Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Fitattun ƴan Najeriya da suka kafa jam'iyyar PDP a 1998
- Marubuci, Usman MINJIBIR
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
A yanzu za a iya cewa babu wata jam'iyya a Najeriya da ta kai jam'iyyar hamayya ta PDP tsawon rai kasancewar ba ta taɓa narkewa zuwa wata jam'iyya ta daban ba.
A shekarar 1998 ne dai aka kafa jam'iyyar ta PDP a birnin Jos na jihar Plateau inda kuma ta shugabancin Najeriya a 1999 har zuwa 2015 lokacin da jam'iyyar APC ta haɗaka ta ƙwace mulki daga hannun PDP.
An kafa jam'iyyar PDP da ake kira da turanci People's Democratic Party a watan Agustan shekarar 1998, a ƙarshen mulkin soja bayan mutuwar Janar Sani Abacha.
Jam'iyyar ta samo asali ne daga haɗakar manyan 'yan siyasa da masu fafutukar dimokuraɗiyya, musamman mambobin ƙungiyoyin G-9 da G-18 da G-34 waɗanda suka yi adawa da yunkurin Abacha na ci gaba da mulki.
BBC ta yi nazari dangane da ƴan Najeriya da suka taka rawa wajen kafa jam'iyyar ta PDP.
Dr. Alex Ekwueme, 1932 - 2017
Dr. Alexander Ifeanyichukwu Ekwueme fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne wanda ya kasance Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko a Jamhuriya ta Biyu a ƙarƙashin Shugaba Shehu Shagari daga 1979 zuwa 1983.
Haka kuma, ana kallon sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin gwagwarmayar dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Najeriya.
Bayan mulkin soja na Janar Sani Abacha, Ekwueme ya jagoranci ƙungiyar G-34, wadda ta yi fito-na-fito da yunƙurin Abacha na ci gaba da mulki.
Wannan ƙungiya ce ta zama ɗaya daga cikin manyan ginshiƙan da suka haifar da kafuwar jam'iyyar PDP a 1998.
Dr. Alex Ekwueme ya rasu a ranar 19 ga Nuwamba, 2017, yana da shekara 85 a duniya.
Cif Solomon Lar, 1933 - 2013
Chif Solomon Daushep Lar fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Plateau, kuma ana ɗaukar sa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jagororin da suka kafa Jam'iyyar PDP a shekarar 1998.
Ya kuma kasance shugaban PDP na ƙasa na farko bayan kafuwarta a 1998.
A matsayinsa na shugaban PDP na farko, ya jagoranci gina tsarin jam'iyyar a faɗin Najeriya, tare da tabbatar da cewa ta samu wakilci daga dukkan yankunan ƙasar.
Wannan ne ya taimaka wa PDP zama jam'iyyar da ta lashe zaɓen shugaban ƙasa na 1999.
Solomon Lar ya kasance gwamnan farko na tsohuwar jihar Plateau daga 1979 zuwa 1983 a lokacin Jamhuriya ta Biyu.
Chif Solomon Lar ya rasu a ranar 9 ga Oktoba, 2013, ya na da shekaru 80. Ana tunawa da shi a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan PDP kuma dattijo mai tasiri a siyasar Najeriya
Prof. Jerry Gana
Farfesa Jerry Gana fitaccen masanin kimiyyar sinadarai ne, ɗan siyasa, kuma jigo a fafutukar dimokuraɗiyya a Najeriya.
Ana masa kallon ɗaya daga cikin mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafa Jam'iyyar PDP a shekarar 1998.
Lokacin da Najeriya ke shirin komawa mulkin dimokuraɗiyya a 1998, Jerry Gana ya shiga cikin jerin manyan jagororin siyasa da suka haɗa kai wajen kafa PDP.
Ya kasance cikin masu tsara manufofi da tsarin jam'iyyar, sannan ya zama Sakataren PDP na farko na ƙasa.
Jerry Gana ya yi aiki a gwamnatoci daban-daban, ciki har da gwamnatin soja da ta farar hula.
