KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/08/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 12 ga watan Agustan 2026.

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Khalifa Dokaji
  • Sheikh Jingir
  • Kano
  • Seriki Abbas
  • xxx
  • xxx
  • Bola Tinubu
  • Senator Gaya
  • xxx
  • xxx
  • Zahra Buhari
  • xxx
  • Nigeria
  • xxx
  • Davido

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Usman MINJIBIR da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Kakakin Donald Trump za ta ajiye aiki

    Karoline Leavitt

    Asalin hoton, Reuters

    Kakakin Fadar White House ta Amurka, Karoline Leavitt, za ta ajiye mukaminta a ƙarshen wannan wata, kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar.

    Trump ya ce Leavitt, wadda yake kira ɗaya daga cikin mataimakansa da ya fi yarda da su, ta yanke shawarar barin aikin domin samun ƙarin lokaci tare da ƴaƴanta da iyalinta.

    Ya ce ya fahimci matakin kuma yana mutunta shawarar da ta yanke.

    Trump ya ƙara da cewa Leavitt za ta ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan masu ba shi shawara a wajen gwamnati, tare da taka rawa wajen jam'iyyar Republican.

    Leavitt mai shekaru 28 ta fara aiki a matsayin kakakin Fadar White House a bara, inda ta zama mafi ƙanƙantar shekaru da ya taɓa riƙe wannan matsayi.

    Har yanzu ba a bayyana wanda zai maye gurbinta ba.

    Leavitt ta haifi ɗiyarta ta biyu a watan Mayu tare da mijinta, Nicholas Riccio. Tana kuma da ɗa mai shekaru biyu.

    Ta dawo bakin aiki a watan da ya gabata bayan kammala hutun haihuwa.

    Bayan sanarwar Trump, Leavitt ta rubuta a shafin X cewa riƙe mukamin kakakin Fadar White House ya kasance “abin girmamawa da kuma kasadar rayuwa mafi girma” a gare ta.

  2. WHO ta yi gargaɗin cutar Ebola na iya zarce annobar da aka gani shekaru goma baya

    WHO

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya, Dr Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya yi gargadin cewa annobar Ebola da ake fama da ita a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo na iya zarce annobar da ta barke a Yammacin Afirka shekaru goma da suka gabata.

    Annobar Ebola a Yammacin Afirka, wadda ta fara a shekarar 2014, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 11,000.

    Tuni Ebola a DRC ta zama annoba ta biyu mafi girma kuma wadda ta fi yaɗuwa cikin sauri a tarihin cutar.

    Dr Tedros ya ce ma'aikatan lafiya na ci gaba da yaƙi da cutar, wadda ta ɓulla a watan Mayu.

    Ya ce kawo yanzu, cutar ta kashe sama da mutum 2,000, yayin da fiye da mutum 4,000 suka kamu da ita.

    Shugaban WHO ya kuma ce an fara matakin farko na gwajin allurar rigakafi guda biyu da ake fatan za su taimaka wajen dakile Ebola nau'in Bundibugyo.

  3. Ƴansanda sun gano gawarwaki tara a jihar Neja

    'Yan sanda

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar ƴansandan Najeriya ta gano wasu gawarwaki tara a kan hanyar Wawa-Lumma da ke ƙaramar hukumar Borgu a jihar Neja.

    Ana zargin ƴan bindiga ne suka kashe mutanen yayin da suke tafiya.

    Kakakin rundunar ƴansandan jihar, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar wa BBC cewa jami'an ƴansanda da sojoji sun garzaya wurin bayan samun rahoton gano gawarwakin a ranar Talata.

    Ya ce jami'an tsaron sun kwashe gawarwakin daga wurin, yayin da aka ƙara tsaurara ayyukan sintiri da bincika wuraren da ake zargin ƴan bindiga na fakewa.

    SP Abiodun ya ce an ƙara yawan jami'an tsaro a kan hanyar Wawa-Lumma da yankunan da ke kewaye da ita, domin hana sake faruwar irin wannan hari da kuma tabbatar da tsaron matafiya.

    Wannan lamari na zuwa ne yayin da ake ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro a yankin , musamman yadda matafiya ke fuskantar barazanar hare-haren ƴan bindiga.

