Haaland na jan hankalin ƙungiyoyin Turai, Barcelona na sanya ido kan Estevao

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Ɗan wasan gaban Norway, Erling Haaland, mai shekara 26, yana jan hankalin ƙungiyoyin Arsenal da Real Madrid yayin da ake cikin yanayin rashin tabbas a kan makomar Manchester City. (Football Insider)

Ɗan wasan gefe na Brazil, Estevao Willian, ya fara nuna ɓacin ransa bisa rashin samun damar buga wasa a Chelsea, yayin da Barcelona ke sa ido kan halin da matashin mai shekara 19 ke ciki. (Sport)

Ɗan wasan gaba na Al-Nassr da Portugal, Joao Felix, na da sha'awar komawa buga ƙwallon ƙafa a Turai, amma ɗan wasan mai shekara 26 bai bayyana sunan ƙungiyar da yake son komawa ba. (AS)

Newcastle United na sa ido kan ɗan wasan baya na Rennes da ƙasar Morocco, Abdelhamid Ait Boudlal, mai shekaru 20, amma tana fuskantar gasa daga Everton da Brentford da Hull City.

Arsenal da Tottenham na sa ido kan ɗan wasan tsakiya na Bayer Leverkusen kuma ɗan ƙasar Algeria, Ibrahim Maza, mai shekara 20. (Teamtalk)

Chelsea na sa ido kan ɗan wasan baya na gefen hagu na Crystal Palace kuma ɗan ƙasar Ingila, Tyrick Mitchell, mai shekara 27, amma za ta iya fuskantar gasa daga Manchester United da Liverpool. (Teamtalk)

Leeds United ba ta da niyyar sayar da ɗan wasan baya na Wales, Ethan Ampadu, mai shekara 26, duk da rade-radin da ke alaƙanta shi da tsohuwar ƙungiyarsa ta Chelsea. (Football Insider)