Shin har yanzu akwai ƴan shidan farko a Premier League?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 7

Shekaru da dama gasar Premier League ta Ingila tana da wata al'ada da aka fi sani da "Ƴan Shidan kan teburi", wadanda ya ƙunshi Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham Hotspur.

Ba wai su ne kawai ƙungiyoyin da suka saba mamaye saman teburin gasar ba, amma sune suka fi yawan magoya baya, suka fi tattalin arziki, kuma galibi su ne suka fi samun nasara a wasannin saboda fitattun yan wasan da suke da su.

Sai dai kuma hakan ya sauya a gasar ba kamar kakar wasannin baya-bayan nan ba.

A cikin 'yan shekarun da suka gabata, Tottenham da Manchester United suna tsintar kansu a ƙasan teburin gasar, yayin da ƙungiyoyi irin su Aston Villa da Brentford da Brighton suka kasance suna fafatawa a saman teburin.

A lokaci guda kuma, Manchester City, wadda ta kasance ƙungiyar da ta mamaye gasar cikin shekaru goma da suka gabata, tana fuskantar wani lokaci na rashin tabbas bayan an samu kungiyar da laifin karya dokokin kuɗi na tsawon shekara tara a kwanan nan.

Har yanzu akwai "Ƴan Shida" idan aka yi la'akari ta fuskar kuɗi, inda Manchester City da Arsenal da Manchester United da Liverpool da Tottenham da kuma Chelsea dukkansu suke cikin ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa masu samun kuɗi mafi yawa.

To sai dai shin ko babu batun ''Yan Shidan'' farko a teburin Premier League a yanzu haka kamar yadda aka saba a baya?

Daga abin almarar lashe kofin Leicester City zuwa ƙalubalen da ta fuskanta

Ɗaya daga cikin labaran da suka fi ɗaukar hankalin mutane a zamanin gasar Premier Leagu shi ne lokacin da Leicester City ta karya duk wani hasashe ta lashe kofin gasar a kakar 2015-16.

Lamarin ya ɗauki hankalin masoya ƙwallon ƙafa a ko'ina, domin a wancan lokaci abin ne mai matuƙar wuya a yi tunanin wata ƙungiya da ba ta cikin "Ƴan Shidan Farko'' za ta iya kusantar daukar kofin babbar gasar tamaula ta Ingila.

Sai dai kuma al'amarin ya faru ne sau ɗaya kacal, domin a kakar uku da suka biyo baya, "Manyan Ƴan Shidan Farko" sun sake mamaye gurare a teburin gasar.

Hasali ma, tazarar da ke tsakaninsu da sauran ƙungiyoyi ta fi kowane lokaci girma, inda mafi ƙarancin bambanci tsakanin ƙungiyar da ta zo ta shida da wadda ta zo ta bakwai a cikin waɗannan kakar uku ya kasance maki takwas.

Tsakanin kakar 2010-11 zuwa 2018-19, abin da ake kira "Ƴan Shidan" sun kare kakar wasa a waɗannan matakin sau biyar. Haka kuma sun kare a cikin manyan bakwan farko sau biyu, sannan cikin manyan takwas din farko sau ɗaya.

Sai dai abubuwa sun sauya bayan wannan lokaci.

A cikin kakar shida da suka gabata tun bayan wancan lokacin, sau ɗaya ne dukkaninsu suka kammala kakar wasa cikin manyan shidan farko a teburi, yayin da Aston Villa da Newcastle da Brighton suka samu gurbi a waɗannan matsayi a wasu lokuta.

Musamman Tottenham ta sha fama da matsaloli, inda ta kare kaka biyu da suka gabata da matsayi ta hudun karshen teburi gurbi daya tsakaninta da yan ukun karshe da suka bar Premier League. A wannan kakar ta bana tana matsayi na biyu a kasan teburi da maki uku, bayan ta kasa cin wasa ko ɗaya daga cikin shida da fara kakar nan.

Duk da cewa gasar Premier League ba ta yi nisaba da fara kakar bana, Manchester United tana matsayi na 13 a teburi da cin wasa daya, yayin da Liverpool take matsayi na tara.

Tun daga kakar 2021-22, Chelsea da Manchester United suna kare kakar wasa ba a cikin yan shidan farkon teburi ba sau biyu, yayin da Tottenham ta kasa shiga matakin har sau biyu har da lokacin da ta kare a mataki na 17 a kasan teburin Premier League.

Gurabe biyar daga cikin Yan shidan farko a teburi da aka saba gani a baya, ya koma ga wasu kungiyoyin da a baya ba a lissafa su a cikin wajen.

Wasu ƙungiyoyi sun ƙara yin arziƙi kuma suna amfani da dabaru masu inganci

Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa aka samu manyan kungiyoyin da suke yan shidan farko a lokacin ya hada da tazarar tattalin arzikin da ke tsakaninsu da sauran kungiyoyin Premier League, to amma yanzu suna rage tazarar da take tsakaninsu

Newcastle na ɗaya daga cikin misalan hakan, wadda bayan kammala cinikin yan wasa a bazara ta kashe fam miliyan 305 wajen sayo sabbin yan kwallo a ƙarƙashin jagorancin Asusun Zuba Jari na Jama'a na Saudiyya a shekarar 2021.

Ƙungiyar ta tashi daga karewa a mataki na 11 a kakar 2021-22 zuwa ta hudu a kakar da ta gabata, sannan ta yi ta biyar a dai kakar gaba.