    Hanyar na daga cikin hanyoyin da ke haɗa wasu yankunan jihar Neja, kuma hare-haren ƴan bindiga a wasu sassan jihar sun jefa matafiya da mazauna yankunan cikin fargaba.

    Rundunar ƴansandan ta ce ayyukan jami'an tsaro na ci gaba da gudana a yankin domin gano masu hannu a kisan tare da tabbatar da cewa an samu cikakken tsaro a hanyar.

  4. An yi wa matashi bulala 20 da ɗaurin shekara 13 kan yi wa yarinya fyaɗe

    An yanke wa wani matashi mai suna Aliyu Bala hukuncin ɗaurin shekara 13 a gidan yari bayan kotu ta same shi da laifin yi wa wata yarinya mai shekaru 10 fyaɗe a jihar Neja.

    Kotun ta kuma umarci a yi wa Bala bulala 20 a bainar jama'a tare da biyan diyyar naira 250,000 ga yarinyar da aka yi wa fyaden.

    Bayan yanke hukuncin, an kai Bala fadar Hakimi da ke Bosso, inda aka yi masa bulalar a bainar jama'a a gaban jama'ar gari.

    Daraktar-Janar ta Hukumar Kare Haƙƙin Yara ta Jihar Neja, Barrister Ummul-Kalthume Muhammad, ta bayyana hukuncin a matsayin wani abu da ba kasafai ake gani ba.

    Ta ce hukuncin ya nuna cewa gwamnatin jihar ba za ta yi wasa da laifukan cin zarafin yara ba.

    Ta kuma ce hukuncin bulalar a bainar jama'a na da nufin aika gargaɗi mai ƙarfi ga duk wanda ke tunanin zai iya cin zarafin yara sannan ya tsira daga hukunci.

    Hukumar ta ce hukuncin ba ya shafi iya wanda aka samu da laifin ba ne, hakan saƙo ga al'umma cewa duk wanda ya aikata laifin cin zarafin yara zai fuskanci hukunci mai tsauri a ƙarƙashin doka.

  5. Ana fuskantar kisfewar rana a Nahiyar Turai

    Kisfewar rana

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙasashen Turai sun fara fuskantar kisfewar rana, wanda zai ratsa ta kusan dukkanin ƙasashen yankin, karon farko cikin shekara 27.

    Ana sa ran miliyoyin mutane za su shaida yadda wata zai rufe rana a wani layi da ya tashi daga Greenland da Iceland, ya ratsa Tekun Atlantika zuwa yankin Iberia.

    Mutane sun yi tururuwa a arewacin Sifaniya domin kallon wannan al'amari.

    Wakilin BBC ya ce Otal Otal a Sifaniyan sun ruwaito cewa tun a watannin bayan wasu masu yawon bude ido na kasashen waje suka biya kuɗin ɗakuna, da ke sa ran kallo.

    Mutanen da ke yankin da ke da tazara daga inda za a samu cikakken kisfewar, a inda ya kai tazarar ɗaruruwan kilomitoci, za su ga wani ɓangare ne kawai na kusufin, da raguwar hasken rana da kuma sassaucin yanayin zafi.

  6. Mene ne ke rage sha'awar saduwa tsakanin ma'aurata?

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Kun san cewa mizanin saduwa tsakanin maʼaurata na raguwa?

    Masana na ci gaba da nazari game da yadda muʼamalar aure ke raguwa tsakananin maʼaurata a faɗin duniya.

    Ko me ya janyo hakan?

  7. Yahudawa ƴan kama wuri zauna sun hana wasu Falasdinawa fita daga gidansu

    Falasdinawa

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu iyalan Falasdinawa biyu na ci gaba da kasancewa a maƙale a gidajensu bayan wasu yahudawa ƴan kama wuri zauna da suka shiga ƙauyensu a Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye sun hana su fita daga gida a ranar Lahadi.

    Wani bidiyo da aka dauka ya nuna yadda sojojin Isra’ila da suka isa wurin suke gudanar da addu’a tare da yahudawan.

    Bayan wasu manyan jami’an sojin Isra’ila sun nuna damuwa, an tura ƙarin jami’an tsaro don cire wani tanti da aka kafa a ƙauyen na Qusra, da ke kudancin Nablus. Sai dai bayan da rikici ya ɓarke, jami’an tsaron sun bar wurin, wanda ya sa yahudawan suka koma.

