Paul Pogba: Man Utd ta nemi sabunta kwangilar ɗan wasan Faransa

Manchester United ta nemi tsawaita kwangilar Paul Pogba da shekara daya, inda dan wasan na tsakiya zai ci gaba da murza leda a Old Trafford har shekarar 2022.

Tsohuwar kwangilar dan wasan mai shekara 27, wanda ya taimaka wa Faransa ta dauki Kofin Duniya, za ta kare a karshen kakar wasan da muke ciki.

Pogba ya murza leda a dukkan wasanni uku na Gasar Firimiya da United ta buga a wannan kakar da muke ciki, ciki har da kashin da suka sha a hannun Tottenham da ci 6-1.

Lokacin da ake hutun tafiya gida, Pogba ya ce babban burinsa shi ne ya murza leda a Real Madrid .

An fahimci cewa an dauki matakin tsawaita kwangilarsa ne a makonnin da suka wuce tun kafin ya yi tsokacin cewa yana son tafiya Madrid.

Pogba ya koma United daga Juventus a kan £89m a shekarar 2016.

Raunin da ya ji a idon sawunsa ya hana shi buga wasanni 22 a kakar wasan da ta wuce.