Ya kasance Ministan Yaɗa Labarai a lokuta daban-daban, inda ya zama ɗaya daga cikin fitattun masu magana da yawun gwamnati.
Farfesa ne a fannin kimiyyar sinadarai (Chemistry), kuma ya yi aiki a fannin koyarwa da bincike kafin shiga siyasa.
An haifi Jerry Ubong Gana a ranar 1 ga Janairu, 1948 a jihar Neja
Mallam Adamu Ciroma, 1934 - 2018
Mallam Adamu Atta Ciroma fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne, ɗan jarida, masanin tattalin arziki kuma jami'in gwamnati wanda ya riƙe manyan muƙamai a Najeriya tsawon shekaru da dama.
Ana kuma kallon a matsayin ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka taimaka wajen kafa Jam'iyyar PDP a 1998.
Adamu Ciroma na cikin fitattun mambobin G-34, ƙungiyar 'yan siyasa da dattawan ƙasa da suka yi adawa da yunkurin Janar Sani Abacha na ci gaba da mulki.
Saboda gogewarsa a fannin tattalin arziki da gwamnati, Adamu Ciroma ya taimaka wajen tsara manufofi da gina tubalan jam'iyyar a shekarun farko na kafuwarta.
Mallam Ciroma ya riƙe manyan muƙamai da dama, ciki har da:
- Gwamnan Babban Bankin Najeriya daga 1977 zuwa 1979.
- Ministan Kuɗi a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo
- Har ila yau ya riƙe wasu manyan mukamai a gwamnatocin soja da na farar hula.
Mallam Adamu Ciroma ya rasu a ranar 5 ga Yuli, 2018, yana da shekaru 83 a duniya.
Chief Tony Anenih, 1933 – 2018
Chif Anthony Akhakon Anenih fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Edo, wanda ya kasance ɗaya daga cikin manyan jiga-jigan da suka kafa Jam'iyyar PDP a shekarar 1998.
An fi sanin sa da laƘabin "Mr. Fix It" saboda ƙwarewarsa wajen sasanta rikice-rikicen siyasa da tsara dabarun jam'iyya.
Daga cikin manyan muƙaman da ya riƙe akwai:
- Shugaban Kwamitin Amintattu na PDP.
- Ministan Ayyuka a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo.
- Babban mai ba da shawara ga shugabannin PDP a shekarun farko na Jamhuriya ta Huɗu.
Chief Tony Anenih ya rasu a ranar 28 ga Oktoba, 2018, yana da shekaru 85 a duniya
Alhaji Abubakar Rimi, 1940 - 2010
Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Kano, kuma ɗaya daga cikin shahararrun 'yan siyasar Arewa a Jamhuriya ta Biyu.
Ya yi suna saboda ra'ayoyinsa na kawo sauyi da kuma siyasar domin ƴanta talakawa. Haka kuma yana cikin mutanen da suka taka rawa wajen kafa Jam'iyyar PDP, a ƙrshen mulkin soja.
A zaɓen 1979, Rimi ya zama gwamnan jihar Kano a ƙarƙashin jam'iyyar PRP. A lokacin mulkinsa daga 1979 zuwa 1983, ya aiwatar da manufofin da suka mayar da hankali kan ilimi, walwalar jama'a da kuma ƙarfafa masu ƙaramin ƙarfi a tsakanin al'umma.
Baya ga gwamna, Rimi ya riƙe muƙamin Ministan Sadarwa a shekarun 1990s. Ya kuma kasance ɗaya daga cikin fitattun masu ruwa da tsaki a siyasar ƙasa tsawon shekaru da dama.
Alhaji Abubakar Rimi ya rasu a ranar 4 ga Afrilu, 2010, yana da shekaru 69. Rasuwarsa ta kasance babban rashi ga siyasar Najeriya, musamman a Arewa
Alhaji Sule Lamido
Alhaji Sule Lamido fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Jigawa, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigan da suka kafa Jam'iyyar PDP a 1998, bayan kasancewa cikin fitattun masu fafutukar dimokuraɗiyya waɗanda suka yi adawa da mulkin soja tare da taka rawa wajen dawo da mulkin farar hula a Najeriya.
