Kasashe 7 da suka fi ƙanƙanta a duniya

Liechtenstein

Asalin hoton, Liechtenstein

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 4

Akwai wasu ƙasashen duniya waɗanda saboda ƙanƙantar su, mutum zai iya zagaye su a cikin ƙanƙanin lokaci, hatta a cikin kwana ɗaya kacal. Ba kamar yadda wasu ke tsara tafiya ta tsawon watanni domin ziyartar sassan ƙasa ɗaya ba, al'amarin ya banbanta a irin waɗannan ƙananan ƙasashe.

Ga mutanen gabashin Afirika, abu ne mai wahala a gamsar da su cewa girman ƙasa ɗaya bai wuce kwatankwacin girman unguwa ko gunduma ɗaya ba. Amma a gaskiyar magana irin waɗannan gidaje ba su wuce girman ƙananan garuruwan Tanzania da Kenya da kuma Uganda ba.

Duk da rashin girman su, ƙasashen suna da ɗimbin tarihi da daɗaɗɗun al'adu, sannan kuma suna jan hankalin masu yawon shaƙatawa sosai. Rashin girman su bai hana su yin tasiri a kan ƙasashen duniya ba.

Ga jerin ƙananan ƙasashen duniya 7 da mutum zai iya kai masu ziyara baki ɗaya rana a cikin kwana ɗaya, ko ma a cikin sa'oi.

7. Malta

s

Asalin hoton, Getty Images

Malta tana da faɗin murabba'in kilomita 316. Ta ɗan zarce sauran ƙasashen da ke cikin wannan jeri, amma girman ta bai zarce a kewaye ta a cikin kwana ɗaya ba.

A gabashin Afirika ana iya kamanta fadin Malta da na birane irin su Arusha da sauran su.

Wannan na nufin mutum zai iya tashi daga wani sashi zuwa wani cikin ƙanƙanin lokaci a cikin mota kuma ana iya kai ziyara wuraren buɗe ido a cikin kwana ɗaya.

Malta na da tarihin gine-ginen da masu ɗimbin tarihi da birane masu kyau. Duk da cewa ba ta da girma, tana da wurare masu ƙayatarwa kuma duk za ka iya ziyartar dukkan wuraren a kwana ɗaya.

6. Liechtenstein

x

Asalin hoton, Getty Images

Liechtenstein tana da faɗin murabba'in kilomita 160. Ta yi iyaka da Switzerland da Austria kuma tana daga cikin ƙasashe marasa faɗin ƙasa amma masu ƙarfin tattalin arziki.

Ana iya kamanta ta da girman garin Thika da sauran ƙauyukan da ke kusa da shi a Kenya.

Za a iya zagaye ƙasar baki ɗaya a cikin ƙanƙanin lokaci a cikin mota.

Duk da ƙanƙantar ta, ƙasar tana da tsaunuka masu kyau da ƙayatattun ƙauyuka da kuma ƙarfin tattalin arziki. Ƙasa ce da mutum zai iya ziyarta a cikin kwana ɗaya kuma ya karaɗe duk wuraren yawon buɗe ido da take da su.

5. San Marino

s

Asalin hoton, Getty Images

San Marino na da faɗin murabba'in kilomita 61. Tana a nahiyar Turai ne kuma ɗaya daga cikin ƙasashe da suka fi tsufa a Najeriya.

Kusan faɗin su ɗaya da birnin Moshi, da ke Kilimanjaro a Tanzania.

Duk da cewa murabba'in kilomita 61 na da ɗan faɗi, mutum zai iuya karaɗe ƙasar a cikin kwana ɗaya kacal da mota, kuma cikin ƴan sa'oi.

Ƙasar tana da tsaunuka da gine-gine masu ɗimbin tarihi da ke jan hankalin masu yawon buɗe ido. Mutum zai iya kammala ziyarar wuraren tarihi da na buɗe idon ƙasar a cikin kwana ɗaya.

4. Tuvalu

s

Asalin hoton, Getty Images

Tuvalu na da faɗin murabba'in kilomita 26 kuma tana daga cikin ƙananan ƙasashe masu fuskantar ɗumamar yanayi.

Za a iya kwatanta faɗin ta da matsakaitan biranen gabashin Afirika irin su Kampala na Uganda.

Saboda rashin girmanta ana iya zagaye mafi yawan garuruwan ta a cikin ƙanƙanin lokaci.

Tuvalu na da ƙayatattun gaɓar teku da wuraren shaƙatawa masu ɗaukar hankali. Babu cunkoson ababen hawa, wani abu da ya banbanta ta da sauran manyan biranen gabashin Afirika.

3. Nauru

s

Asalin hoton, Getty Images

Nauru wani ƙaramin tsibiri a tekun Pacific mai faɗin murabba'in kilomita 21. Tana daga cikin ƙasashen duniya da ba a san su sosai ba, kuma mafi ƙanƙanta.

Kusan faɗin su ɗaya da tsibirin Chumbe.

Idan da mota ne, mutum zai iya zagaye ƙasar baki ɗayan ta a cikin ƙasa da sa'oi biyu.

Nauru bata da dogaye gine gine, amma tana da ƙayatattun gine-gine masu ban sha'awa da kuma yanayin ƙasa mai matuƙar kyau.

2. Monaco

s

Asalin hoton, Getty Images

Monaco na da faɗin murabba'in kilomita 2 kacal. Tana daga cikin ƙasashe masu arziki a duniya, kuma ta yi suna kan tsadar rayuwa da shaƙatawa da kuma tseren mota na Formula.

Monaco ta kai aƙalla rabin faɗin Kenya.

Abu ne mai sauƙi a tashi daga farko a kai ƙarshen ta cikin ƙanƙanin lokaci.

Duk da ƙanƙantar ta, Monaco na da yawan gine-ginen ƙawa da otel-otel da gaɓar teku masu kyau, kuma a cikin kwana ɗaya kacal za a iya zagaye ta.

1. Vatican City

s

Asalin hoton, Getty Images

Birnin Vatican ne ƙasa mafi ƙanƙanta a duniya kuma tana da faɗin murabba'in kilomita 0.49. Tana cikin birnin Rome na Italiya kuma a cikin ta hedikwatar cocin ɗarikar katolika na addinin kirista take.

An kwatantan faɗin ta da na Kariakoo a Dar es Salaam.

Ko a hankali mutum ke tafiya zai iya zagaye ƙasar baki ɗaya a cikin sa'a biyu.

Duk da rashin girman ta Vatican na da wuraren yawon shaƙatawa da na tarihi masu yawa da suka haɗa da St. Peter's Basilica da sauran su.

An rubuta wannan maƙala ne ta hanyar tattara bayanai daga majiyoyi da dama, ciki harda mentalfloss