Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Jana'izar Khamenei da abubuwan da ke faruwa a sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kai tsaye dangane da jana'izar Ayatollah Ali Kahamenei da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar 07/07/2026

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman MINJIBIR da Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ban taɓa haɗuwa da Adeyemi ba — Gbajabiamila

    Shugaban ma’aikatan fadar shugaban Najeriya, Femi Gbajabiamila, ya musanta cewa ya taɓa haɗuwa ko yin wata mu’amala da Adeniyi Adeyemi, wanda ya bayyana kansa a matsayin Darakta Janar na hukumar PFIPC.

    Adeyemi wanda gwamnatin tarayyar ƙasar ta ce ya naɗa kansa a matsayin shugaban majalisar bai wa shugaban shawara kan tattalin arziki da zuba jari daga ƙasashen ƙetare, ya zargi Gbajabiamila da yin barazana ga rayuwarsa bayan turka-turka ta ɓarke tsakaninsu.

    Sai dai Gbajabiamila ya ce ba shi da wata alaƙa ko mu’amala da Adeyemi a baya.

    A cikin wata wasiƙa da lauyansa, Kemi Pinheiro ya aika wa Adeyemi a madadinsa, Gbajabiamila ya buƙaci Adeyemi ya janye kalamansa tare da neman afuwarsa a gidajen jaridu biyar na ƙasar da kuma shafukan sada zumunta da aka yaɗa zarge-zargen.

    "Wanda mu ke wakilta [Gbajabiamila] ya shaida mana cewa, ba ka taɓa haɗuwa da shi ba, ba ka taɓa yin wata mu’amala, ko wata hulɗa ta sirri ko aiki da shi ba,” in ji Lauyan.

    A cikin wasiƙar, lauyoyin Gbajabiamila sun ce idan Adeyemi bai cika waɗannan buƙatu cikin sa’o’i 72 ba, za su ɗauki matakin shari’a a kansa, ciki har da shigar da ƙara kan zargin ɓata suna.

    Sun ce za su kuma nemi diyyar Naira biliyan 10, tare da umarnin kotu da zai tilasta masa bayar da haƙuri da kuma dakatar da sake yaɗa irin waɗannan zarge-zarge.

    Wannan rikici ya samo asali ne daga zarge-zargen da Adeyemi ya yi a wani taron manema labarai da ya gudanar a watan da ya gabata, inda ya yi ikirarin cewa Gbajabiamila na da hannu wajen tafiyar da harkokin PFIPC.

  2. An kai gawar Ali Khamenei birnin Najaf domin jana'izarsa a Iraƙi

    An kai gawar tsohon jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei, zuwa birnin Najaf da ke Iraƙi domin gudanar da jana'izarsa.

    Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya isa birnin Najaf domin halartar bikin jana'izar.

    Kamfanin dillancin labaran Iran ta IRNA ta ce bayan halartar taron, zai kuma gana da Firaministan Iraki.

    Za a fara gudanar da jana'izar Khamenei a birnin Najaf, daga bisani kuma a ci gaba da ita a birnin Karbala, waɗanda ke daga cikin muhimman wuraren addini na mabiya Shi'a.

    Kamfanin dillancin labaran Mehr ya rawaito cewa, baya ga Pezeshkian, babban ɗan marigayi Khamenei, Mostafa Khamenei, da shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Baqer Qalibaf, na cikin waɗanda za su halarci jana'izar a Iraki.

    Bayan kammala bukukuwan jana'izar a Iraki, ana sa ran za a binne Ali Khamenei ranar Alhamis a haramin Imam Reza da ke birnin Mashhad, garinsu na asali.

  3. An kama masu zanga-zanga a Kenya

    An kama mutane da dama a Nairobi, babban birnin Kenya, bayan sun tsallake shingen ’yan sanda domin shiga wata zanga-zangar da gwamnati ta haramta.

    Masu fafutukar kare dimokuradiyya ne suka shirya zanga-zangar domin tunawa da cikar shekara daga zanga-zangar neman sauyi ta shekarar 1990.