Sule Lamido ya shiga ƙungiyoyi da tarukan siyasa da suka nemi a dawo da mulkin dimokuraɗiyya bayan soke zaɓen shugaban ƙasa na 12 ga Yunin 1993.
Daga cikin manyan muƙaman da ya riƙe akwai:
- Ministan Harkokin Waje na Najeriya a gwamnatin Shugaba Olusegun Obasanjo daga 1999 zuwa 2003.
- Gwamnan Jihar Jigawa daga 2007 zuwa 2015 a ƙarƙashin jam'iyyar PDP
Senata Iyorchia Ayu
Senata Dakta Iyorchia Ayu fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Benue, kuma yana cikin mutanen da suka taka rawa wajen kafa Jam'iyyar PDP a shekarar 1998.
Ya kasance ɗaya daga cikin jagororin siyasa da suka taimaka wajen haɗa ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun 'yan siyasa daban-daban domin kafa jam'iyyar.
A lokacin Jamhuriya ta Uku, ya kasance ɗan majalisar dattawa, inda ya wakilci jihar Benue.
Daga baya ya zama Shugaban Majalisar Dattawa a shekarar 1992, kodayake ya yi ɗan gajeren lokaci a wannan muƙami.
Daga baya, Ayu ya ci gaba da kasancewa jigo a cikin PDP, har ma ya zama Shugaban Jam'iyyar PDP na Ƙasa a shekarar 2021.
Chief Bola Ige, 1930 - 2001
Chief James Ajibola Idowu Adegoke Ige, wanda aka fi sani da Bola Ige (1930–2001), fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga jihar Osun.
Ya kasance ɗaya daga cikin manyan jagororin siyasar Yarabawa kuma ƙwararren lauya wanda ya taka muhimmiyar rawa a siyasar Najeriya tun daga Jamhuriya ta Farko har zuwa Jamhuriya ta Huɗu.
Bola Ige bai kasance cikakken ɗan PDP na tsawon lokaci ba. Sai dai yana cikin manyan 'yan siyasar da suka shiga tattaunawa da shawarwarin da suka taimaka wajen samar da yanayin komawar Najeriya zuwa dimokuraɗiyya a shekarar 1998.
Daga baya ya shiga Alliance for Democracy (AD), wadda ta zama babbar jam'iyyar Yarabawa a lokacin.
Bola Ige ya kasance Gwamnan tsohuwar jihar Oyo daga 1979 zuwa 1983 a lokacin Jamhuriya ta Biyu.
Bayan dawowar mulkin farar hula a 1999, Shugaba Olusegun Obasanjo ya naɗa shi Ministan Wutar Lantarki da Karafa, daga baya kuma ya zama Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari'a.
An kashe Bola Ige a gidansa da ke Ibadan a ranar 23 ga Disamba, 2001, yayin da yake ministan shari'a na tarayya.
Senator Francis Ellah, 1927 - 2008
Sanata Francis John Ellah fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne daga Omoku a jihar Rivers. Ya kasance ma'aikacin gwamnati, ɗan kasuwa, marubuci kuma ɗan majalisar dattawa a Jamhuriya ta Biyu.
Ana kuma danganta shi da ƙoƙarin kafa PDP a shekarar 1998, inda ya kasance ɗaya daga cikin dattawan siyasar da suka shiga jam'iyyar tun farkonta.
A lokacin komawar Najeriya zuwa mulkin dimokuraɗiyya a 1998, Francis Ellah ya shiga PDP kuma har ma ya kasance cikin masu neman tikitin shugaban ƙasa na jam'iyyar a shekarar 1998
Sanata Farncis Ellah ya rasu a shekarar 2008 yana mai shekara 81.
Sauran fitattun ƴan Najeriya da suka kafa PDP
- Cif Olusegun Obasanjo - Tsohon shugaban Najeriya na soja da farar hula
- Cif Barnabas Gamade - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP
- Cif Audu Ogbeh - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP
- Alhaji Bamanga Tukur - Tsohon shugaban jam'iyyar PDP