Ko za a iya ɗaukar cutar sanyi ta sifilis ta hanyar sumbata?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Cutar sanyi ta sifilis na daga cikin manyan cutukan da ke damun mutane da dama a faɗin duniya.

Masana lafiya na cewa akwai hanyoyi da dama na kamuwa da cutar, wadda ke yawan yaɗuwa tsakanin ma'aurata.

Jima'i ba tare da kariya ba da kuma kin zuwa a gwajin lafiya na daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa ƙaruwar masu kamuwa da cutar.

Saboda kunya da ƙyamar da al'umma ke nuna wa masu irin waɗannan cututtuka, mutane da dama kan yi ƙoƙarin ɓoye halin da suke ciki na lafiya.

Ana kuma kiran sifilis da suna "mai kisan mummuƙe" domin tana iya daɗewa a jikin mutum ba tare da ta nuna wata alama a zahiri ba a wajen masu kamuwa da ita da yawa.

Babban abin da ya sa sifilis ke ƙaruwa cikin sauri a baya-bayan nan shi ne ƙaruwar jima'i cikin yanayi mai haɗari ba tare da kariya ba.

Kamar yadda likita Nimali Jayasuriya ta bayyana, ƙwayoyin cutar da ke haddasa sifilis na iya yaɗuwa cikin sauri ta kowace irin mu'amalar jima'i da ba a yi amfani da kariya ba, walau tsakanin maza biyu ko kuma tsakanin namiji da mace.

Likitar ta jaddada cewa ana iya kamuwa da sifilis cikin sauƙi har ma ta hanyar jima'i ta baki.

Har ila yau, an samu karuwar mutanen da ke yin jima'i da abokan hulɗa da ba sa cikin dangantaka ta dindindin.

Alamomin cutar

A mafi yawan lokuta, cutar sifilis kan bi matakai huɗu, kuma kowanne mataki na da alamominsa na musamman:

  • Mataki na farko

A wannan mataki, wani ƙurji guda da ba ya haifar da ciwo kan bayyana a wurin da ƙwayar cutar ta shiga jiki, kamar azzakari da farji da dubura, baki ko leɓɓa.

A fannin kiwon lafiya, ana kiran wannan ƙurji da 'chancre'.

Yawanci ƙurjin yana da tsabta saboda ba ya rufewa, kuma yana iya zama kamar ɗan ƙulli idan an taɓa shi.

Saboda ba ya haddasa ciwo, musamman mata na iya kasa gane cewa sun kamu da cutar.

  • Mataki na biyu

A wannan mataki, ƙwayoyin cutar kan bazu a jiki ta hanyar jini da kuma tsarin ruwan lymph.

Alamomin na iya haɗawa da:

Kumburin ƙwayoyin lymph.

Miyagu ko ƙuraje a baki.

Kuraje a wurare daban-daban na jiki.

Baƙaƙen tabo ko kumfa, musamman a tafukan hannu da tafin ƙafa.

Kumburi masu kama da kuraje a al'aura.

Haka kuma cutar na iya shafar idanu, ƙwaƙwalwa da kunnuwa.

  • Matakin ɓoye alamomi

Wannan shi ne matakin da ƙwayoyin cutar ke ci gaba da kasancewa a jiki ba tare da nuna wata alama a zahiri ba.

Sai dai duk da rashin alamomi, mutum na iya ci gaba da yaɗa cutar ga wasu, gwargwadon matakin da cutar take ciki da kuma ko akwai raunuka masu ɗauke da ƙwayoyin cutar.

  • Mataki na ƙarshe

Idan sifilis ta daɗe a jiki ba tare da an yi magani ba, tana iya haddasa mummunar illa ga gabobin ciki.

Illolin na iya haɗawa da:

Matsaloli masu tsanani na zuciya.

Lalacewar tsarin jijiyoyin jiki da kan iya janyo shanyewar sassa na jiki.

Rashin gani ko rashin ji.

Samuwar kumbura ko ƙuraje masu lalata ƙwayoyin halitta da gabobin jiki.

A wannan mataki, cutar na iya zama barazana ga rayuwa idan ba a gano ta tare da yi mata magani da wuri ba.

Ana iya kamuwa da cutar da hanyar sumbata?

"A mafi yawan lokuta, ba a yaɗa cutar sifilis ta hanyar sumbata ko mu'amalar yau da kullum. Sai dai, a wasu lokutan alamomin cutar na iya bayyana a sassa daban-daban na jiki''.

