Yaƙin Iran da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku bayanai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Juma'a 29 ga watan Mayun 2026

  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Sadis Buba
  • Pantami
  • xxx
  • Nafiu Gombe
  • Mace da ƴarta mai lalaurar Autism
  • wata mata
  • BBC reporter

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Trump na tunanin amincewa da yarjejeniyar tsayar da yaƙin Iran

    Donald Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaba Trump ya ce zai bayyana matsayarsa ta ƙarshe kan ko zai cimma yarjejeniya da Iran.

    Hakan na zuwa ne gabanin tattaunawar da zai yi da makusantansa, inda ya nace cewa dole Iran ta buɗe mashigar Hurmuz ta kuma amince ba za ta taɓa mallakar makamin Nukiliya ba.

    Ya kuma ƙara da cewa za a lalata sinadarin Uranium na Iran.

    Jami'an Iran sun bayyana kalaman nasa da cewa ya cakuɗa gaskiya da ƙarya, inda suka ce a daftarin yarjejeniyar babu batun buɗe mashigar Hurmuz sakaka, ko kuma lalata sinadaran makamin nukiliyarta.

    Tehran ta ce ita ma har yanzu ba ta yanke hukunci na ƙarshe kan amincewa da tsawaita yarjejeniyar na tsawon kwana sittin domin bayar da damar cigaba da tattaunawa ba.

  2. Zan haskaka Najeriya da lantarki don bunƙasa tattalin arziƙi – Tinubu

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na warware ƙangin da ɓangaren lantarkin ƙasar ke ciki ta hanyar ƙarfafa kayan samar da lantarki da kuma zuba jari a ɓangaren makamashi maras guraɓata muhalli.

    A wani bayani da Tinubu ya fitar na cika shekara uku bayan hawa kan mulki, shugaban ya ce “babu wata ƙasa da za ta bunƙasa a cikin duhu.

    “A duk lokacin da lantarki ta bunƙasa, harkokin kasuwanci za su haɓɓaka, masana’antu za su bunƙasa sannan za a samu ayyukan yi kuma iyali za su shiga walwala,” a cewar Tinubu.

    Najeriya na fama da matsanancin ƙarancin wutar lantarki na tsawon shekaru, wanda hakan ya janyo durƙushewar masana’antu da rasa ayyukan yi.

    Haka nan ɓangaren lantarki na ƙasar na fama da matsaloli na rashawa, inda a cikin wannan watan na Mayu wata kotu ta yanke wa tsohon ministan ƙasar hukuncin ɗaurin sama da shekara 70.

  3. WHO na neman ƙarin kuɗi don daƙile Ebola a Congo

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya na neman ƙarin kuɗi don taimaka wa Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo don ta samu ta yaƙi ɓarkewar cutar Ebola.

    Da yake magana a Kinshasa, Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce kashi ɗaya bisa uku na tallafin da ake nema aka samu zuwa yanzu.

    Amurka ta yi alƙawarin bayar da ƙarin dala miliyan 80 domin tallafa wa ƙoƙarin da ake a Congo da Uganda inda aka tabbatar da wasu mutum bakwai sun kamu da cutar.

    WHO ta ce mutum na farko da ya warke daga cutar tuni aka sallame shi daga asibiti.

    Cutar ta kashe fiye da mutum 200 inda ake zargin dubbai sun kamu da cutar.

  4. An samu raguwa mafi girma a yawan al'ummar Japan

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙidayar baya-bayan nan da aka yi ta yawan jama'ar Japan ta nuna cewa ƙasar ta samu raguwa mafi girma a yawan al'ummarta.

    Adadin ya ragu da fiye da miliyan uku cikin shekaru biyar zuwa miliyan 123.

    Japan ta jima a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashe da ba sa yawan haihuwa a duniya ga kuma ƙaruwar tsofaffi.

    Matakan da aka bijiro da su don mutane su yi aure su kuma hayayyafa ba su cika yin nasara ba.

  5. Mun shimfiɗa tubalin magance matsalolin Najeriya - Tinubu

    Shugaba Tinubu

    Asalin hoton, Presidency

    Shugaba Bola Tinubu ya ce ya fahimci irin sadaukarwar da iyalai suka yi a shekarun baya-bayan nan inda kuma ya bayyana fatansa na samun ci gaba a Najeriya.

    Ya kuma ce har yanzu tsaro na ka gaba a manufofin gwamnatinsa yayin da ƙasar ke ci gaba da tunkarar ƙalubale gadan-gadan kuma ana samun ci gaba yana mai bai wa ƴan Najeriya tabbacin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ganin ƴan Najeriya suna harkokinsu ba tare da zullumi ba.

    Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa na bikin shekara uku kan mulki inda ya ce gwamnatinsa ba ta kai ga magance matsalolin ƙasar ba amma sun dasa tubalin samun ci gaba.

    Ya ce aikin da ke gabansu shi ne tabbatar da cewa al'ummar Najeriya sun amfana daga sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi.

    Shugaban ya kuma ce gwamnatinsa za ta ci gaba da tabbatar da cewa farashin kayan masarufi da ya sauka tun 2023/2024 bai tashi ba.

    Ya kuma ce yana aiki don rage kuɗin sufuri kasancewar masu ababen hawa na mayar da motocinsu zuwa masu amfani da iskar gas da motoci masu amfani da lantarki.

  6. An kama ɗalibai takwas kan zargin hannu a mummunar gobarar Kenya

    ..

    An kama ɗalibai takwas kan zargin suna da hannu a mummunar wutar da ta tashi a wata makarantar kwana ta ƴanmata da ke Gilgil a Kenya, lamarin da ya yi sanadin mutuwar ɗalibai 16.

    Sashen binciken manyan laifuka a ƙasar ya tabbatar da kamen inda ya ce an gano waɗanda ake zargin sakamakon binciken farko-farko da aka yi kan gobarar da hukumomi ke zargin hari ne aka kai da gangan.

    Gobarar ta tashi ne a ɗakin kwanan ɗalibai inda ta lalata wani ɓangare na ginin mai hawa biyu.

    Hukumomi sun ce ƙwararru na ci gaba da yin bincike don gano musabbabin tashin wutar.

    Zuwa yanzu masu binciken sun tattauna da ɗalibai da malamai da shaidu yayin da kuma suke nazarin kyamarar tsaron da aka sa duk a ƙoƙarinsu na gano yada wutar ta tashi.

  7. Isra'ila da Rasha na cikin ƙasashe masu cin zarafin lalata lokacin yaƙi - MDD

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta sanya sunan Isra'ila da Rasha cikin wani jerin ƙasashe da aka yi wa tambari da masu aikata cin zarafin lalata a lokutan yaƙi.

    Cikin wani rahoton shekara-shekara na Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres na shekarar 2025 an tabbatar da aukuwar wasu nau'ikan cin zarafi da jami’an sojin Isra’ila da ‘yan sanda ko masu gadin gidan yari suka aikata kan mutum 31 daga Gaza da Gabar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, ciki har da yara ƙanana.

    Rahoton ya ce a wasu lokutan jami'ai da dama ne ke taruwa suna yi wa jama'a fyaɗen rubdugu, baya ga wani mutum da aka tarar an harbarwa al’aurada gangan.

    Isra’ila, wadda aka sanya sunanta tare da ƙungiyar Hamas cikin jerin, ta nuna fushinta kan matakin tare da musanta zarge-zargen.

    Tun da farko jakadan ƙasar a Majalisar Dinkin Duniya ya ce ƙasarsa za ta dakatar da duk wata hulɗa da shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya.

    Dangane da Rasha kuwa, rahoton ya ce dakarunta sun aikata ɗaruruwan take haƙƙin ɗan adam a Ukraine, ciki har da fyaɗe da kuma amfani da lantarki wajen azabtarwa.

    Moscow ba ta ce komai ba game da rahoton.

  8. Yadda ake al'adar Tareni ta sarrafa naman layya a Sokoto

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama don ganin yadda Sakkwatawa suke al'adar nan ta Tareni - wata hanya ta sarrafa naman sallah
  9. Lebanon ta soki munanan hare-haren Isra'ila a ƙasarta

    ...

    Asalin hoton, Mohammed Zaatari / AP

    Firaministan Lebanon ya ce babu wani dalili da zai iya zama hujja kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa da kuma umarnin da take bayarwa na kwashe jama’a daga kudancin ƙasar.

    Nawaf Salam ya ce matakan da Isra’ilar ke ɗauka, ciki har da na lalata wuraren tarihi, sun kai a kira su da hukuncin kan mai uwa da wabi, wanda ya ce ya saɓawa dukkan dokoki da ƙa’idojin ƙasa da ƙasa.

    Mutane da dama sun mutu a baya-bayan nan sakamakon faɗaɗa hare-haren Isra’ila, wanda a ranar Alhamis ya shafi Beirut, babban birnin ƙasar.

    Isra’ila ta ce tana kai hare-haren ne kan ƙungiyar Hezbollah wadda ke ci gaba da harba jirage marasa matuƙa zuwa cikin ƙasar.

