Me ya shiga tsakanin Ronaldo da kocin Portugal?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Magoya bayan Portugal sun fara ganin yadda tawagar ta buga wasa ba tare da Cristiano Ronaldo ba, bayan da ƙasar ta doke Denmark da ci 4-2 a gasar Nations League ranar Alhamis.

Joao Cancelo da Goncalo Ramos ne suka bai wa baƙin damar cin kwallo biyu, yayin da Mikkel Damsgaard da Rasmus Hojlund suka farke wa Denmark.

Tsohon ɗan wasan Manchester United, Hojlund, ya yi murnan cin kwallon da ya ci da kwaikwayon salon yadda Ronaldo ke yi 'Siuuu' da zarar Ronaldo ya zura kwallo a raga - kuma wannan ne karo na biyu da Hojlund ya yi irin haka a wani lokaci da suka fafata da Portugal.

Vitinha ya sake ci wa Portugal kwalo na uku, sannan Joao Felix ya ƙara ta huɗu a Copenhagen da ta kai Portugal ta samu maki uku..

Wannan ne karon farko da Portugal ta buga wasa tun bayan da Ronaldo mai shekara 41, wanda shi ne mafi zura ƙwallaye a tarihin ƙwallon ƙafar ƙasashe, ya bar sansanin kasar, bayan an ajiye shi a benci a wasan da suka yi da Norway.

Bayan nasarar da suka samu a Denmark, koci Jorge Jesus mai shekaru 72 ya ce: "Akwai ƴan wasa masu matsayi na musamman. Wannan abu ne a fili.

"Amma zan sake faɗa - ƙa'idojin iri ɗaya ne ga kowa. Wannan ita ce hanyar da na bi a duk tsawon aikina na horarwa, kuma zan ci gaba da bin ta."

'Yar'uwar Ronaldo, Elma Aveiro, ta rubuta a shafukan sada zumunta tun da farko cewa: "Cin amana abinci ne da aka fi jin daɗinsa idan aka ci shi a hankali."

An shafe shekaru ana ganin kamar ba za a iya cire Ronaldo daga cikin tawagar ba - bayan da ya ci wa Portugal ƙwallo 146 a wasa 234.

Sai dai a shekarun baya da kokarinsa ya ragu, an fara cece-kuce cewa wataƙila ɗan wasan Al-Nassr, wanda ya ci ƙwallo 979 jimila a rayuwarsa ta ƙwallon ƙafa, yana hana tawagar yin abin da ya dace.

BBC Sport ta duba wannan muhawara da kuma yadda ake kallon lamarin.

'Ba za ka yi wa Cristiano haka ba' - Wai me ya faru ne?

Ronaldo ya sake haɗuwa da tsohon kocinsa a Al-Nassr, Jesus, a wannan bazarar bayan da Roberto Martinez ya yi murabus daga matsayin kocin Portugal, saboda kasa taka rawar gani a gasar cin kofin duniya.

Ronaldo ya fara taka leda karkashin sabon kociyan Portugal a karawar da ta doke Wales da ci 1-0 a Nations League - amma bai buga wasan da suka nasara a kan Norway da ci 2-1 ba a fafatawa ta biyu a gasar.

Wannan ne karon farko tun shekarar 2008 da Ronaldo ya kasance a benci ba tare da an saka shi a wasa ba.

Koci, Jesus ya musanta cewa akwai wata matsala tsakaninsu, amma daga baya Ronaldo ya bar sansanin tawagar - yana mai cewa zai bayyana dalilan da suka sa ya bar sansanin "a lokacin da ya dace".

Wataƙila abin ya zo wa mutane da dama a matsayin abin mamaki, amma rashin jitwa tsakanin Cristiano Ronaldo da Jorge Jesus na daga cikin rikice-rikicen da aka fi tsammanin za su faru. Mutane biyu ne daga cikin manyan masu fada a ji a Portugal suna kuma aiki a wuri guda.

