Yadda tikitin wasan ƙarshe na gasar cin Kofin Duniya na dala 11,000 ke jan hankali

Asalin hoton, Getty Images
Lokacin da aka buɗe shafin sayar da tikitin zuwa kallon gasar Cin Kofin Duniya, mutane da dama sun ga ana sayar da tikitin kallon wasan karshe kan dala 10,990.
Ana kyautata zaton cewa shi ne tikitin kallon kwallon kafa mafi tsada.
A lokacin da aka bai wa Amurka da Canada da kuma Mexico damar karɓar bakuncin gasar, sun ce tikitin kallon wasan karshe ba zai haura dala 1,550 ba.
Lokacin da aka fara sayar da tikiti ga magoya bayan tawagogin waɗannan ƙasashe a watan Dismaba, tikitin da ya fi tsada shi ne wanda kuɗinsa ya kai dala 8,680.
Farashi ya sake yin sama a ranar Laraba lokacin da aka fara sayar da tikitin kallon wasan karshe.
An sayar da tikitin wasan karshe na gasar Kofin Duniya a Qatar a 2022 kan dala 1,604.
Abu ne mai wuya a gano abin da ya janyo tikitin ya yi tsadar gaske saboda Fifa ba ta taɓa fitar da yadda take tsara farashin tikiti ba.
A ƙarshen shekarar da ta gabata an kwatanta farashin tikiti da aka fitar a matsayin "cin amana mai girma". A watan Disamba, Fifa ta sanar da wasu tikiti da ake sayar wa kan dala 60.
Abin da aka lura da farashin tikitin wasan karshe
Yana da matukar wahala a iya gane yadda tsarin saka farashin tikitin yake saboda babu bayanai da suka kamata.
Yin duba kan shafin sayar da tikiti na Fifa da kuma ganin abubuwan da suka rage da kuma abin da ake caza yana nuna abu mai kyau. Sai dai, hakan ba yana nufin cewa akwai tikiti masu tsada ba, ko kuma idan akwai masu rahusa waɗanda za a iya saya.
Daga abin da aka lura, tikitin wasan karshe na gasar Kofin Duniya ya ƙaru da kashi 38 lokacin da aka fara sayar da shi, ba kamar lokacin da aka fitar da shi a watan Disamba ba.
Ba ya ga tikitin mataki na farko da ake sayarwa kan dala 10,990:
- Tikitin mataki na biyu kuma ya ƙaru da kashi 32.78 daga dala 5,575 zuwa dala 7,380.
- Tikitin mataki na uku kuma ya ƙaru da kashi 38.23 daga dala 4,185 zuwa dala 5,785.
Har ila yau, Fifa ba ta ba da sanarwa kan wasanni ba, ko kuma a farashi nawa za a sayar da su "lokacin da aka buɗe" sayar da tikiti.
Waɗanda suka ziyarci shafin sun lura da cewa an fi neman sayan tikitin manyan wasanni - ciki har da na manyan tawagogi da kuma na wasannin zagaye.
Sake buɗe sayar da tikiti da tsauwala farashi
Fifa ta sake bude shafin sayar da tikiti ranar Alhamis, kuma kamar yadda aka yi tsammani an samu karin farashi a tikitin wasannin da za a yi a Amurka da Canada.
Dokokin Mexico sun hana sake sayar da tikiti fiye da ƙima.
Duk wanda ya sayi tikiti zai iya sayar da shi kan farashi da yake so.
BBC ta yi duba kan sayar da tikitin jim kaɗan bayan sake buɗe shafin sayar da shi, kuma an gano cewa farashin tikitin da ya fi tsada shi ne na wasan karshe wanda ya kai dala 82,780, inda mai karamin kuɗi ya kasance kan dala 27,000.
Farashin tikitin wasan Ingila na farko da Croatia, wanda yake kan dala 60, ya kai dala 1,499 a shafin.
Fifa na cazar dukkan masu saya da sayarwa da kashi 15.
Farfesa Mark James, a jami'ar Manchester, ya ce ya kamata da Fifa ta saka farashin daidai da yadda dokar New York ta bayyana.
"Dokar jihar ta ce babu batun sake sayar da tikiti ba tare da izini ba," in ji James.
'Wani taɓo ga tsarin sayar da tikiti na Fifa'
Yadda Fifa ta gudanar da tsarin sayar da tikitin ya haifar da rudani da cece-kuce.
Rashin tsari kan farashi da ƙarancin bayanai, sun janyo wahala ga magoya baya wajen shirya wa gasar ta kofin duniya.
"Da alama babban sirri ne," in ji Thomas Concannon, wanda ke jagorantar magoya bayan tawagar Ingila, kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Magoya baya ba su san inda suka dafa ba."
Lamarin bai sauya ba ranar Laraba, inda babu wani bayanai da magoya baya suka samu kan batun farashin tikiti.
"Wani taɓo ne kan tsarin sayar da tikiti na Fifa," in ji Concannon. "Ba sabon abu bane ga ɗaukacin gasar."
"Wani lokaci a rayuwa, sau ɗaya kaɗai kake samu damar zuwa gasar Kofin Duniya," in ji shi.
"Ga mutane da yawa, wannan ita ce damar su ɗaya tilo kuma ba za su samu damar zuwa ba."