    Falasdinawan sun ce an katse musu ruwan sha da wutar lantarki, kuma abincin su ya kusa ƙarewa.

  8. Faransa ta fara bincike kan jakadanta da ake wa zargin neman mata

    Macron

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata majiya daga ma'aikatar harkokin wajen Faransa ta tabbatar wa BBC cewa ƙasar ta fara ɗaukar matakan ladabtarwa kan jakadanta a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, Bruno Foucher.

    Ana zargin jakadan da gayyatar mata da dama zuwa gidansa da gwamnati ta bashi ya zauna a Bangui, tare da yin lalata da wasu daga cikinsu.

    Kafofin yaɗa labaran Faransa sun ce ana zargin lamarin ya faru ne tsakanin watan Janairun 2024 da Maris na 2026.

    Rahotannin sun kuma ce ana zargin jakadan mai shekaru 65 da gayyatar kusan mata 30 zuwa gidansa a wannan lokacin, inda wasu daga cikinsu suka kwana a wurin.

    Wata jami'ar diflomasiyyar Faransa ta shaida wa BBC cewa ma'aikatar harkokin wajen ƙasar ce ta bayar da umarnin gudanar da binciken a Bangui.

    Ta ce bayan samun sakamakon binciken, ministan harkokin wajen Faransa ya umarci ma'aikatar da ta fara matakin ladabtarwa kan jakadan.

    Har yanzu ba a bayyana irin matakin ladabtarwar da za a iya ɗauka kan jakadan ba, ko kuma tsawon lokacin da binciken zai ɗauka.

    Foucher shi ne jakadan Faransa a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya tun shekarar 2023.

  9. Putin ya yi barazanar ƙwace jiragen ruwan ƙasashen Turai

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Rasha vladimir Putin ya yi barazanar ƙwace jiragen ruwan ƙasashen Turai a matsayin martani ga shirin kungiyar na tare jiragen da ake zargin suna cikin “jiragen ruwan dakon mai da ke fasa kauri ko kauce wa takunkuman Rasha.

    Yayin da yake kallon wani atisayen sojojin ruwa a gabashin Rasha, Putin ya bayyana takunkumin da ake son ƙaƙabawa kan zirga-zirgar jiragen ruwan Rasha a matsayin “fashin teku kuma fashi da makami”.

    Ya ce za a tilastawa Moscow mayar da martani daidai da abin da aka mata, kuma za ta dauki duk matakin da take ganin ya dace.

  10. Dalilan da suka sa na nace kan zaɓen Muslim-Muslim - Sheikh Jingir

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Shugaban majalisar malamai ta ƙungiyar Izala, Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ce ya yi tsammanin zai sha suka lokacin da ya yi wasu kalamai game da takarar Muslim-Muslim. Jingir ya kuma ce ba ya da na sanin matsayarsa.

  11. A shirye muke mu ɗauki tsawon lokaci muna yaƙi - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce a shirye take ta ɗauki tsawon lokaci tana yaƙi idan buƙatar hakan ta taso, tare da ci gaba da gudanar da ayyukan soji na tsawon lokaci.

    Mataimakin babban jami’in gudanarwa na rundunar sojin ƙasar, Alireza Sheikh, ya bayyana cewa Iran na da ƙarfin da za ta iya mayar da martani ga duk wata barazana, har ma da ɗaukar matakan kariya.

    A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Mehr, Alireza Sheikh ya ce dabarun da Iran ke amfani da su sun tilasta wa Amurka sake nazarin manufofinta akai-akai, yana mai cewa Tehran na ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fagen siyasa da tsaro.

    Ya kuma ce Iran ta sauya daga tsarin kare kai zuwa tsarin hana barazana da kuma ɗaukar matakai kai tsaye idan hali ya buƙata, yana mai jaddada cewa ƙasar na da isassun kayan aiki da dabarun ci gaba da yaƙi na dogon lokaci.

    Jami'in ya ƙara da cewa ikon Iran na ƙera makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa na daga cikin manyan abubuwan da ke ƙarfafa shirinta na ci gaba da gudanar da ayyukan soja cikin dogon lokaci.