    ’Yan sanda sun ce zanga-zangar ba ta halatta ba, saboda masu shirya ta ba su sanar da hukumomi tun da wuri ba, kamar yadda doka ta tanada.

    An baza jami’an tsaro da dama a sassa daban-daban na Nairobi, tare da kafa shingayen bincike a manyan hanyoyin shiga birnin.

    A bara irin wannan zanga-zanga ta rikide zuwa tashin hankali, inda akalla mutum talatin da takwas suka rasa rayukansu

  4. Xi Jinping ya nemi a gudanar da ayyukan ceto bayanan matsanancin yanayi

    Shugaban ƙasar China , Xi Jinping, ya yi kira da a gudanar da ayyukan ceto cikin gaggawa da dukkan ƙarfi, bayan da matsanancin yanayi a sassa daban-daban na ƙasar ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 15 tare da raba dubban mutane da muhallansu.

    A lardin Hubei da ke tsakiyar ƙasar, munanan guguwa da ruwa sama sun afakawa birane da gundumomi da dama, inda suka kashe aƙalla mutum takwas.

    A lokaci guda kuma, mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa da guguwar Typhoon Maysak ta haddasa sun yi sanadin mutuwar aƙalla mutum biyu a yankin Guangxi da ke kudancin ƙasar.

    A lardin Gansu da ke yammacin kasar kuwa, an ba da rahoton cewa zaftarewar ƙasa a wani yanki mai tsaunuka ta binne fiye da mutum 30.

  5. Yadda aka tsara jana'izar Ayatollah Ali Khamenei

  6. An kama mahaifin Adeyemi Adeniyi: Me dokar Najeriya ta ce?

    Ƴan Najeriya na ci gaba da bayyana ra'ayoyinsu game da rahotonnin kamen da ake zargin jami'an tsaro sun yi wa mahaifi da dangin shugaban hukumar PFIPC da ake zargi ta bogi ce.

    A ranar Litinin ne bayanai suka ce ƴansanda sun kai samame gidan Prince Adeniyi Adeyemi da ke Ogbomoso na jihar Oyo tare da kama wasu daga cikin danginsa ciki har da mahaifinsa.

    A baya-bayan nan ne dai aka zargi Prince Adeniyi Adeyemi da kafa sabuwar hukumar gwamnati ta bogi, wadda kuma har ta samu kaso a kasafin kuɗin ƙasar na 2026.

    Bayanai sun ce an kama dangin nasa ne a lokacin da suka ziyarci gidan Adeyemi a ranar Litinin.

    Sai dai babu bayani dangane da ko jami'an tsaron sun kama dangin Prince Adeyemi bisa hannu a laifin da ake zargin ɗan uwan nasu da aikatawa.

    A cikin wannan muƙala mun duba abin da dokokin Najeriya suka tanada kan kama wani bisa laifin ɗan'uwansa.

  7. Trump ya isa Turkiyya domin halartar taron shugabannin NATO

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya isa birnin Ankara na ƙasar Turkiyya domin halartar taron ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO, inda Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya tarbe shi.

    Ana sa ran Trump zai gana da Erdogan kafin a fara liyafar shugabannin ƙasashen NATO da za a gudanar a daren Talata, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

    Babban taron shugabannin ƙasashen NATO kuma zai gudana ne a ranar Laraba.

    Rahotanni sun ce shugabannin ƙasashen ƙungiyar na fatan samun goyon bayan Trump, wanda a watannin baya ya riƙa sukar NATO da kuma yadda Amurka ke ɗaukar nauyin tsaron ƙungiyar.

    A don haka ne ma, ƙasashen suka yi alƙawarin ƙara yawan kuɗaɗen da suke warewa fannin tsaro.

    Taron na bana ya zo ne shekara guda bayan da mambobin NATO suka amince da ƙara yawan kuɗaɗen tsaro zuwa kaso biyar cikin ɗari na yawan kuɗin shiga na ƙasashensu sakamakon matsin lambar Trump.

    Kafin isowar Trump, ƙawayen NATO sun sanar da sabbin yarjejeniyoyin sayen makamai na biliyoyin daloli, tare da jaddada ƙudirin ƙara kasafin kuɗin tsaro, matakin da ake ganin na da nufin kwantar masa da hankali kan yadda Turai ke taka rawa wajen tsaron ƙungiyar.

