Yaushe za a kawo ƙarshen taƙaddamar masarautar Kano?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 8

Matakin da gwamnatin Kano ta ɗauka na hana yin hawan dawaki a babban birnin jihar cikin ƙarshen mako ya sake tuno wa al'umma taƙaddamar da ake yi a masarautar ta Kano mai ɗimbin tarihi.

Sanarwar haramta hawan ta zo ne a daidai lokacin da ake shirin gudanar da wani hawan doki da ke cikin jerin bukukuwan da Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero ya tsara yi, lamarin da ya haifar da martani daga bangarori daban-daban.

Rikicin masarautar Kano ta kwashe shekaru tana fama da shi ya janyo ce-ce-ku-ce tun bayan sauye-sauyen da gwamnatin jihar ta yi kan harkokin masarautun jihar, wanda ya haddasa shari'o'i da kuma sabanin ra'ayi tsakanin masu ruwa da tsaki.

Ko da yake gwamnati ta bayyana dalilan da suka sa ta ɗauki matakin hana hawan dokin, masu bibiyar al'amuran masarautar na ganin lamarin ya sake bayyana yadda rikicin ke ci gaba da yin tasiri a harkokin masarautar.

Rikicin masarautar Kano ya samo asali ne tun a shekarar 2020 lokacin da gwamnan jihar na wancan lokaci Abdullahi Ganduje ya sauya dokar masarautar, inda ya raba masarautar zuwa biyar tare da sauke Muhammadu Sanusi II daga kan karaga.

Sai dai gwamnan jihar da ya biyo baya, Abba Kabir Yusuf ya sanya hannu kan sabuwar dokar masarautun jihar ta 2024, wadda ta rushe masarautun jihar tare da mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan mulki.

To sai dai tun wancan lokacin aka riƙa ɗauki ba daɗi a kotu har zuwa wannan lokaci, duk da cewa a baya-bayan nan lamarin ya lafa bayan da tsohon gwamnan jihar Abdullahi Ganduje da kuma gwamna mai ci Abba Kabir suka haɗu a jam'iyya ɗaya.

To amma tambayar da mutane da dama ke yi ita ce, yaushe ne za a kawo ƙarshen wannan rikici da ya dade yana haifar da rashin tabbas a kan makomar masarautar Kano?

Matakin da aka tsaya yanzu

A ranar 19 ga watan Afrilun wannan shekara ne Kotun ƙolin ƙasar, wadda shari'ar ke gabanta ta ɗage sauraron shari'ar zuwa ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2027 mai kamawa.

Ɓangaren Sarki Aminu Ado Bayero ne ya shigar da ƙarar zuwa Kotun Ƙolin ƙasar, yana ƙalubalantar matakin dokar rushe masarautun jihar, lamarin da ya shafi sarautarsa.

Tun bayan da gwamnnatin jihar ta aiwatar da dokar, ɓangaren Sarki Aminu Bayero ke ƙalubalantar sauye-sauyen inda suka je kotuna daban-daban kafin zuwa kotun ƙolin da ta ɗage zaman har na tsawon shekara biyu.

Hukuncin Ƙotun Ƙolin na watan Afrilu ya sa al'amura sun lafa dangane da batun masarautar, sai a wannan mako ya sake tasowa, sakamakon sabuwar dokar da gwmanatin jihar ta saka game da hawa doki.

Gwamnatin ta saka dokar ne a daidai lokacin da Sarki Aminu ado ya shirya wani hawan daba a ƙarshen mako, lamarin da ya sa suka zargi gwamnatin da saka dokar da nufin muzguna musu.

Sai dai a nata ɓangare gwamnatin ta ce ta saka dokar ne bayan samun bayanan sirri kan tsaro a lokacin hawan.

Me ya sa aka kasa kawo ƙarshen rikicin?

Barista Nuhu Hamza Dantani, ƙwararren lauya masanin dokokin Najeriya ya ce abin da ya sa aka kasa kawo ƙarshen rikicin masarautar Kano ba ya rasa nasaba da siyasa.

''Kuma ka san duk wani al'amari ko doka ko ƙa'ida idan ya haɗu da siyasa sai ka ga yana tafiyar hawainiya,'' in ji shi.

