Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Me dokar Najeriya ta ce kan masu son tsayawa takara idan ba su ajiye muƙaminsu ba?
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- Lokacin karatu: Minti 4
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.
A wata takardar umarni, wacce sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa dole dukkan waɗanda ke da ƙudurin su ajiye aiki.
Tinubu ya jaddada cewa matakin ya zama dole domin tabbatar da bin dokokin zaɓe sau da ƙafa, da wanzar da gaskiya da adalci a cikin tsarin siyasa, da kuma tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe.
Ya buƙaci jami'an da abin ya shafa su tabbatar sun mika wasiƙun murabus ɗinsu ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kafin cikar wa'adin da aka bayar.
Umurnin ya shafi ministoci, masu ba da shawara, daraktoci da shugabannin hukumomi.
Me dokar zaɓe ta ce?
Takardar umarnin da shugaban Najeriyar, ta ce matakin ya yi daidai da tanadin Sashe na 88(1) na Dokar Zaɓe ta shekarar 2026, da kuma jadawalin gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyu da hukumar INEC ta fitar.
Sashe na 88(1) ya ce "dukkan wani mai riƙe da muƙamin siyasa a kowane mataki, ba zai zama daliget a zaɓe ba, ko kuma a zaɓe ba, ko wakili a taron jam'iya ko ya tsaya takara a matakin jam'iya ko neman wata kujerar siyasa da ake zaɓe".
Hakan na nufin babu wanda zai yi takara a lokacin da ya ke riƙe da ofishin gwamnati.
Sai dai ba ta bayyana wa'adin yin murabus ɗin ba, kamar yadda Tinubu ya bayar na wa'adin yin murabus.
A sabon jadawalin da hukumar zaɓen Najeriya Inec ta fitar na gudanar da zaɓukan 2027, ya buƙaci dukkanin jam'iyyu su gudanar da zaɓukan fidda gwani tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayun 2026.
Hukumar ta ce jadawalin ya yi daidai da sashe na 84 na sabuwar dokar zaɓe ta 2026, wanda ya buƙaci "dukkanin jam'iyyun siyasa su gudanar da zabuƙan cikin gida kuma su gabatar da ƴantakarar su, zaɓen wanda zai gudana bisa sanya idon Inec."
Wannan ke nuna cewa sashe na 84 da 88 da dokar, ya wajabta wa dukkanin jam'iyuu gudanar da waɗannan zaɓuka a lokacin da Inec ta tsara, kuma ba a yarda wani mutum ya yi takara a lokacin da yake riƙe da ofishin gwamnati ba.
Yadda jadawalin hukumar zaɓen Najeriya yake
A jadawalin da hukumar Inec ta fitar, ta sanya tsakanin 23 ga watan Afrilu zuwa 30 ga watan Mayun 2026, jam'iyyu su gudanar da zabuƙan cikin gida kuma a gabatar mata da sunayen ƴantakarar shugaban ƙasa da ƴanmajalisar tarayya a ranar 11 ga watan Yuli, sai kuma na gwamnoni da ƴanmajalisar jiha kada ya wuce 8 ga watan Agusta.
Saboda haka dole ne duk wanda ke da sha'awar takara ya ajiye muƙaminsa, duk da yake dokar ba ta ƙayyade adadin kwanaki ba, amma sai don ya zama wajibi ga masu son tsayawa takarar su shiga zaɓen fitar da gwani.
A lokacin zaɓen Najeriya 2023, ƙarƙashin tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, masu riƙe da muƙaman gwamnati da dama sun ƙi yin murabus, lamarin da ya hafar da cece-ku-ce kan yadda ma'aikata suke watsi da aikinsu zuwa yaƙin neman zaɓe.
Abin da zai faru idan mutum ya shiga takara ba tare da yin murabus ba
Barista Aminu Abdulrashid, lauya ne mai zaman kansa a Najeriya, ya ce dokar ta fayyyace komai kuma dole duk mai riƙe da muƙamin gwamnati da yake son yin takara, kafin cikar wa'adin jadawalin zaɓe na kwanaki 30 da yin zaɓen fitar gwanin jam'iya, da gabatar da sunayen ga hukumar Inec.
Sai dai ya ce dokar ba ta haramta wa ma'aikacin gwamnati shiga siyasa ba, kamar yada yake a kundin tsarin mulkin Najeriya, amma idan mutum zai yi takara ne ake son ya ajiye aikin.
"Wanda bai yi haka ɗin ba, ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasa," in ji shi.
Ya ce an yi dokar ne saboda kada masu riƙe da muƙaman siyasa su yi amfani da ofishinsu wajen samun fifiko ko nasa a kan abokan takararsu.
Shin za a hukunta wanda ya taka dokar?
Barista Abdulrashid ya ce duk wanda ya yi takara ba tare da ya bi wannan matakin ba, hukumar zaɓen ƙasar za ta iya soke nasararsa ko da bayan ya ci zaɓe.
"Za a iya haramta ma zaben fidda gwanin, a ce ya haramta. Idan ma ya tsallake hukumar zaɓe, za a iya ƙalubalantar shi a kotu, kuma za a iya soke wannan zaɓen."
Amma Baristan bai bayyana wani hukunci na ladabtarwa da za a dauka kan wanda ya aikata hakan ba.
Sai dai ya ce za a iya tuhumar mutum a gaban shari'a da saɓa dokokin aikin shi da ƙin bin dokokin ƙasa.