  8. An kwashe ma'aikatan jirgin dakon gas na Qatar bayan kai masa hari a Mashigar Hormuz

    An kwashe ma'aikatan wani jirgin dakon iskar gas na ƙasar Qatar bayan da wani abu da ba a tantance ko menene ba ya harbi jirgin yayin da yake wucewa ta Mashigar Hormuz.

    Kamar yadda wasu majiyoyi uku suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters, jirgin ya aika da saƙon neman agajin gaggawa bayan abin ya harbi ɓangaren hagun sashen jirgin.

    Sun ƙara da cewa harin ya yi wa jirgin mummunar ɓarna, sai dai har yanzu ba a tabbatar da cikakken yanayin da yake ciki ba.

    Tun da farko, an ruwaito cewa wani jirgin dakon man fetur ma ya gamu da irin wannan hari yayin da yake ratsawa ta Mashigar Hormuz daga ɓangaren Oman.

    Har zuwa yanzu babu wata ƙungiya ko ƙasa da ta ɗauki alhakin harin.

  9. Za a kai gawar Ali Khamenei zuwa Najaf bayan kammala jana'iza birnin Qom

    Ana sa ran za a tafi da gawar marigayi Ayatollah Ali Khamenei zuwa birnin Najaf na ƙasar Iraki a yau, bayan kammala jana'izar da ake yi masa a birnin Qom na Iran.

    Kamfanin dillancin labarai na Mehr ya ruwaito cewa babban ɗan marigayin, Mustafa Khamenei, da Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da Kakakin Majalisar Dokokin ƙasar, Mohammad Baqer Qalibaf, za su halarci jana'izar da za a gudanar a Najaf.

    Rahotanni sun ce za a gudanar da bukukuwan jana'izar Khamenei a ranar Laraba a biranen Karbala da Najaf na Iraki.

    Bayan kammala jana'izar a Iraki, ana sa ran za a mayar da gawarsa Iran domin binne ta a ranar Alhamis a harabar Hubbaren Imam Reza da ke garinsu na haihuwa, Mashhad.

  10. Macron yana cikin ƙoshin lafiya bayan wata fashewa a Damascus

    Gwamnatin Faransa ta sanar da cewa Emmanuel Macron na cikin koshin lafiya, bayan rahotonnin AFP cewa an ji ƙarar fashewar wani abu a birnin Damascus a ranar Talata.

    Hotunan da aka fitar daga Damascus sun nuna hayaki mai ƙauri a kusa da otal ɗin da Emmanuel Macron ya sauka a lokacin ziyararsa zuwa Syria.

    Rahotanni daga Syria sun ce aƙalla mutum 18 sun jikkata sakamakon fashe-fashen da suka auku a tsakiyar Damascus.

    Wata majiyar tsaro ta shaida wa BBC cewa fashe-fashen sun samo asali ne daga bama-bamai biyu da aka ƙera da hannu kuma sun jikkata mutane da dama.

    Kafofin yaɗa labarai na Syria sun ruwaito cewa jami’an ‘yan sanda huɗu na cikin waɗanda suka jikkata a lamarin.

    A halin yanzu Mista Macron yana babban birnin Syria, inda yake tattaunawa da Shugaba Ahmed Sharaa a fadar shugaban ƙasa, a cewar wata sanarwa daga Fadar Elysee.

    Fadar Elysee ta kuma ce ziyarar “na ci gaba kamar yadda aka tsara.”

    Mista Macron shi ne shugaban wata ƙasa na farko daga ƙasar Tarayyar Turai da ya ziyarci Syria tun bayan da sabuwar gwamnati ta hau mulki.

  11. Za mu iya gamawa da Iran a ƙanƙanin lokaci amma na zaɓi mu tattauna - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce farashin mai bai tashi sosai ba duk da rufe mashigin ruwa na Hormuz, yana mai cewa: “Mun karɓi mai mai yawa daga gare su. Mutane ba su san haka ba, kuma duk wannan ya faru ne cikin wata ɗaya da rabi kacal.”