"Alal misali, idan ƙurjin farko na cutar ya bayyana a leɓɓan mutum. Ba wai ta hanyar ruwan da ake musayawa yayin jima'i kaɗai ake kamuwa da sifilis ba, har ila yau ana iya kamuwa da ita idan wurin da ke ɗauke da cutar ya yi hulɗa kai tsaye da wani sashe na jikin wani mutum.

"Sai dai kamuwa da cutar ba ya faruwa kawai saboda taɓa lafiyayyar fata. Amma idan leɓe ko bakin mai ɗauke da sifilis mai ƙurji ya haɗu da wata ƙaramar rauni a jikin wani mutum, akwai yiwuwar a samu kamuwa da cutar. Musamman idan mai sifilis ɗin yana da ƙurji a fili, cutar na iya yaɗuwa ta irin wannan hulɗa."

Ƙwararriyar likita Nimali Jayasuriya ta ce: "Saboda haka, a mafi yawan lokuta ba a kamuwa da sifilis ta hanyar sumbatar mutumin da ba shi da wata alama da ke nuna yana ɗauke da cutar."

Ko ana warkewa daga cutar sanyi ta sifilis?

Ƙwararriyar likita Dakta Nimali Jayasuriya ta ce ana iya warkar da cutar sifilis gaba ɗaya idan aka yi amfani da magungunan da suka dace.

"Eh, ana iya warkar da sifilis gaba ɗaya. Babban maganin cutar shi ne allurar wani magani da ake kira benzathine penicillin. Dangane da matakin da cutar take ciki da kuma nau'inta, wasu marasa lafiya na buƙatar allura guda ɗaya, wasu biyu, wasu kuma uku."

"Sai dai idan ƙwayoyin cutar sun bazu a sassan jiki kuma suna iya shafar tsarin jijiyoyin jiki, mai cutar na iya buƙatar jinya na kusan kwanaki 10. Idan mutum ya kammala maganin da ƙwararren ma'aikacin lafiya ya rubuta masa, za a iya warkar da wannan cuta gaba ɗaya," in ji ta.

Cutar na kashe mutane?

Cutar sifilis na iya jawo mutuwa idan ba a gano ta tare da yi mata magani a kan lokaci ba.

Mutuwa kan faru ne sakamakon mummunan illolin da cutar ke haifarwa idan ta daɗe a jiki ba tare da magani ba.

Ƙwayoyin cutar da ke haifar da sifilis na iya shafar zuciya, su haddasa matsaloli masu tsanani na zuciya, har da gazawar zuciya wajen gudanar da aikinta yadda ya kamata, lamarin da zai iya kai ga mutuwa.

Ko da kuwa cutar ba ta kai ga mutuwa ba, illolinta na dogon lokaci na iya matuƙar shafar rayuwar mara lafiya.

Waɗannan illoli sun haɗa da rasa ikon tafiya, shanyewar wani sashe na jiki ko gaba ɗayansa sakamakon lalacewar tsarin jijiyoyin jiki, rasa gani, da kuma rasa ji.

Ta yaya sifilis ke shafar juna biyu?

Idan mace mai juna biyu ta kamu da cutar sifilis kuma ba ta samu ingantaccen magani ba, cutar na iya haifar da mummunar illa ga jaririn da take ɗauke da shi.

A cewar ƙwararriyar likita Dakta Nimali Jayasuriya, ƙwayoyin cutar da ke cikin jikin mahaifiya na iya tsallakawa ta cikin mahaifa su isa jikin jariri.

Mummunan sakamakon da zai iya biyo baya ya haɗa da zubar da ciki ko haihuwar jariri matacce.

A wasu lokutan kuma, jariri na iya haihuwa da rai amma ya kasance cikin babban haɗarin mutuwa a cikin kwanakin farko bayan haihuwarsa.

Idan jaririn ya rayu, yana iya kasancewa an haife shi da wata cuta da ake kira sifilis ta haihuwa (congenital syphilis).

A irin wannan yanayi, ƙwayoyin cutar kan bazu a duk jikin jaririn su haifar da matsaloli iri-iri, ciki har da kumburin hanta da saifa, munanan cututtukan fata, matsalolin gani, da rashin daidaiton girman ƙasusuwa.

Yayin da yaron ke girma, yana iya fuskantar matsalolin tsarin ginin jiki da kuma lalacewar wasu gabobin ciki, ciki har da rasa ji.

Waɗannan illoli na iya ci gaba da kasancewa tare da shi har tsawon rayuwarsa.

Sai dai idan aka yi wa mai juna biyu gwajin sifilis da wuri a lokacin ɗaukar ciki kuma ta samu maganin da ya dace, ana iya rage yiwuwar kamuwa da jaririn da cutar matuƙar gaske.