Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda aka kama ni bayan sayen layin waya da ƴan bindiga suka taɓa amfani da shi'
A baya-bayan nan ne ƴansanda suka tsare wata matashiya mai suna Tititlayo Ibrahim, ƴar jihar Ondo kan laifin da ba ta san komai a kai ba bayan sayan layin waya da aka taɓa amfani da shi.
Duk da cewa ba ta aikata laifi ba, ƴansanda sun bibiyi layin waya da masu garkuwa suka taɓa amfani da shi da ke hannunta wajen tsare ta. Masana shari'a sun kwatanta wannan lamari da rashin adalci, inda suka buƙaci matashiyar ta dangana da kotu don neman hakkinta.
Yayin da take tattaunawa da BBC, Titilayo ta bayyana abin da ta fuskanta a hannun ƴansanda kan abin da ta san komai a kai ba.
Lamarin ya faru ne a Akure, babban birnin jihar Ondo.
Titilayo ta tuna yadda wata mata ta kira ta a waya inda take cewa tana son sayan wani abu a wurinta. A ce ba ta sani ba ƴansanda ne ke son kama ta ba.
"Lamarin ya afku ranar 16 ga watan Oktoban, 2025, lokacin da wata bakuwar lamba ta aika sako ga layin da nake amfani da shi wajen yin kasuwanci.
"Ta buaci na aika hotunan abin da nake sayarwa, sai na aika, inda ta zaɓi biyu daga cikin kayayyakin.
"Ta ce wayarta ta samu matsala tana amfani ne da wayar mijinta. Don haka ta kai musu kayan wajen da suke jira don karɓar kuɗinta.
"Na ce ba na kai kayayyaki ga kwastomomi, amma ina da manaja wanda zai iya kai musu.
"Idan kuma za su zo su karɓi kayan da kansu, zan tura musu adireshin gidana sai su karɓa.
"Na tsaya a kofar shiga rukunin gidajenmu, sannan na ga wata mara, matar ta haɗa zufa sosai, na kuma gano cewa ba za ta iya sayan farin kaya da tayi niyya ba duka.
"Na je na same ta sannan na fara nuna mata abin da take son saya, yayin da muke magana, sai wani mutum ya isa."
"Ya nuna min katin shaida da ke nuna cewa shi ɗansanda ne, na ɗauka mijin matar ce, sai dai ina ta kan nunawa matar irin kayayyaki da nake da su a waya ta.
"Kwatsam, suka karɓi wayata, sannan ita ma matar ta nuna min shaidarta ta ƴarsanda, sai suka ce za su tsare ni."
Yayin da Titilayo ta ki amincewa a tsare ta wajen ƴansanda inda ta buƙaci a tafi kotu, matar ba ta nuna fara'a ba.
Yayin da suke bayyana abin da ya faru a baya, ƴansandan sun faɗa mata cewa masu garkuwa sun taɓa amfani da layin waya da ke hannunta wajen aikata ɓarna.
Tsohon wanda yake amfani da layin ya yi garkuwa da wani sannan ya kashe shi bayan karɓar kuɗin fansa naira miliyan 50 ranar 1 ga Janairun, 2024, ƴansanda suka faɗa mata.
Bayanan Airtel sun nuna cewa Titilayo ta sayi layin wayar watanni 15 bayan aikata garkuwa da kuma kisan.
"Na faɗa musu cewa ina amfani da layin don shiga intanet, ba ya kan wayata kawai amfani da shi na yi wajen haɗa shi da wayata, sannan na saye shi layin da ke kira 2025."
"Sai dai ba su amince da duka abubuwan da na faɗa ba, na tsorata kawai na fashe da kuka, ina addu'ar Allah ya fitar da ni.
"Lauya na ya faɗa wa ƴansanda su je su binciki bayanan kamfanin sadarwa na Airtel mallakin layin wayar don ganin ko a wurinsu na sayi layin.
"Mun je wurin, kuma bayanai sun tabbatar da cewa a wurin na sayi layin ranar 15 ga Afrilun, 2025, shekara ɗaya da wata uku bayan aikata garkuwa da kuma kisan.
"Sai dai duka wannan bai sa ƴansandan sun yarda da ni ba, sun wulakanta ni. Na tsorata sosai saboda na san ƴan Najeriya da dama na tsare a hannunsu babu mai ƙwata musu ƴanci."
BBC ta tuntuɓi ƴansandan birnin Akure da kuma kamfanin layin waya na Airte Nigeria, sai dai ba su ce uffan ba ga buƙatar martaninsu.
Me dokar Najeriya ta ce ga bayar da layin waya daga kamfanonin sadarwa?
Wata masaniya shari'a da ta ƙware kan ɓangaren sadarwa, Abimbola Orogade, ta bayyana abin dokokin Najeriya suka faɗa kan bayar da layi da kuma sake bayar da shi daga wajen kamfanonin sadarwa a Najeriya.
Orogade ta faɗa wa BBC a tattaunawa ta wayar tarho cewa "idan mutum na buƙatar layin waya, dole ne sai ya je wurin kamfanonin sadarwa, muna da kamfanoni huɗu zuwa biyar.
"Mutumin da ke son rajistar layin waya zai garzaya ofishinsu, za su ɗauki hoton yatsun hannu, su kuma yi duba kan mutum.
"Za su ɗauki hoton mutum, sannan za su saka bayanan shi.
Daga nan za a bai wa mutum layin waya, sai kuma a haɗa shi da shaidar zama ɗan ƙasa wato NIN."
Orogade ta ce hakkin hukumar da ke kula da kamfanonin sadarwa ta Najeriya, NCC ne wajen sa ido a aikin.
A kan abin da ake buƙata wajen mutumin da ke son sayan layin waya, Abimbola ta ce dole ne mutum ya gabatar da kansa domin bayar da bayanai da kamfanin sadarwa ke buƙata.
"Dole ne ka gabatar da kanka idan kana son sayan layin waya. Saboda za a ɗauki yatsun hannunka da kuma hotonka don haɗa bayananka.
"Ana yin haka ne saboda idan masu garkuwa da mutane ko ƴan fashi suka yi amfani da layin wajen aikata ta'asa, to kai za a kama," in ji Orogade.
Ta ƙara da cewa yana da muhimmanci ga mutumin da ke amfani da layin waya ya kai rahoto wajen ƴansanda idan wani abu da ya faru da layin.
Ta ce yana da kyau mutum ya sanarwa kamfanin sadarwa idan layinsa ya ɓata.
Masaniyar shari'ar ta ce idan aka samu yanayin da kamfanin ya sadarwa ya sayarwa mutum layin da aka taɓa amfani da shi wajen aikata ta'asa, to mutum ya faɗa wa lauya wanda zai tinkari ƴansanda da batun.
Ta kuma ce wanna ita ce dabara mai kyau da Titilayo ta yi amfani da shi da ya kai ga fitar da ita.
"Kamfanin sadarwa ya jefa matashiyar cikin tsaka mai wuya ta hanyar kasa yin abin da ya dace."
Orogade ta ce ƴar bautar ƙasa da lamarin ya shafa na da damar shigar da ƙarar kamfanin sadarwa da kuma ƴansanda bisa wani tsarin ƴanci na 2009, don a biya ta diyya na kokarin tauye mata hakki.