  12. 'Iran ta ce babu tattaunawar tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka'

    ...

    Asalin hoton, IRNA

    Wani babban jami’in gwamnatin Iran ya ce babu wata tattaunawa da ake yi da Amurka domin tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Tehran da Washington in ji kamfanin dillancin labaran Reuters.

    Jami’in, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya ce babu abin da Iran za a tsawaita, domin a cewarsa Amurka ta karya yarjejeniyar wucin-gadi sa’o’i 48 bayan ƙulla ta, sannan ta janye daga cikinta bayan wasu kwanaki.

    Wannan na zuwa ne yayin da ministan harkokin cikin gida na Pakistan, Mohsen Naqvi, ya kai ziyara Tehran inda ya gana da shugaban Iran da kuma ministan harkokin wajen ƙasar, a wani yunƙuri da ake dangantawa da ƙoƙarin sasanta rikicin da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.

    A ranar 17 ga Yuni ne Amurka da Iran suka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna wadda ta tanadi tsagaita wuta da kuma wa’adin kwanaki 60 na tattaunawar kawo ƙarshen yaƙi.

    Sai dai bayan sabbin rikice-rikice da musayar hare-hare, ɓangarorin biyu sun zargi juna da karya yarjejeniyar.

  13. Ghana ta kafa sabuwar dokar ƴaƙi da fashin teku a Gulf na Guinea

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Ghana ta kafa wata sabuwar doka da nufin magance matsalolin tsaro a yankin Tekun Gulf na Guinea.

    Dokar wadda Majalisar Dokokin ƙasar ta amince da ita, za ta taimaka wajen yaƙi da fashin teku, fashi da makami a ruwa da sauran laifukan da ke barazana ga harkokin jiragen ruwa.

    Hukumar Kula da Harkokin Teku ta Ghana ta ce ta yi aiki tare da Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya mai yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi da Laifuka (UNODC) da Tarayyar Turai domin wayar da kan hukumomin tsaro kan yadda za a aiwatar da sabuwar dokar.

    Mataimakin darakta janar na hukumar, Mubarick Masawudu, ya bayyana dokar a matsayin wani babban mataki na daƙile ayyukan masu laifi da ke kawo cikas ga harkokin sufurin teku.

    Sai dai masana sun yi gargaɗin cewa doka kaɗai ba za ta wadatar wajen kare yankin ruwan Ghana ba.

    Wani masanin harkokin tsaro na Ghana, Adib Sana, ya shaida wa BBC cewa nasarar dokar za ta dogara ne da ingantaccen sa ido, musayar bayanan sirri tsakanin hukumomi, haɗin gwiwa da maƙwabtan ƙasashe, da kuma ƙarfafa ikon gurfanar da masu laifi a gaban kotu.

    Ya kuma nuna damuwa kan yadda wasu jiragen ruwa na Rasha da ake kira shadow fleet ke amfani da tutocin ƙasashe masu tasowa domin kauce wa takunkuman ƙasa da ƙasa.

  14. Tinubu ya amince da farfaɗo da rijiyoyin man fetur da ke tsakiyar teku

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Najeriya ta amince da wani sabon tsarin haraji da dokoki da nufin farfaɗo da harkar hako man fetur da iskar gas daga rijiyoyin mai da ke tsakiyar teku.

    Gwamnatin ta yi imanin cewa matakin zai iya jawo jarin da ya kai dala biliyan 50 cikin harkar mai da gas, tare da ƙara samar da ayyukan yi da kuma kuɗaɗen shiga ga ƙasar.

    Babban gwajin wannan sabon tsarin shi ne ko kamfanonin mai daga ƙetare za su amince su ci gaba da aikin Bonga South West-Aparo, wani shiri da ya kwashe kimanin shekaru 30 ana shirin aiwatar da shi.

    Ana sa ran aikin zai buƙaci jarin farko na kusan dala biliyan 10, kuma idan aka kammala shi zai iya samar da ganga 150,000 na ɗanyen mai a kowace rana.

    Gwamnatin Najeriya na sa ido kan ko kamfanin Shell, wanda ke gudanar da rijiyar man Bonga, zai yanke shawarar fara aikin a shekarar 2027.

