Ghana Black Stars na farautar sabon koci

Ghana Team
Bayanan hoto, Ghana za ta kara da Guinea tar da kocin rikon kwarya
An wallafa

Kasar Ghana za ta kara da Guinea a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin Nahiyar Afirka ba tare da kocin tawaagar 'yan kwallon kafar kasar ba.

Tsohon koci Kwesi Appiah ya raba gari da Ghana a farkon watan nan, kuma kasar ta rufe takardar zawarcin horas da kasar ranar 19 ga watan Satumba.

Wani mamba a kwamitin amintattun kungiyar kwallon kafar Ghana Fred Pappoe ya ce za su nada kocin rikon kwarya a karawar da za su yi da Guinea din.

Ghana za ta kara da Guinea a Morocco ranar 10 ga watan Satumba, kafin ta karbi bakuncin Guinea kwanki biyar tsakani.

Ana hasashen cewa tsohon kocin Ghana Milovan Rajevac ne zai maye gurbin Appiar a matsayin sabon kocin Black Stars.