Tinubu ya jajanta kan kisan sojoji a Borno

Asalin hoton, X/Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya jajanta wa al'ummar ƙasar kisan da aka yi wa sojoji a wani hari da mayaƙa suka kai kan wani sansanin soji a jihar Borno, arewa maso gabashin ƙasar.
"Ina miƙa saƙon ta'aziyyata ga iyalan jajirtattun sojojinmu ƙarƙashin jagorancin Birgediya Janar Oseni Omoh Braimah, waɗanda suka rasa rayukansu wajen kare ƙasarmu a jihar Borno," kamar yadda shugaban ya bayyana a wani bayani da ya fitar a jiya Alhamis.
A ɗaya ɓangare, cikin wata sanarwa, rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun daƙile harin da aka kai kan sansanin soji a garin Benisheik ranar Alhamis, sai dai rundunar ba ta tabbatar ko ƙaryata kashe sojoji ba.
Wasu mazauna yankin da abin ya faru sun shaida wa BBC cewa babban sojan da ya jagoranci yunƙurin dakile harin Birgediya Janar Oseni Braimah na cikin waɗanda aka kashe.
Kafar yaɗa labarai ta AFP ta bayar da rahoton kashe babban sojan, inda ta kafa hujja da bayanai daga majiyoyin tattara bayanan sirri, duk da cewa sojojin Najeriya ba su tabbatar da hakan ba.
Harin na cikin hare-hare na baya-bayan nan da masu iƙirarin jihadi ke kaiwa kan sansanonin soji a arewa maso gabashin Najeriya, inda mayaƙa suka kwashe sama da shekara 10 suna kai hare-hare.