Ana iya cewa Ronaldo shi ne ɗaya daga cikin, ko kuma mafi girman dan wasan Portugal a tarihi. Shi kuwa Jesus, a nasa ɓangaren, ya taɓa cewa yana ganin kansa a matsayin kociyan da ba kamarsa a duniya.

Ko da yake wannan magana ana iya muhawara a kanta, mutum ne mai tsaurin ra'ayi. Babu wani abu daga abin da ke faruwa a yanzu da ya zo wa magoya bayan Portugal da mamaki, domin sun saba da ganin fushin Jesus da kuma yadda yake faɗin abin da yake tunani kai tsaye.

Idan akwai wani mutum da zai iya ƙalubalantar matsayin Ronaldo a tawagar Portugal to Jesus ne. Ya taɓa yin hakan da Neymar a Al-Hilal, inda ya gaya wa ɗan wasan Brazil cewa ya "Ta kare masa".

A lokacin da yake kocin Belenenses, tun kafin ya shahara sosai, Jesus ya ma taɓa fuskantar mawakin Amurka 50 Cent tare da dakatar da gwajin sauti da yake yi a filin wasa na Restelo da cewar saukin yana katsalandan ga atisayen ƙungiyar.

Ba ya tsoron kowa, kuma hakan ya nuna babban bambanci da salon tsohon koci, Roberto Martinez, wanda ya kasance mai matuƙar diflomasiyya.

Ronaldo ya fahimci saƙon sosai, inda ya yanke shawarar tattara kayansa ya bar tawagar ƙasa.

Daga cikin kociyoyin Portugal biyar na baya-bayan nan, Ronaldo ya samu matsala da huɗu daga cikinsu – Carlos Queiroz da Paulo Bento da Fernando Santos da kuma na yanzu Jesus.

Wannan ba irin halayyar da ake tsammani daga kyaftin ɗin tawagar ƙasa ba ce.

Ko Portugal ta fi kyau ba tare da Ronaldo ba? Me alkalumma suka ce?

Babu shakka cewa Ronaldo ya kasance fitaccen ɗan wasan Portugal gaba ɗaya, inda ya taimaka wa ƙasar ta lashe Euro 2016 - kuma yana cikin jerin manyan ƴan wasan ƙwallon ƙafa da aka taɓa gani a tarihi.

Ya karya tarihin wanda ya fi zura ƙwallaye a matakin ƙasa shekaru da suka wuce a Portugal, kuma bai taɓa daina zura ƙwallaye yadda ya kamata ba.

Wanda ya lashe kyautar Ballon d'Or sau biyar shi ne wanda ya fi zura ƙwallaye a tarihin gasar European Championship - kuma shi ne ɗan wasa kaɗai da ya ci ƙwallaye a gasar Kofin Duniya guda shida.

Sai dai a cikin ƴan shekarun da suka gabata, an shafe ana ta muhawara kan ko yana hana ci gaban kwazon Portugal. A zahiri, wannan tambaya ce da ake ta yi kusan shekara biyar da suka gabata.

A Kofin Duniya na 2022, Fernando Santos ya nuna ƙarfin hali wajen ajiye shi a benci a wasannin zagayen ƙarshe, amma a wannan bazarar ya buga wasanni da yawa ƙarƙashin koci, Martinez.

A cikin shekaru biyar da suka gabata, Ronaldo ya rasa wasanni biyu kacal na neman gurbin shiga Kofin Duniya ko Euro, kuma duka biyun saboda dakatarwa ce, inda Portugal ta samu manyan nasarorin da ta taɓa samu a tarihinta - ta doke Luxembourg da ci 9-0 da Armenia da ci 9-1.

Tun daga shekarar 2017, kaso na nasarar Portugal ba tare da Ronaldo ya ɗan fi yawa - kashi 64% idan aka kwatanta da 63% - kuma tana zura ƙwallaye 2.7 a kowane wasa ba tare da shi ba, idan aka kwatanta da 2.1 tare da shi a cikin fili.