba sannan an ɗage duk batutuwan da suka shafi shirin nukiliyar zuwa kwanaki 60 bayan an sa hannu kan yarjejeniyar."
Fars ta ce "Ba a yi alƙawarin miƙa sinadaran haɗa nukiliya ba."
Tasnim ta ce yarjejeniyar ƙara shige da ficen jiragen ruwa ta Mashigar Hormuz kamar yadda aka gani kafin lokacin yaƙi ba yana nufin cewa mashigar za ta koma matsayinta na baya.
Kamfanin dillancin labaran ya kuma rubuta cewa duk da akwai yiwuwar a sa hannu kan yarjejeniyar fahimta, Iran a shirye take tattaunawar ta rushe inda ya ruwaito wata majiyar tsaro yana cewa "idan Amurka ta sake yin kuskure ta kuma ci gaba da kai hari kan Iran, za ta fuskanci fushin Iran."
Muhimman lokuta a tattaunawar Iran da Amurka
Ga wai ƙarin bayani kan ci gaban da aka samu kan tattaunawar Iran da Amurka bisa shiga tsakanin Pakistan a makonnin baya-bayan nan:
8 ga Aprilu: Pakistan ta sanar da tsagaita wuta na tsawon mako biyu tsakanin Iran da Amurka wadda ta ƙare ranar 22 ga Aprilu. Donald Trump ya ce yarjejeniyar ta jingina ne kan ƙa'idar buɗe Mashigar Hormuz. Pakistan ta ce Lebanon ma tana cikin yarjejeniyar amma Amurka da Isra'ila sun musanta hakan.
11 ga Aprilu: Manyan jami'an Amurka da Iran har da Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance da shugaban majalisar dokoki Mohammed Baqer Qalibaf da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Aragchi sun gana a Pakistan. Bayan shafe sa'a 21 suna tattaunawa, an gaza warware muhiman batutuwan da ake taƙaddama a kai tsakanin Amurka da Iran.
12 ga Aprilu: Bayan tashi baram-baram a tattaunawar Islamabad, Mista Trump ya sanar cewa zai toshe hanyoyin teku a Iran.
13 ga Aprilu: Cibiyar ayyukan soji ta Amurka CENTCOM ta sanar cewa matakin toshe hanyoyin tekun Iran ya soma aiki yayin da Iran ta ci gaba da rufe Mashigar Hormuz.
21ga Aprilu: Mista Trump ya tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta domin a ci gaba da tattaunawa.
5 ga Mayu: Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya sanar da kawo ƙarshen samamen Operation Epic Fury don ruguza cibiyoyin Iran.
8 ga Mayu: Donald Trump ya ceyarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Amurka da Iran na nan daram duk da cewa an gwabza faɗa tsakanin Iran da Amurka a Mashigar Hormuz.
10 5 ga Mayu: Iran ta gabatar wa Amurka wani tsari da ya ƙunshi yadda za a gaggauta kawo ƙarshen yaƙi da kuma dakatar da toshe hanyoyin sufurin Iran. Donald Trump ya bayyana hakan a matsayin abin da ba za a lamunta ba.
15 ga Mayu: Shugaban Amurka ya ce zai amince idan Iran ta dakatar da shirin nukiliyarta na shekara 20.
18 ga Mayu: Donald Trump ya sanar a shafinsa na Truth Social cewa ya ce Amurka ta fasa kai wa Iran hari bisa buƙatar ƙasashen Gulf sai dai idan har ba a cimma yarjejeniya ba, Amurka a shirye take ta kai gagarumin farmaki kan Iran "ko wane lokaci."
23 ga Mayu: Mr. Trump ya ce an ƙarƙare yarjejeniya da Iran kuma za ta ƙunshi buɗe Mashigar Hormuz . Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran ya ce an ɗan warware wasu matsaloli da ake taƙaddama a kai sai dai ya jaddada cewa har yanzu ana taƙaddama a kan wasu.
24 ga Mayu: Marco Rubio,a wani taron manema labarai a New Delhi ya ce an samu ci gaba sosai sannan akwai yiwuwar a ji ƙarin labarai.










