Me zai faru da Manchester City idan Guardiola ya tafi?

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na shirin ban-kwana da mai horas da ƴan wasanta Pep Guardiola da zarar ta kammala wasanninta na wannan kaka, inda a ƙarshe za ta kara daAston Villa a ranar Lahadi.
Majiyoyi sun shaida wa BBC Sport cewa ana sa ran fitaccen kocin zai bar filin wasa na Etihad Stadium a karshen kakar wasan bana.
City na cewa har yanzu kwantaragin Guardiola za ta kai kakar wasa mai zuwa, kuma tana fatan zai ci gaba da zama koci har zuwa karshen kakar baɗi. Sai dai kuma ana ci gaba da shirye-shiryen yiwuwar tafiyarsa da zarar aka kare kakar nan, inda ma'aikatan ƙungiyar da dama suka fahimci cewa zai tafi.
An kuma fahimci cewa wasu daga cikin ƴan wasan City suna tsammanin Guardiola zai ajiye aikin da zarar an kammala wasa da Aston Villa, yayin da ƙungiyar za ta yi tunanin gagarumin ban kwana da kociyan da ya ɗora kungiyar kan turba.
Ɗaya daga cikin hanyoyin da ake tunanin za a martaba ɗan kasar Sifaniya shi ne sanya sunan Guardiola ga sabon bangaren wajen kallo daga Arewacin Etihad, wato North Stand a filin Etihad da aka fadada.
Tsohon kocin Chelsea, Enzo Maresca, wanda ya taɓa aiki karkashin Guardiola a City, shi ne kan gaba da ake cewa zai maye gurbin Guardiola.
Guardiola ya jagoranci City zuwa lashe manyan kofuna 17 — gaba daya 20 jimilla — ciki har da kofin Premier League shida da na Champions League daya da FA Cup uku da kuma EFL Cup biyar cikin shekaru 10 da ya shafe a kungiyar.
Ana kallon shi a matsayin mafi girman koci a tarihin ƙungiyar kuma ɗaya daga cikin mafi kwarewa a tarihin kwallon kafa. Har yanzu yana da damar ci gaba da zamansa a Etihad da lashe kofin lig na bakwai, bayan da ya riga ya ɗauki FA Cup da Carabao Cup a wannan kakar.
An dade ana rade-radin makomar Guardiola, inda aka ta yi masa tambayoyi game da ci gaba da zamansa a City a duk lokacin da zai gana da ƴan jaridu.
Zamanin da ya karya tarihi a ƙungiyar
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Pep Guardiola ya sanya hannu a karon farko kan kwantiragin shekara uku da Manchester City a watan Fabrairun 2016 domin maye gurbin Manuel Pellegrini daga farkon kakar 2016–17.
Ko da yake ya kammala wannan kakar ba tare da lashe kofi ba karo na farko a rayuwarsa ta horaswa — sannan kuma ya sake ƙare wata kakar babu kofi a bara — ƙungiyar City ta mamaye ƙwallon kafar Ingila a mafi yawan lokutan mulkinsa.
City ce kaɗai ƙungiyar da ta taɓa haɗa maki 100 a kakar Premier League, abin da ta yi a kakar 2017–18. A wannan kakar kuma ta kafa tarihin mafi yawan cin ƙwallaye a kakar wasa ɗaya, inda ta zura Kwallo 106 a raga.
A kakar 2022–23, City ta zama ƙungiya ta biyu kacal a tarihin Ingila bayan Manchester United a 1998–99 da ta lashe kofi uku rigis "Treble" — wato ɗaukar Premier League da FA Cup da kuma UEFA Champions League a kakar wasa guda.
Daga baya kuma ƙungiyar da Guardiola ke jan ragama ta zama ta farko da ta lashe kofin lig na Ingila sau hudu a jere bayan nasarar kakar 2023–24.
Tsohon dan wasan tawagar Sifaniya ya sake sanya hannu kan karin kwantiragin shekara biyu a watan Nuwamban 2024, wanda zai kai shi zuwa karshen kakar 2026–27.
Rayuwa mai cike da lashe kofuna