    Hakan na zuwa ne a lokacin da Najeriya ke fuskantar raguwar saka jari a harkar mai da gas sakamakon satar mai, rashin tsaro da kuma ficewar wasu manyan kamfanonin mai daga wasu rijiyoyin da ke kan tudu.

    A lokaci guda, gwamnati na kuma shirin sauya wasu ƙa'idojin rarrabawa da farashin ɗanyen mai ga matatun mai na cikin gida, domin rage musu tsadar samar da mai.

    Ana sa ran matakan za su taimaka wajen ƙara yawan man da ake haƙowa da jawo ƙarin jari da kuma tabbatar da cewa ana sarrafa mafi yawan ɗanyen man Najeriya a cikin ƙasar.

  15. Abin da ya sa muka bai wa gwamnoni wa'adi kafin shiga yajin aiki - ASUU

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya (ASUU) ta umarci malaman jami'o'i 20 da su fara shirye-shiryen shiga yajin aikin gama-gari, bisa zargin cewa gwamnatin tarayya da wasu gwamnatocin jihohi sun gaza cika alƙawuran da suka ɗauka a yarjejeniyar da aka ƙulla da ƙungiyar tun a shekarar 2025.

    Ƙungiyar ta ce ta bai wa gwamnatocin da abin ya shafa wa'adin mako biyu domin magance matsalolin da suka rage.

    Shugaban ASUU na shiyyar Kano, Dakta Abdulrazaq Ibrahim Fagge, ya ce an ɗauki matakin ne bayan taron da uwar ƙungiyar ta gudanar a Abuja sakamakon ƙorafe-ƙorafen da ta samu daga wasu jami'o'i, musamman na jihohi.

    Ya ce duk da yarjejeniyar da aka cimma a watan Disambar 2025 kan sabbin alawus-alawus da wasu sauye-sauye a tsarin tafiyar da jami'o'i, har yanzu wasu gwamnatocin jihohi ba su aiwatar da abin da suka amince da shi ba.

    ASUU ta ce yayin da gwamnatin tarayya ta fara cika nata alƙawuran tun daga watan Janairun wannan shekarar, wasu gwamnoni sun gaza yin haka.

    Ƙungiyar ta zargi wasu gwamnatocin jihohi da fifita ayyukan da ba su da muhimmanci fiye da ilimi, tana mai cewa babu shirin sake zama da gwamnati a yanzu saboda an shafe watanni takwas ana tattaunawa ba tare da samun ci gaba ba.

    Ta gargadi cewa rassan da abin ya shafa za su shiga yajin aiki idan wa'adin mako biyun ya cika ba tare da an warware matsalolin ba.

  16. Iran za ta jima bata ƙera makamin mukiliya ba - Isra'ila

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Isra'ila ta Mossad, Yossi Cohen, ya ce duk da cewa Iran na da sinadarin uranium mai wadatar kaso 60 cikin 100, hakan ba yana nufin tana gab da ƙera makamin nukiliya ba.

    Ya ce har yanzu ƙasar na da sauran aiki mai yawa kafin ta kai matakin kera irin wannan makami.

    Yossi Cohen ya bayyana haka ne a wani taro da aka gudanar ranar Talata, inda ya ce hukumar Mossad ta shafe lokaci tana bibiyar cibiyar nukiliyar Fordow ta Iran da ke ƙarƙashin ƙasa tare da gudanar da bincike mai zurfi game da ita.

    Sai dai tsohon shugaban leƙen asirin bai yi ƙarin bayani kan irin bayanan da suka tattara daga cibiyar ta Fordow ba.

  17. NiMet ta yi gargaɗin ambaliya a Sokoto, Kaduna, Neja da wasu jihohi 10 a watan Agusta

    .....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi gargaɗin yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa a jihohi 13 tsakanin ranar 11 da 20 ga watan Agustan 2026.

    Jihohin da ta ce ke fuskantar barazanar sun haɗa da Sokoto, Zamfara, Kebbi, Neja, Kaduna, Nasarawa, Adamawa, Filato, Benue, Kogi, Taraba, Cross River da Akwa Ibom.