Ya ci gaba da cewa sai ka rasa inda batun ya dosa. ''Ko shakka babu ni a ganina wannan ba ya rasa nasaba da batun siyasa'', in ji shi.

Me ya sa kotu ta saka lokaci mai tsawo?

A watan Afrilun da ya gabata ne dai Kotun Ƙolin ƙasar ta ɗage shari'ar zuwa Afrilun shekarar 2027, wani abu da ya sa mutane da dama mamakin yadda aka ɗage shari'ar zuwa shekara guda.

To amma Barista Nuhu Hamza Dantani ya ce akwai wasu abubuwa da Kotun koli ke la'akari da su wajen ɗage shari zuwa dogon lokaci irin wannan ko ma fiye.

''Ɗaya daga cikin dalilan shi ne ka san ita Kotun ƙoli, ita kaɗai ce a duka faɗin Najeriya, kuma takan saurarin manyan shari'o'i daga jihohin ƙasar 36, don haka dole ne ta riƙa saka lokaci mai rata, don samun lokacin wasu shari'o'in'', in ji shi.

Masanin harkokin shari'ar ya ƙara da cewa a yanzu haka akwai wata shari'a da kotun ƙolin ta ɗage zuwa 2028 domin fara sauraron ta.

Barista Nuhu Dantani ya ce wani dalilin da Kotun za ta iya la'akari da shi wajen saka dogon lokaci, shi ne zaman lafiyar jihar.

''Wataƙila kotun ta yi la'akari da zaman lafiyar jihar da kuma fargabar samun fitina, shi ya sa ta saka dogon lokaci ta yadda zukatan al'umma za su kwanta wasu ma su manta da batun'', in ji shi.

Yaushe za a kawo ƙarshen rikicin

Wannan ita ce tambayar da mutane da dama suke yi, duk lokacin da aka ɗago dambarwar masarautar Kanon.

To amma Nuhu Dantani ya ce "ita shari'a mace ce da ciki ba a san yaushe za ta haifu ba".

Ya ce ana iya ƙare shari'ar a shekarar mai kamawa da kotun ta saka domin fara sauraron ƙarar, ana kuma iya wuce shekarar ma ba a ƙare ta ba.

''Amma ni a ganina wannan shari'a bai kamata ta wuce shekarar mai zuwa ba, saboda ba ta da sarƙaƙiya sosai''.

''Ni a ganina ma wannan shari'a bai kamata a ce ta kawo yanzu ba, saboda ba wasu abubuwa ba ne masu tsauri ba, rigima ce ta wane ne yake da iko da sauya doka da wanda ba shi da shi, da batun hanyar da ya kamata a bi, da wadda bai kamata ba'',

Ya ci gaba da cewa bai kamata a ce shari'ar ta kawo wannan lokaci ba.

Yadda rikicin ya samo asali

A watan Mayun shekarar 2024 ne majalisar dokoki ta jihar Kano ta amince da rushe duka masarautun jihar bayan soke sabuwar dokar da ta ƙirƙiri sababbin masarautu ta shekarar 2019.

Majalisar ta bayyana cewa rushe sabuwar dokar na nufin cewa za a koma amfani da tsohuwar dokar da ta kafa masarautar Kano.

Sabon matakin da majalisar ta ɗauka ne ya rushe sarakunan jihar biyar na Kano, da Bichi, da Ƙaraye, da Gaya, da Rano.

A lokacin ne kuma majalisar ta gabatar da sabuwar dokar da za ta ƙirƙiri sabbin sarakuna masu daraja ta biyu.

A sabuwar dokar, gwamnatin Kano ta tsara masarautun kamar haka:

  • Masarautar Kano: Masarautar Kano ita ce mai daraja ta ɗaya, inda sauran sarakuna masu daraja ta biyu za su zama ƙarƙashin ikon sarkin Kano mai daraja ta ɗaya. Masarautar mai daraja ta ɗaya na da iko na kai tsaye da hakiman ƙananan hukumomi 36 daga cikin 44 na jihar.
  • Masarautar Rano: Sarki mai daraja ta biyu na wannan masarauta na da ƙananan hukumomi uku wato Rano da Bunkure da Kibiya
  • Masarautar Ƙaraye: Ita kuma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi guda biyu na Ƙaraye da Rogo.
  • Masarautar Gaya: Ita ma wannan masarautar mai daraja ta biyu ta ƙunshi ƙananan hukumomi uku na Gaya da Ajingi da kuma Albasu.