    Sojojin Isra’ila sun umarci mazauna kusan kashi ɗaya cikin takwas na Lebanon da su koma arewacin ƙasar.

  10. Aminu Abdussalam ne ɗantakararmu na gwamna a 2027 - Kwankwaso

    ..

    Asalin hoton, @KwankwasoRM/X

    Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sanar da zaɓar Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin wanda zai yi wa jam'iyyar NDC takarar gwamna a zaɓen 2027.

    Kwankwaso ya faɗi haka ne a saƙon da ya wallafa a shafinsa na X inda ya ce Dakta Nasiru Yusuf Gawuna kuma zai nemi kujerar sanata don wakiltar al'ummar Kano ta Tsakiya.

    Ya ce an ɗauki matakin bisa gaskiya da biyayya da kuma ƙwarewa - ɗabi'un da har yanzu ginshiƙai ne a ci gaba da haɗin kan jam'iyyarmu da kuma Kwankwasiyya.

    Sanarwar ta zo ne bayan shafe kwanaki ana tattaunawar sirri a tsakanin mambobin Kwankwasiyya da kuma tuntuɓar manyan ƴan siyasa.

    Kwamared Gwarzo ya sauka daga muƙaminsa na mataimaki gwamnan jihar Kano a watan Maris sakamakon rikicin siyasa tun bayan da gwamna Abba Kabir Yusuf ya fice daga NNPP ya koma jam'iyyar APC mai mulki.

  11. Gwamnati na duba yiwuwar sa takunkumin tafiye-tafiye kan Ebola

    ..

    Asalin hoton, Femi Gbajabiamila/FB

    Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar sa takunkumi kan jiragen da suka taso daga ƙasashen da ke fama da cutar Ebola a wani ɓangare na sabbin matakai don kare ɓarkewar cutar a ƙasar.

    Shugaban ma'aikata a Fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a wani babban taro da aka yi a Legas domin nazari kan shirin da Najeriya ta yi na tunkarar Ebola.

    Gbajabiamila, wanda ya ja ragamar taron ya ce shawarwarin ƙaƙaba takunkumin tafiye-tafiye za a maye su da keɓe fasinjojin da ke nuna alamun kamuwa da ƙwayar cutar Ebola.

    Taro ya samu halartar manya jami'ai da suka haɗa da Darakta Janar na hukumar daƙile yaɗuwar cututtuka NCDC, Jie Idris da Ministan cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo da kwamishinan lafiya na jihar Legas, Akin Abayomi.

    Gidan Talabijin na Channels ya ruwaito Gbajabiamila yana bayyana cewa an yi wa Shugaba Tinubu ƙarin bayani kan halin da ake ciki gae da cutar a Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Congo da Uganda, inda ya ba da tabbaci cewa gwamnati za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ba a samu ɓullar cutar a Najeriya ba.

  12. Amurka da Iran na dab da cimma yarjejeniya - JD Vance

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce Washington da Tehran na dab da cimma yarjejeniya kan tsawaita tsagaita wutar da ke tsakaninsu, wadda rahotanni suka ce za ta haɗa da sake bude mashigar ruwa ta Hormuz a hankali.

    Sai dai ya ce har yanzu akwai wasu batutuwa da ba a warware ba, ciki har da batun sinadarin uranium na Iran din, don haka har yanzu lokaci bai yi ba da za a tabbatar ko yaushe za a cimma yarjejeniyar.

    Wakiliyar BBC ta ce tsarin da ake magana a kansa ba wai yana nufin cimma yarjejeniya ta dindindin ba ne, illa dai yarjejeniya ce ta fahimtar juna da za ta tsawaita tsagaita wutar da kwanaki sittin, don hakan ya buɗe ƙofar cimma yarjejeniya ta dindindin cikin watanni biyu.

    Ana kyautata zaton yarjejeniyar za ta ƙunshi janye shingen da Amurkar ta sanya wa jiragen dakon man Iran da ke tashi daga tashoshin jiragen ruwanta, da kuma sassauta wasu takunkumai.

    Har yanzu Tehran ba ta ce komai ba kan batun.

  13. Barka da Juma'a

    Muna muku barka da kasancewa tare da Shafin Kai Tsaye na BBC Hausa a daidai wannan lokaci.

    Kamar kullum wannan shafi zai kawo muku labarai kan abubuwan da ke faruwa game da yaƙin Iran da kuma wainar da ake toyawa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.

    Nabeela Mukhtar Uba ce za ta kasance tare da ku a don haka sai ku ci gaba da kasancewa da mu.

    Za ku iya zuwa shafukanmu na sada zumunta domin kallon bidiyo har ma ku tafka muhawara kan labaran da muka wallafa.