Abin da ƴansanda suka ce kan hawan doki a Kano

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Hukumomi a Kano sun sake jaddada dokar da ta haramta hawan doki ko wani nau'in na dabbobi wajen zirga-zirga, tare da gargaɗin jama'a da su kiyaye dokar domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kwamishinan ƴansandan jihar Kano, Ibrahim Adamu Bakori ne ya bayyana hakan a zantawarsa da BBC, inda ya nanata cewa an ɗauki matakin ne bayan gwamnati ta samu rahotannin cewa wasu mutane sun karya dokar da aka sanya a ranar Asabar, duk da bai ambata waɗanda suka karya dokar ba.

A cewarsa, bayan samun rahoton cewa an karya dokar, gwamnati ta sake jaddada umarnin tare da hada kai da jami'an tsaro domin tabbatar da bin dokar.

"Abin da ya faru shi ne, ranar Asabar gwamnatin Kano ta bayar da umarni tare da sanya doka da ta hana hawa; wato an hana amfani da kowace irin dabba wajen hawa," in ji Bakori.

Ya ce jami'an tsaro za su kula da duk wani yunƙuri na hawa, kuma duk wanda ke da buƙatar yin hakan sai ya sanar da jami'an tsaro tun da farko.

"Duk wanda zai yi hawa na kowace irin dabba ya sanar da jami'an tsaro. Ni ne zan kira sauran jami'an tsaro, idan mun amince, za mu bayar da tsaron da za a yi lafiya," in ji shi.

Su wane ne suka karya doka?

Bakori ya kuma bayyana cewa matakin ya samo asali ne daga buƙatar tabbatar da tsaro, musamman ganin cewa mutane da yawa kan hau doki a wuraren taruwar jama'a, lamarin da zai iya sa ya yi wahala a gane wadanda ke cikin jerin masu dokin.

A game da waɗanda yake nufi da cewa sun karya doka, kwamishinan ya ce, "jama'a da yawa suna hawa doki, ba za a iya gane su wane ne ba. Amma mun samu rahoton sirri ne, sai aka tabbatar," in ji Bakori.

Da aka tambaye shi ko akwai yiwuwar kama waɗanda aka samu suna karya dokar, ya ce a halin yanzu an fi mayar da hankali wajen gargaɗi da wayar da kan jama'a kan muhimmancin bin dokar.

"Yanzu mun bayar da kashedi, muna so kuma a kiyaye, saboda da mu da su duka zaman lafiya ake nema," ya bayyana.

Dangane da wasu mutane da suka bayyana iƙirarin cewa idan wani ɓangare ya hau doki, su ma za su hau, Bakori ya ce hukumomi na ci gaba da tsara matakan da suka dace domin magance duk wani abu da zai iya kawo cikas ga tsaro.

"Muna cikin tsare-tsare. Kila sun yi wannan maganar ne kafin wannan dokar," in ji shi.

Abin da ya faru

Tun da farko, gwamnatin Kano ce ta ɗauki matakin hana yin hawan dawaki a babban birnin jihar a cikin ƙarshen makon jiya.

Sanarwar haramta hawan ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da wani hawan doki da ke cikin jerin bukukuwan da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya tsara yi, lamarin da ya haifar da martani daga ɓangarori daban-daban.

An dai ruwaito cewa ko da sanarwar ta fita, Sarki Aminu Ado Bayero ya riga ya fita a doki, inda wasu rahotanni suka bayyana cewa bai koma gida a dokin ba, inda ya koma a ƙafa.

Sai dai bayan komawa gida ne aka ga wani faifan bidiyo yana kara-kaina a kafofin sadarwa, inda a ciki aka ji ɗaya daga cikin makusantan Sarki Aminu, Aminu Babba Dan Agundi yana cewa sun yi biyayya ga umarnin gwamnati na dakatar da hawan.

Sai dai ya yi barazanar cewa duk lokacin da wani ya yi hawa, su ma ɓangarensu zai hau dokin.

Sai dai ana cikin haka ne aka ga wasu faya-fayan bidiyon Sarki Muhammadu Sanusi II a saman doki a ranar bikin ƴancin kan Najeriya, inda rahotanni suka nuna cewa a dokin ya je filin bikin.

Wannan ne ya ƙara jan hankalin mutane, inda muhawara ta kaure kan batun ganin lamarin ya zo a daidai lokacin da ake magana kan gargaɗin na gwamnatin Kano da kuma iƙirarin ɓangaren su Babba Ɗan Agundi.

Ko da yake gwamnati ta bayyana dalilan da suka sa ta ɗauki matakin hana hawan dokin, masu bibiyar al'amuran masarautar na ganin lamarin ya sake bayyana yadda rikicin ke ci gaba da yin tasiri a harkokin masarautar.

Rikicin masarautar Kano

Rikicin da masarautar Kano ta kwashe shekaru tana fama da shi ya janyo ce-ce-ku-ce tun bayan sauye-sauyen da gwamnatin jihar ta yi kan harkokin masarautun jihar, wanda ya haddasa shari'o'i da kuma saɓanin ra'ayi tsakanin masu ruwa da tsaki.

Rikicin masarautar Kano ya samo asali ne tun a shekarar 2020 lokacin da gwamnan jihar na wancan lokaci Abdullahi Ganduje ya sauya dokar masarautar, inda ya raba masarautar zuwa biyar tare da sauke Muhammadu Sanusi II daga kan karaga.

Sai dai gwamnan jihar da ya biyo baya, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024, wadda ta rushe masarautun jihar tare da mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan mulki.

To sai dai tun wancan lokacin aka riƙa ɗauki ba daɗi a kotu har zuwa wannan lokaci, duk da cewa a baya-bayan nan lamarin ya lafa bayan da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da kuma gwamna mai ci Abba Kabir suka haɗu a jam'iyya ɗaya, wato ta APC.

To amma tambayar da mutane da dama ke yi ita ce, yaushe ne za a kawo ƙarshen wannan rikici da ya dade yana haifar da rashin tabbas a kan makomar masarautar Kano?

Barista Nuhu Hamza Dantani, ƙwararren lauya masanin dokokin Najeriya ya ce abin da ya sa aka kasa kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano ba ya rasa nasaba da siyasa.

''Kuma ka san duk wani al'amari ko doka ko ƙa'ida idan ya haɗu da siyasa sai ka ga yana tafiyar hawainiya,'' in ji shi.

To amma Nuhu Dantani ya ce "ita shari'a mace ce da ciki ba a san yaushe za ta haifu ba".

Ya ce ana iya ƙare shari'ar a shekarar mai kamawa da kotun ta saka domin fara sauraron ƙarar, ana kuma iya wuce shekarar ma ba a ƙare ta ba.

''Amma ni a ganina wannan shari'a bai kamata ta wuce shekarar mai zuwa ba, saboda ba ta da sarƙaƙiya sosai''.