Kotu za ta yanke hukunci kan makomar Jonathan ta yin takara a 2027

Asalin hoton, @GEJonathan/X
Yau ake sa rai babbar kotun tarayya a Najeriya za ta yanke hukunci kan ko tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan zai iya yin takara a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Wani ɗan Najeriya, Johnmary Jideobi ne ya shigar da ƙarar a kotu inda yake neman kotu ta dakatar da tsohon shugaban ƙasar daga komawa kan kujerar shugabancin ƙasar.
Wanda ya shigar da ƙarar ya ce ya shigar da ƙarar ce saboda a halin da ake ciki Jonathan ya karɓi rantsuwar kama aiki sau biyu kafin wa'adin shugabancinsa ya ƙare a 2015.
Yana neman kotu ta yi ƙarin haske kan sashe na 1 da 137(3) na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasa na 1999 kan cancantar tsayawa takarar shugaban ƙasa da kuma shekarun da aka ƙayyade na wa'adin mulkin.
Ƙarar kuma na neman a hana hukumar zaɓe ta Najeriya, INEC karɓa ko wallafa sunan Jonathan cikin jerin sunayen ƴan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027.
An shigar da ƙarar ce yayin da wani tsagi na Jam'iyyar PDP ke ƙoƙarin ganin Jonathan ya shiga takarar bayan rahotanni da ke cewa sun amince ya tsaya takara ba tare da hamayya ba.








