Majalisar Dokokin Masar ta ɗage kaɗa ƙuri'ar baiwa Saudiyya tallafin soji
Wasu ‘yan majalisar dokokin Masar guda biyu sun shaida wa AFP cewa an ɗage kaɗa ƙuri’ar da za ta yanke hukunci kan buƙatar Shugaba Abdel Fattah al-Sisi na neman izinin ba da tallafin soji ga Saudiyya.
An dakatar da tattaunawar a zaman yau, sannan aka ɗage batun zuwa gobe Litinin, 19 ga Oktoba.
Wani ɗan majalisar Masar ya bayyana cewa an tsawaita zaman ne domin bai wa dukkan ‘yan majalisar damar yin tsokaci da bayyana ra’ayoyinsu kan batun.
A jiya, Al-Sisi ya roƙi ‘yan majalisar su amince da goyon bayan Saudiyya idan ta nemi taimako wajen fuskantar hare-haren da mayakan Houthi ke kaiwa.
Ya ce: “Na san cewa irin wannan mataki yana buƙatar amincewar majalisar dokokin Masar, saboda haka na nemi a kira taron gaggawa domin a ba mu ikon daukar mataki idan Saudiyya ta nemi hakan.”
Masar ta shiga kawancen sojin da Saudiyya ke jagoranta a Yemen tun shekarar 2015, amma rawar da ta taka ta fi mayar da hankali ne wajen kare hanyoyin jiragen ruwa a Tekun Bahar Maliya, maimakon shiga yaƙi kai tsaye a fagen daga.
Wasu jiga-jigan kungiyar Houthi sun yi gargadin cewa kada Masar ta tsoma baki a yaƙin tana goyon bayan Saudiyya, suna masu cewa irin wannan shiga tsakani zai amfanar da Isra’ila ne a ƙarshe.
Sai dai ba su yi wata barazana kai tsaye ba. Maimakon haka, sun tunatar da Masar game da tsoma bakinta a yaƙin Yemen a shekarun 1960, wanda ya haddasa asarar rayuka masu yawa ga sojojin Masar.