    Hukumar ta ce hasashen ya samo asali ne daga nazarin yawan ruwan sama da ake sa ran samu, yanayin danshin ƙasa, ƙarfin magudanan ruwa, yanayin ƙasa da kuma yanayin madatsun ruwa.

    Ta yi gargaɗin cewa ambaliyar ka iya shafar yankunan da ke fama da ambaliya, ƙananan wurare, birane da kuma al'ummomin da ke kusa da koguna, lamarin da zai iya haddasa rufe hanyoyi da tsaikon sufuri.

    NiMet ta kuma ce ambaliyar na iya lalata gonaki, amfanin gona da dabbobi tare da shafar wutar lantarki da hanyoyin sadarwa.

    Hukumar ta shawarci jama'a su riƙa bibiyar hasashen yanayi da gargaɗin ambaliya, su guji wucewa ta hanyoyin da ruwa ya mamaye, yayin da ta buƙaci hukumomin agajin gaggawa da manoma su ɗauki matakan kariya domin rage illolin da ka iya tasowa.

  18. 'Yan Pakistan uku sun mutu a harin Houthi kan wani jirgin ruwa

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan Harkokin Wajen Pakistan, Mohammad Ishaq Dar, ya sanar a ranar Laraba cewa 'yan ƙasar Pakistan uku sun mutu sakamakon harin da mayaƙan Houthi suka kai kan wani jirgin ruwa a Tekun Bahar Maliya.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafin X, Ishaq Dar ya ce: "'Yan ƙasar Pakistan uku sun rasa rayukansu, yayin da mutum guda ya jikkata a wannan lamari."

    Kalaman nasa sun zo ne kwana guda bayan hukumomin tsaron gaɓar tekun Yemen suka tabbatar da cewa aƙalla mutum shida ne suka mutu a harin da mayaƙan Houthi suka kai kan wani jirgin ruwa a gaɓar ƙasar.

    Har yanzu ba a bayyana ƙarin cikakkun bayanai kan mutanen da suka mutu ko kuma yanayin jirgin ruwan da harin ya rutsa da shi ba.

  19. Sabon jirgin da aka sauya min ya ma fi haɗarin fuskantar harin Iran - Trump

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sabon jirgin sojin da aka sauya masa a lokacin da yake komawa Amurka daga Turkiyya ya fi haɗarin fuskantar harin Iran fiye da jirgin shugaban ƙasar Amurka Airforce one da ya bari.

    Da yake magana da manema labarai, Trump ya ce ya bi shawarar hukumomin tsaro inda ya koma Amurka ta wani jirgin daban bayan halartar taron ƙungiyar NATO a Turkiyya kusan wata guda da ya wuce.

    Rahotannin kafofin yaɗa labaran Amurka sun ce jami'an tsaro sun gano wata babbar barazana daga Iran ta yiwuwar harba makami mai linzami kan jirgin Trump lamarin da ya sa ya sauya jirgi a asirce.

    Trump ya kuma yi iƙirarin cewa Amurka ce ke da cikakken iko da Mashigar

  20. Za mu farmaki cibiyoyin Amurka da na ƙawayenta idan aka sake kai mana hari - Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Jami'in dakarun juyin juya halin Iran (IRGC), Hossein Mohebi, ya ce Amurka da ƙawayenta za su fuskanci hare-hare kan muhimman cibiyoyinsu idan aka sake kai wa Iran hari.

    Ya yi gargaɗin cewa Iran za ta iya kai farmaki kan tashoshin samar da wutar lantarki, layukan isar da makamashi da sauran muhimman tsare-tsaren Amurka da na ƙawayenta.

    Mohebi ya kuma ce, manyan sassan cibiyoyin sadarwa na duniya da ke da alaƙa da intanet na iya fuskantar barazana idan aka sake kai wa Iran hari.

    Ya ƙara da cewa a halin yanzu babu wani jirgin ruwa na Amurka da ke cikin ruwan Tekun Fasha.

    Kalaman kakakin IRGC na zuwa ne sa'o'i kaɗan bayan shugaban Amurka Donald Trump ya ce ba yarda da Iran domin, a cewarsa, tana yi masa ƙarya.

    Trump ya kuma jaddada cewa Mashigin Hormuz yana ƙarƙashin ikon Amurka kuma mallakin Amurka ne.