KAI TSAYE, Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya 02/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku rahoto kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Laraba 02 ga watan Afrilun 2026.

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida da Haruna Kakangi

  1. Ƙauyen da ake zargin ƴansanda sun ƙona a Kano

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    Al'ummomin wasu garuruwa a yankin ƙaramar hukumar Wudil a jihar Kano, da ke Najeriya, sun zargi ƴansanda da ƙone musu gidaje da wuraren sana'a da kayan abinci da kuma dabbobi a sanadiyyar wata hatsaniya kan mallakar gonaki.

    Rikicin, wanda yanzu haka yake gaban ƙotu, na da alaƙa da batun mallakar gonakin wata fadama a yankin ƙananan hukumomin Wudil da Bunkure.

  2. Za mu bar jiragen da ba su da alaƙa da Amurka su bi ta mashigar Hormuz - Iran

    ....

    Asalin hoton, Anadolu via Getty Images

    Iran ta ce za ta buɗe mashigar Hormuz ga jiragen ruwa da ba su da alaka da Amurka ko Isra’ila.

    Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje ta Iran, Esmail Baghaei, ya ce Iran za ta bar jiragen ruwa su wuce ta mashigin Hormuz – hanya mafi muhimmanci wajen jigilar man fetur – muddin “na su da alaƙa da Amurka ko Isra'ila.”

    A wata hira da tashar talabijin Newzroom Afrika, Baghaei ya ce jiragen ruwa za su samu izinin wucewa ta mashigin ne “bayan haɗa kai da hukumominmu kamar yadda ya dace.”

    Yayinda yake magana kan rikicin gabaɗaya, Baghaei ya ce Iran ba za ta lamunci “zagayowar yaƙi da tattaunawa ko tsagaita wuta ba".

    A watan Yuni, wani yaƙi na kwanaki 12 tsakanin Iran da Isra’ila ya haɗa da hare-haren Amurka kan wasu wuraren nukiliya da sojin Iran.

    Ya ce, “Sun ce mu dakata, mun dakata, amma bayan watanni tara, su suka sake farawa.”

  3. Iran ta ce za ta faɗaɗa hare-harenta bayan barazanar Trump

    ...

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Wani mai magana da yawun rundunar sojin Iran ya yi gargaɗi cewa Amurka da Isra’ila za su “ɗanɗana kuɗarsu” kan tashin hankalin da suka haifar sakamakon hare-haren da suke kai wa inda ya ce Iran za ta faɗaɗa hare-harenta bayan narazanar Trump na jaddada anniyarsa ta ci gaba da kai mata hare-hare

    A cikin wata sanarwa da gidan jaridar Tasnim da kafofin Fars suka fitar, mai magana da yawun rundunar ya ce kasashen biyu ba su da cikakken bayani game da ƙarfin soji da kayan aikin Iran.

    Ya kuma bayyana cewa samar da kayan yaƙi a Iran “yana gudana a wurare da ba ku sani ba kwata-kwata,” inda ya yi watsi da iƙirarin Trump cewa Iran ta yi ƙasa da kayan yaƙi sosai.

  4. Mun kakkaɓo wani jirgi mara matuƙi da aka harba mana - Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar juyin juya halin Iran ta tabbatar da cewa dakarunta sun kakkaɓo wani jirgin yaƙi mara matuƙi ƙirar Hermes 900 da aka harba mata.

    Rundunar ta ce ta kakkaɓo makamin ne daga sararin samaniyar birnin Shiraz a safiyar yau.

    Yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila dai na ƙara tsananta inda duka ɓangarorin ke ci gaba da kai wa juna hari da makamai masu linzami da na jiragen yaƙi mara matuƙa.

  5. Iran ta zantar da hukunci kisa kan ɗaya daga cikin masu zanga-zanga

    Hukumar labarai ta Mizan wacce ke da alaƙa da kotun Iran ta ce, an kashe Amir Hossein Hatami, ɗaya daga cikin waɗanda aka kama yayin zanga-zangar watan Janairu, a yau.

    Mizan ta bayyana cewa, “Amir Hossein Hatami tare da wasu masu tayar da tarzoma sun kai hari wani muhimmin wurin soja a Tehran, bayan sun lalata shi tare da ƙona shi.”

    Kafofin shari’a na Iran sun rubuta cewa, “Bayan jami’an tsaro sun kama Hatami kuma ya amincewa da tuhumar da ake masa, ya bayyana rawar da ya taka wajen lalatawa da ƙona wannan wurin na soja lokacin shari’a.”

    Har yanzu ba a fitar da cikakken bayani ba game da tuhumar da kuma yadda aka gudanar da shari’ar ba.

    Wannan shi ne hukuncin kisa ta biyu da aka yanke a Iran cikin wannan wata.