    A wata hira da ya yi ta talabijin, Shugaban Amurkan ya sake jaddada cewa ya lalata jiragen ruwan yakin Iran da kuma dukkan jiragen saman rundunar sojin saman Iran.

    “Daga ƙarshe sun fahimci cewa ba su da na’urorin hangen jirage na rada kuma, domin an lalata tsarin radarsu. Saboda haka muka kai musu hari cikin dare da kuma a cikin duhu.”

    “Rundunar ruwanmu mai ƙarfi ta ƙaƙaba mafi girman takunkumi da aka taɓa gani, inda suka yi wa tashoshin Iran ƙawanya kuma tsawon watanni biyu babu wani jirgin ruwa da ya iya ketare ƙawanyar. Daga baya muka kusan cimma yarjejeniya, sai muka sassauta ƙawanyar. Ban sani ba, wataƙila za mu iya cimma yarjejeniya.”

    Mista Trump ya nace cewa: “Za mu yi nasara ta kowace hanya ce. Ko dai mu cimma yarjejeniya, ko kuma mu kammala lamarin.”

    Ya ce kammala murƙushe Iran abu ne mai sauƙi: “Ba zai yi wahala mu gama da ita ba. Amma tabbas, na fi son a samu yarjejeniya, domin ba na son mutane miliyan 91 su fuskanci illa.”

    “Za mu iya rusa gadojinsu cikin sa’a guda. Za mu iya lalata cibiyar samar da wutar lantarkinsu. Dukkan waɗancan tashoshin wutar lantarki da suka gina manyan, kyawawa kuma na zamani. Suna da kuɗi da yawa a baya, amma yanzu ba su da kuɗi. Ba mu ba su ko sisin kwabo ba, amma za mu iya katse musu wutar lantarki da kuma lalata tashoshin samar da wutar nasu.”

    A kwanaki kaɗan da suka gabata, Mista Trump ya ce ya bai wa Iran mako guda domin ta binne tsohon shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

  12. An nemi Iraniyawa su shigar da ƙorafi kan raɗaɗin rashin Khamenei

    Ministan Shari'a na Iran: Mutane na iya shigar da ƙara saboda "raɗaɗin tunani da na zuciya da rashin jagora ya haifar."

    Ministan Shari'a na Iran, Amin Hossein Rahimi, ya bayyana cewa Ma'aikatar Shari'a da gwamnati sun samar da dukkanin hanyoyin da suka dace domin mutane su shigar da ƙorafe-ƙorafe da ƙara dangane da "lahanin tunani da na ƙwaƙwalwa da rasuwar jagoran ƙasar ta haifar musu".

    Ya ce ana iya yin hakan ta hannun lauyoyi ba tare da biyan kuɗi ba, a gaban hukumomin cikin gida da na ƙasa da ƙasa.

    "Ana ci gaba da bibiyar laifukan da maƙiya suka aikata a ƙungiyoyi da kotunan ƙasa da ƙasa da kuma hukumomin cikin gida, kuma an tattara hujjoji masu ƙarfi kan lamarin."

    Ya ƙara da cewa:

    "Bisa doka, hukumomin shari'a na Jamhuriyar Musulunci ta Iran suna da ikon binciken waɗannan laifuka, kuma akwai yiwuwar gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata su, ciki har da gwamnatin Amurka da kuma gwamnatin Isra'ila."

    Ministan ya kuma bayyana akwatin gawar jikar Ali Khamenei a matsayin "shaidar irin zaluncin da aka yi wa jagoran Iran", inda ya kwatanta lamarin da Ali Asghar, ɗan Imam Husaini bn Ali, Imam na uku a wajen mabiya Shi'a.

    A ƙarshe, Rahimi ya jaddada cewa "Wannan wata fafatawa ce ta shari'a da za ta gudana tare da sauran fannoni na tinkarar waɗanda suka aikata wannan hari."