Asalin hoton, Getty Images
Pep Guardiola ya koma Manchester City ne bayan ya shafe shekara uku yana horar da Bayern Munich, inda ya lashe kofunan Bundesliga uku a jere da kuma na Jamus biyu.
Ya fara aikin horaswa a Barcelona a shekarar 2008, inda ya gina ɗaya daga cikin mafi kyawun ƙungiyar ƙwallon kafa. A lokacinsa, ya lashe kofin La Liga uku a jere da UEFA Champions League biyu da Copa del Rey biyu kafin ya ɗauki hutun shekara guda bayan kakar 2011–12.
A matsayinsa na tsohon ɗan wasan, Guardiola ya shafe mafi yawan rayuwarsa ta tamaula a Barcelona, inda ya lashe kofin La Liga shida da Copa del Rey biyu da kuma European Cup a 1991–92.
Ya kuma jagoranci tawagar Sifaniya zuwa lashe lambar zinare a 1992 Summer Olympics, sannan daga baya ya buga wa babbar tawagar kasar wasa 47. Ya yi ritaya daga taka leda a matkin ƙwararre a shekarar 2006.
Shin wannan ne jerin rabuwa da manyan ƴan wasa da kociyan Manchester City FC?

Asalin hoton, Getty Images
Idan aka tabbatar da cewa Pep Guardiola zai bar Etihad a karshen kakar nan, zai bi sahun wasu daga cikin manyan ƴan wasan da ya ɗauko a zamaninsa a Manchester City da suma za su bar ƙungiyar da zarar an kare kakar bana.
Kyaftin ɗin ƙungiyar kuma ɗan wasan tawagar Portugal, Bernardo Silva, tare da mai tsaron bayan Ingila, John Stones sun sanar cewar wannan ce kakarsu ta karshe a Manchester City, saboda kwantiraginsu zai kare a wannan bazarar.
Ɗan wasan tawagar Belgium, Kevin De Bruyne, wanda yanzu ke taka leda a Napoli, ya bar Etihad Stadium bayan karewar yarjejeniyarsa a bara. Haka kuma mai tsaron ragar Brazil, Ederson an sayar da shi zuwa Fenerbahce a watan Satumba.
Tsohon mai tsaron bayan Ingila, Kyle Walker, ya koma Burnley a watan Yuli bayan da ya shafe rabin kakar bara aro a AC Milan.
Sai dai duk da rasa waɗan nan fitattun ƴan wasan, City har yanzu na fama da tuhume-tuhume 115 da ake yi mata kan zargin karya dokokin kudi na Premier League.
Shin akwai alamun yiwuwar Guardiola zai bar Etihad?

Asalin hoton, Getty Images
Shin wannan ce kakar ƙarshen Pep Guardiola a Manchester City? Alamomi sun nuna yiwuwar tafiyarsa a cikin makon da ya gabata.
A ranar Juma'a, an tambayi Guardiola ko ziyarar da suka kai Wembley Stadium washegari za ta kasance ta ƙarshe a gare shi. Sai ya amsa da cewa "ko kaɗan", domin har yanzu yana da "shekara guda a ragowar kwantiraginsa".
Sai dai yadda ya faɗi maganar cikin raha da kuma yadda ya fice daga ɗakin taron cikin sauri ya sa mutane da dama suka fara ƙara zargin cewa watakila yana dab da barin Etihad.
City ta lashe FA Cup karo na uku a ƙarƙashin Guardiola bayan doke Chelsea ranar Asabar. Wata alama mai muhimmanci ita ce, Guardiola ya ɗauki hoto da kofin tare da kowane ma'aikacin ƙungiyar ɗaya bayan ɗaya.
Kyamarori sun kuma nuna shi yana kallo daga nesa da tunani, yayin murnar lashe kofin a filin Wembley — ko yana neman wani daga cikin iyalansa a cikin masu kallo ne, ko kuma yana jin daɗin lokutansa na ƙarshe a wannan babban filin wasa na ƙasa?
Har yanzu City ba ta fitar da wata sanarwa kan sabbin abubuwan da ke faruwa ba, kuma ƙungiyar za ta je wasan Premier League a Bournemouth ranar Talata, inda babu shakka za a sake tambayar Guardiola game da makomarsa.
Tambayar ita ce: zai bayar da cikakkiyar amsa ko kuma zai ci gaba da jaddada maganarsa a baya cewar yana da saura "shekara guda" kamar yadda yake ta faɗa a tsawon wannan kakar?
Guardiola ya jagoranci wasa na 1,000 a rayuwarsa ta horaswa tun a watan Nuwamba, kuma yana iya kawo ƙarshen wannan tarihin ranar Lahadi ta hanyar jagorantar City karo na 593 — mafi yawan wasannin da wani koci ya taɓa jagoranta a tarihin kungiyar.
Zai zama hanya mai cike da armashi wajen yin bankwana, ko da kuwa an lashe kofin Premier League ko ba a ɗauka ba.