A gefe guda kuma, wasu ƙungiyoyi kamar Brighton sun mayar da hankali kan amfani da bayanai da kuma dabarun sayen 'yan wasa masu kyau da gogewa kuma matasa, domin rage gibin da ke tsakaninsu da manyan ƙungiyoyin Premier League.

Brighton tana da kyakkyawan tsarin sayen matasa masu hazaka kan kuɗi kaɗan kafin daga baya ta sayar da su da tsoka.

A shekarar 2021 ta ɗauki ɗan wasan Ecuador mai shekara 19, Moises Caicedo daga Independiente del Valle kan fam miliyan 4, sannan ta sayar da shi ga Chelsea a cinikin da ya kai fam miliyan 115, wanda a lokacin shi ne mafi tsada a Birtaniya.

Haka kuma ta sayi Marc Cucurella kan fam miliyan 15, sannan ta sayar da shi ga Chelsea kan fam miliyan 62, yayin da ta ɗauki Alexis Mac Allister kan fam miliyan 7 kafin daga baya ta sayar da shi ga Liverpool a yarjejeniyar da darajar dan wasan ta kai fam miliyan 55.

Rashin ci gaba da gudanar da kyakkyawan tsari ya sa wasu kungiyoyin sun koma baya

Tun bayan da Sir Alex Ferguson ya yi ritaya a shekarar 2013, Manchester United ke fuskantar kalubale, wadda ta kasa koma kan ganiya, bayan dumbin nasarorin da dan kasar Scotland ya samu a tsawon shekara 26 da ya ja ragamar kungiyar Old Trafford.

United mai kofin Premier League 20 jimilla tana ta sauya masu horar da ita, domin taga ta koma lashe kofuna, amma har yanzu ta kasa kamo bakin zaren.

Tun daga 2021 United ta sauya masu horarwa guda hudu, wannan yake nuna maka irin halin da kungiyar ta Old Trafford ta tsinci kanta.

Sai dai ba ita kaɗai ba ce ke yawan sauya masu horarwa, domin wasu kungiyoyin na Premier League ma suna fuskantar koma baya.

A cikin wannan lokaci, Chelsea ta dauki mutane daban-daban guda bakwai a matsayin masu horarwa na dindindin, yayin da Tottenham ta dauki shida yayin da su ma suke ƙoƙarin neman hanyar da za su koma kan ganiya a babbar gasar tamaula ta Ingila.

A gefe guda kuma, Arsenal ta nuna cewa haƙuri na iya haifar da sakamako mai kyau, bayan da ta bai wa Mikel Arteta aikin kociyanta, wanda aka naɗa a shekarar 2019, daga lokaci ya gina ƙungiyar da ta sa Gunners ta kawo ƙarshen shekaru 22 rabon da ta dauki kofin Premier League, wadda ta yi wannan bajinta a kakar da ta wuce.

Ko dai ba koda yaushe canji ke kawo ci gaba ba?

Ba koda yaushe "Yan shidan farkon teburi" Premier League za su ci gaba da mamaye gasar ba, kamar yadda aka sani dole idan iskar canji ta motsa sai an samu sauye-sauye ta yadda za a ga wasu kungiyoyin da ba a yi tsammani ba a babban matakin da zarar sun yi abin da ya kamata.

A hakikanin gaskiya, lokacin da aka ƙaddamar da gasar Premier League a shekarar 1992, akwai abin da ake kira "Yan Biyar" din farko a teburin gasar da suka hada da Arsenal da Everton da Liverpool da Manchester United da Tottenham. A wancan lokacin ana kallon waɗannan ƙungiyoyi a matsayin waɗanda suka fi yawan magoya baya da kuma ƙarfin tattalin arziki.

Daga baya wannan matakin ya rikide zuwa "Yan biyun farko" a teburin Premier League a ƙarshen shekarar 1990 da farkon shekarun 2000, inda Manchester United da Arsenal suka mamaye gasar, kafin daga baya abin ya faɗaɗa zuwa "Yan hudun farko" lokacin da Chelsea da Liverpool suka kara kwazo da suke kare gasar a mataki na uku zuwa na hudu akai-akai.

Kakar 2010-11 ita ce karon farko a tarihin gasar lig ta Ingila da manyan kungiyoyi shida suka kasance Arsenal da Chelsea da Liverpool da Manchester City da Manchester United da kuma Tottenham.

Daga nan kuma an sake maimata hakan a kakar 2014-15 da 2016-17 da 2017-18 da kuma 2018-19.

A baya babu batun yan biyar ko yan shidan farko a Premier League a lokacin da ba a sauya mata fasali ba, inda a daga shekarar 1960 aka samu kungiyoyin da suka lashe kofin da ya hada da Burnley da Tottenham da Ipswich da Everton da Liverpool da Manchester United da Manchester City da kuma Leeds United.

Duk da cewa har yanzu ana ganin mai yiwuwa wadda za ta lashe Premier League na bana za ta iya fitowa daga wadanda suka yi kaurin suna a yan shidan teburi a baya, amma ana ganin zai yi wuya a samun yan shidan farko da aka samu a baya da suke mamaye gasar a bana.

A halin yanzu, Brighton da Brentford da Everton duk suna cikin yan shidan farko a kakar nan, kuma duk da cewa har yanzu akwai wasanni da yawa da za a buga a wannan kakar, saman teburin gasar ya bayyana cewa gasar a bude take komai zai iya faruwa.