'Ƴanbindiga sun sace fiye da mutum 150 a Zamfara'
Al'ummar yankin Bukkuyum a jihar Zamfara sun ce ƴanbindiga sun yi sace fiye da mutum kusan 150 a wani hari da suka kai cikin dare.
Mazauna yankunan sun ce ƙauyuka da dama ne ƴanbindigar suka tarwatsa, inda ɗaruruwan mutane suka yi gudun hijira.
Hon Sulaiman Abubakar Gumi, ɗanmajalisar wakilai na tarayya mai wakilar Gumi da Bukkuyum ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce mazauna ƙauyukan Kurfa Ɗanya da Kurfan Magaji sun kwana cikin tashin hankali.
Ya ƙara da cewa kawo yanzu duka mutanen waɗannan garuruwa sun guda sun bar gidajensu, yayin da suke gudun jira a cikin garin Bukuyyum.
Ya ci gaba da cewa dama yankin Bukuyyum da Gumi da Anka ya jima yana da fama da matsalar hare-haren ƴanbindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
Hon Abubakar ya yi kira ga gwamnatin ƙasar ta mayar da hankali domin magance matsalolin tsaron jihar Zamfara.
''Mun ga alamun gwamnati yanzu ta mayar da hankalinta a Borno, saboda barazanar dawowar Boko Haram, amma muna kira a gare ta cewa Zamfara na fama da matsalar tsaro'', in ji shi.