Amurka za ta sha mamaki idan ta koma yaƙi da mu - Iran

Asalin hoton, EPA/Shutterstock
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya mayar da martani ga kalaman barazanar shugaban Amurka, Donald Trump, dangane da yiwuwar sake kai hari kan Iran, inda ya ce: “Amurka za ta sha mamaki idan ta koma fagen yaƙi da mu.”
Araghchi ya yi wannan gargaɗi ne a wani sabon saƙo da ya wallafa a shafin X inda ya ce
“Watanni bayan fara yaƙin da aka yi da Iran, Majalisar Dokokin Amurka ta amince da lalata jirage masu yawa da darajarsu ta kai biliyoyin daloli. Yanzu kuma an tabbatar a hukumance cewa rundunar sojinmu mai ƙarfi ita ce ta farko a duniya da ta harbo shahararren jirgin yaƙin F-35 ta Amurka.”
A ƙarshen saƙon nasa, ya yi iƙirarin cewa:
“Da darussan da muka koya da kuma ilimin da muka samu, ku tabbatar cewa komawa fagen yaƙi zai kawo ƙarin abubuwan mamaki.”
A jiya ne shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi iƙirarin cewa a daidai lokacin da ake shirin kai wani babban harin soji kan Iran, ya bayar da umarnin dakatar da harin bayan roƙon shugabannin yankin.