  6. Tinubu zai kai ziyara Jos yau Alhamis

    ...

    Asalin hoton, Baya Onanuga/X

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai kai ziyara birnin Jos a yau Alhamis, biyo bayan harin da aka kai ranar Lahadi da ta gabata wanda ya yi sanadin mutuwar fiye da mutane 25.

    Shugaban ya ce manufar ziyarar ita ce jajanta wa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

    Ya ce, “Babban abin da ya rataya a wuyana a wannan lokaci shi ne tsayawa tare da al’ummar Plateau, waɗanda ke ƙoƙarin yaɗa tsoro ba za su yi nasara ba. Za mu ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro tare da tabbatar da an yi adalci.”

    Ziyarar na zuwa ne kwanaki huɗu bayan harin, inda shugaban ya soke wata tafiya da ya shirya zuwa Ogun da wasu jihohi domin ayyukan more rayuwa da kasuwanci da bunƙasar tattalin arziki.

    Jihar Plateau, inda Jos take, ta daɗe tana fama da rikice-rikice masu alaƙa da bambancin ƙabilu da addinai, da kuma rikicin makiyaya da manoma.

    Har yanzu babu wata ƙungiya da ta ɗauki alhakin harin na baya-bayan nan.

    Mahukunta sun sanya dokar hana fita na kwanaki biyu a ranar Litinin domin dawo da zaman lafiya, amma an sake samun tashin hankali a ranar Laraba a yankin Angwan Rukuba bayan sassauta dokar.

  7. Darajar hannayen jari ta sake faɗuwa bayan Trump ya ce zai ci gaba da yaƙi da Iran

    ....

    Asalin hoton, Reuters/Getty Images

    Kasuwannin hannayen jari na duniya sun sake dagulewa, biyo bayan jawabin da shugaba Trump din ya gabatar na jaddada aniyarsa ta ci gaba da yakin har nan da makwanni.

    Farashin man fetur ya haura sama da dala 105 kan kowace ganga, yayin da ‘yan kasuwa ke ƙoƙarin fahimtar abin da ka ce ya zo.

    Rahotanni sun nuna cewa irin bayanai masu cin karo da juna da shugaban ke yi, na janyo wa kasuwa rashin tabbas wajen fahimtar inda aka sanya gaba.

    Babu dai wani karin bayani mai gamsarwa daga shugaban kan batun rufe mashigin Hormuz, wadda ke da matuƙar muhimmanci wajen jigilar man fetur a duniya.

    Trump ya ce ya rage wa kasashen da ke amfani da mashigin su je su bude shi da kansu, ko kuma su jira ya bude kansa da kansa idan aka kawo karshen yakin.

  8. Trump ya ce Amurka na gab da cimma manufofinta a Iran

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce, kasar na kan hanyar cimma dukkan manufofinta a Iran nan ba da jimawa ba.

    A wani jawabi da ya gabatar ta talabijin, Trump ya lashi takobin tsananta hare-hare kan Iran ɗin cikin makonni biyu zuwa uku masu zuwa.

    Ya kuma yi gargadin cewa idan ba a cimma wata yarjejeniya a wannan lokaci ba, Amurka za ta kai munanan hare-hare kan dukkan tashoshin samar da lantarkin Iran din.

    Jawabin ya bar tambayoyi da dama ba tare da amsa ba, yana mai cewa har yanzu shugaban bai fito karara ya bayyana yadda yake ganin nasara za ta kasance ba.

  9. Me dokar Najeriya ta ce kan masu son tsayawa takara idan ba su ajiye muƙaminsu ba?

    ....

    Asalin hoton, BAYO ONANUGA/X

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya umurci duk masu riƙe da muƙaman siyasa da ke son tsayawa takara a zaɓen 2027 su yi murabus kafin ko a ranar 31 ga Maris, 2026.

    A wata takardar umarni, wacce sakataren gwamnatin tarayya, George Akume, ya sanya wa hannu, ta bayyana cewa dole dukkan waɗanda ke da ƙudurin su ajiye aiki.

    Tinubu ya jaddada cewa matakin ya zama dole domin tabbatar da bin dokokin zaɓe sau da ƙafa, da wanzar da gaskiya da adalci a cikin tsarin siyasa, da kuma tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe.

    Ya buƙaci jami'an da abin ya shafa su tabbatar sun mika wasiƙun murabus ɗinsu ga ofishin sakataren gwamnatin tarayya, kafin cikar wa'adin da aka bayar.

    Umurnin ya shafi ministoci, masu ba da shawara, daraktoci da shugabannin hukumomi.

  10. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis ga wannan shafin namu na BBC Hausa, inda za mu ci gaba da kawo muku labaran kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.