  13. An gabatar da hujjoji a gaba kotu kan Charlie Kirk

    Masu gabatar da ƙara a jihar Utah ta Amurka sun gabatar da hujjoji a gaban wata kotu gabanin shariar da za a yiwa mutumin da ake zargi da kashe fitaccen mai ra'ayin rikau din nan , Charlie Kirk.

    Suna ƙoƙarin gamsar da alƙali cewa suna da shaidar da za su iya amfani da ita wajan gurfanar da wanda ake zargin, Tyler Robinson, a gaban kotu domin fara shari'a.

    Har yanzu Robinson bai bayyana ko ya amsa ko ya musanta zargin da ake yi masa ba.

    Mista Kirk, wanda ke da kusanci da Shugaba Trump, ya mutu ne bayan an harbe shi yayin da yake jawabi ga ɗalibai a harabar wata jami'a a watan Satumban bara.

  14. An fara gudanar da jana'izar Khamenei a birnin Qom.

    Bayan kammala jana'izar a hukumance da aka yi wa tsohon jagoran Jamhuriyar Musulunci a Tehran, tare da kai akwatin gawarsa da kuma na wasu daga cikin 'yan iyalansa da aka kashe tare zuwa birnin Qom, an fara gudanar da jana'izarsa a hukumance a wannan birni da ke lardin tsakiyar ƙasar.

    Kamar yadda aka ruwaito, Ayatullah Javadi Amoli ne ya jagoranci sallar jana'izar a Masallacin Jamkaran da ke Qom, sannan aka fara gudanar da jana'izar a gaban dubban magoya bayan marigayi Ali Kahamenei

    Bayan wannan taro, za a gudanar da wani makamancin taron jana'izar a birnin Najaf bayan an kai gawarwakin zuwa Iraki.

    Daga bisani kuma, za a kammala jerin jana'izar a birnin Mashhad ranar Alhamis.

  15. BBC ta gano yadda Rasha ke tsare da dubban fararen hula ƴan Ukraine

    Wani binciken da BBC ta gudanar ya samu shaidu da suka nuna cewa Rasha na tsare dubban fararen hula 'yan Ukraine a cibiyoyin tsare mutabe , inda ake zargin ana yi wa wasu azabtarwa da cin zarafin ta hanyar fyade.

    An kiyasta cewa fararen hula 'yan Ukraine kusan 16,000 ne aka tsare ko kuma suka bace tun daga shekarar 2014.

    Wata mata da aka saki a wani shirin musayar fursunoni ta shaida wa BBC cewa an yi mata fyade , sannan an tilasta mata cin ɗanyen abinci da aka gauraya da ƙasa da shara.

    Ta ce a cikin tsawon shekaru da kwana goma sha uku na rayuwarta ruhi na da jikina sun kasance cikin matsananciyyar nakasa.

    Ofishin Jakadancin Rasha da ke London ya ce Rasha ta dade tana nuna goyon bayan mutunta dokokin yaki , kuma hukumomin ƙasar na bincike kan duk wani zargi da ya shafi aikata laifukan yaƙi."

  16. Shugabannin NATO na taro a Turkiyya kan yaƙin Ukraine da Russia

    Shugabannin ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO na taruwa a Turkiyya domin halartar wani taron koli.

    Gabanin taron, Babban Sakataren kungiyar ta NATO ya bukaci mambobin ƙungiyar su ci gaba da bai wa Ukraine goyon baya, yayin da Rasha ta ƙara kai hare-hare da makamai masu linzami.

    Wakilin BBC ya ce jamian kungiyar ta Nato sun nuna damuwa akan Rasha da Ukraine da kuma matakan da turai za ta dauka domin ta kare kanta.

    Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya yi gargaɗin cewa ƙasarsa na fuskantar ƙarancin makaman kariya da ake amfani da su wajen kakkabo makamai masu linzami.

  17. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barkan ku da safiyar ranar Talata a watan Yulin 2026. Da fatan kun wayi gari lafiya. Allah ya sa hakan.

    Yau ma kamar kullum mun dawo da shafinmu na kai tsaye inda muka kawo muku bayanai dangane da al'amuran da ke faruwa a jana'izar jagoran addinin Musulunci na Iran, Ayatollah Ali Kahamenei da sauran muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.