Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wane ne Moussa Kaka, ɗanjaridar da ya yi ɓatan-dabo a jamhuriyar Nijar?
Kimanin wata guda kenan ba a ji ɗuriyar fitaccen ɗanjaridar nan na jamhuriyar Nijar ba, Moussa Kaka wanda ya bar ofishinsa zuwa gidansa da misalin ƙarfe 7 na yammacin ranar 31 ga watan Agustan 2026.
Tun daga lokacin, iyalansa da abokan aikinsa ba su samu damar tuntubar sa ba, yayin da ita ma motarsa ta ɓace.
Bacewarsa ta tayar da hankalin ƙungiyoyin kare 'yancin 'yan jarida da na farar hula, waɗanda ke kira ga hukumomin Nijar da su bayyana inda yake da kuma tabbatar da lafiyarsa.
Ƙungiyar G25-Niger ta ce ɓacewar Moussa Kaka ta faru ne a cikin wani yanayi mai matuƙar tayar da hankali, kuma tana tunatar da irin abubuwan da aka riga aka gani a ƙarƙashin mulkin sojan Janar Abdourahamane Tiani tun bayan juyin mulkin 26 ga Yulin 2023.
Moussa Kaka na ɗaya daga cikin fitattun 'yan jarida a Jamhuriyar Nijar. Shi ne Babban Daraktan gidan rediyo da talabijin na RTS (Radio Télévision Saraounia), kuma tsohon wakilin Radio France Internationale (RFI) ne.
Tsawon fiye da shekaru talatin, Moussa Kaka ya shahara wajen ba da rahotanni kan harkokin siyasa, tsaro, rikice-rikice masu ɗauke da makamai, da batutuwan mulki a Nijar da yankin Sahel baki ɗaya.
Martanin ƙungiyar G25-Niger
Ƙungiyar fararen hula da ta ƙunshi ƙungiyoyi da dama na 'yan jarida da ƙwararu a bangaren sadarwa, da 'yan fafutuka mai sunan G-25 NIGER, da ke da cibiyar ta a Turai ta ce al'amarin ya ƙara haifar da damuwa saboda hukumomin Niamey sun ci gaba da yin shiru tun daga lokacin, shiru da ake ganin ba na al'ada ba ne.
Haka kuma, ƙungiyar G25-Niger, ta bayyana damuwarta sosai tare da neman a sake shi cikin gaggawa idan yana hannun hukumomi.
ƙungiyar a wata sanarwa da ta fitar ta ce ta bi diddigi kuma ta gano hannun mutanen da ya faɗa.
"Bisa ga bayanan da ƙungiyar ta tattara, jami'an sirri sun bi sawun Moussa Kaka tun daga ofishinsa da ke Kalley-East kafin wasu mutane su tare motarsa a kusa da madauwar Gadafawa, suka tafi da shi tare da motarsa," in ji sanarwar.
Ƙungiyar ta ce tana da yakinin cewa Moussa Kaka na hannun hukumar DGDSE (hukumar tsaron ƙasa), wadda Bala Arabé ke jagoranta.
Ƙungiyar ta kuma ƙara da wasu bayanai kamar haka:
- Tana nuna matuƙar nuna damuwa kan wannan ɓacewa, wadda ba ita ce ta farko irinta ba.
- Tana buƙatar a saki Moussa Kaka nan take ba tare da wani sharadi ba, ko wane ne ya ɗauke shi kuma ko mene ne dalilinsa.
- Tana alawadai da wannan ɓacewa tare da sake jaddada buƙatar ganin an dawo wa Moussa Kaka da 'yancinsa cikin gaggawa.
- Tana tunatar da cewa tun bayan hawan Janar Abdourahamane Tiani kan mulki, an tsare 'yan jarida da dama tare da ɓacewar wasu 'yan ƙasa a yanayi makamancin wannan.
- Tana kira ga hukumomin da ke mulki a halin yanzu da su yi cikakken bincike kan ɓacewar Moussa Kaka, su fitar da duk bayanan da suke da su cikin gaggawa, tare da ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da lafiyarsa da dawowarsa gida lafiya.
- A ƙarshe, G25-Niger ta ɗora alhakin duk wani abu da zai samu Moussa Kaka da sauran mutanen da ake zargin an kwashe su ba bisa ka'ida ba a kan Janar Tiani.
Me gwamnati ta ce?
Kawo yanzu dai babu wabi martani da hukumomin da ƙungiyar G25-Niger ta zarga da kama fitaccen ɗanjaridar.
To sai dai ƙungiyoyin kamar ƙungiyar da ke kare ƴanjarida ta Committee to Protect Journalists (CPJ), da ta ƴanjaridu marasa shinge ta Reporters Without Borders (RSF) da kuma ƙungiyar kare haƙƙin bil'adama ta Human Rights Watch sun nemi hukumomin Nijar su yi bincike tare da bayyana inda yake. Ya zuwa yanzu, babu wata sanarwar hukuma da ta yi cikakken bayani kan inda yake ko abin da ya same shi
Wannan dai kamar yadda ƙungiyar G25-Niger ta fadi ba shi ne karon farko ba na faruwar irin wannan yanayin da za a wayi gari a nemi ɗanjarida a rasa.
- Ƙungiyoyin suna zargin gwamnatin sojin ta Nijar da abubuwa kamar haka:
- Kama da tsare ƴanjarida
- Matsin lamba kan kafafen yada labarai da masu sukar gwamnati.
- Ɓacewar mutane cikin yanayi mai ruɗani.
Ita ma ƙungiyar Human Rights Watch ta zargi gwamnatin sojin Nijar da ƙara tsaurara matakan da suka haɗa da rushe wasu ƙungiyoyin farar hula, tsare masu adawa da gwamnati, da ƙuntata ayyukan kafafen yaɗa labarai.