Shari'o'i kan rikicin sarautar Kano

A ranar Litinin, 15 ga watan Yuli ne mai shari'a Amina Aliyu ta babbar kotun jihar Kano ta umarci sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero da sauran sarakuna huɗu na Rano, Ƙaraye, Bichi da Gaya da su daina ayyana kansu a matsayin sarakai.

Kotun ta kuma umarci sarakunan biyar da su miƙa duk wasu kaya na sarauta mallakar masarauta ga gwamnatin jiha.

Majalisar dokokin jihar Kano ce dai ta shigar da Aminu Ado Bayero da ƴan sanda da sojoji a gaban kotun.

To sai dai kuma kafin hukuncin, babbar kotun tarayya da ke zamanta a jihar Kano ta yanke hukuncin cewa dokar da ta rushe masarautu a jihar na nan daram amma kuma ta soke aiwatar da dokar wadda gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

A lokacin yanke hukuncin, Mai Shari'a Abdullahi Muhammad Liman ya ce ba daidai ba ne gwamnan jihar Kano ya aiwatar da dokar soke masarautun saboda akwai umurnin kotun da aka bayar da ya dakatar da duk wani yunƙuri na gwamnan Kano wajen aiwatar da sabuwar dokar da ta cire rawanin sarakuna biyar a jihar ta Kano.

Mai shari'a Liman ya ce "A don haka na bayar da umurnin cewa dukkan matakan da gwamnati ta ɗauka na soke su amma hakan bai shafi sabuwar dokar masarautu ba. Amma sun shafi matakan da gwamna ya dauka ciki har da sanya hannu a sabuwar doka da kuma sake nada Sanusi".

Kotun ta ce "An soke dukkan matakan da masu kare kai a shari'ar suka ɗauka, amma kuma hakan bai shafi dokar ba."

Bisa dokar ne dai gwamna Abba Kabir Yusuf ya rushe sarakunan biyar ciki har da Alhaji Aminu Ado Bayero ya kuma sake naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sarki na 16, bayan da tsohon gwaman jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tuɓe shi a 2020.

A ranar 23 ga watan na Mayu ne ɗaya daga cikin masu naɗa sarkin Kano, Alhaji Aminu Babba Ɗan Agundi ya ƙalubalanci dokar a babbar kotun tarayyar da ke Kano, sannan ya ce za su garzaya kotu na gaba.

Wane ne Muhammadu Sanusi II?

An haife shi a zuriyar sarakunan Fulani a ranar 31 ga watan Yuli 1961.

Jika ne ga sarki Sanusi da aka sauke daga gadon sarauta.

Ya samu digiri a fannin tsimi da tanadi da fannin addini Musulunci.

An nada shi mukamin gwamnan Babban Bankin Nigeria (CBN) a watan Yuni 2009.

Mujallar Banker ta bayyana shi a matsayin gwarzon shekara a 2010.

An dakatar da shi a watan Fabrairu bayan sun samu sabani da shugaban kasa.

An kuma nada shi a matsayin Sarkin Kano ranar 8 ga watan Yuni 2014.

Sunansa ya canja daga Sanusi Lamido Sanusi zuwa Muhammad Sanusi II.

An sauke Muhammadu Sanusi daga sarauta ranar a watan Maris 2020.

An sake naɗa shi sarkin Kano a watan Mayun 2024.

Wane ne Aminu Ado Bayero?

An haifi Alhaji Aminu Bayero a birnin Kano ranar 21 ga watan Agusta, 1961, gabanin mahaifinsa Ado Bayero ya zama sarkin Kano da shekara biyu.

A 1990 mahaifinsa Alhaji Ado Bayero ya fara ba shi mukamin sarauta, inda aka nada shi Dan Majen Kano kuma Hakimin Nassarawa.

Daga nan ne kuma aka kara masa girma zuwa Dan Majen Kano Hakimin Gwale a dai shekarar ta 1990.

A shekrar 1991 kuma likkafa ta kara gaba inda aka nada shi Turakin Kano kuma Hakimin Dala a watan Janairun 1991 zuwa Janairun 2001, ma'ana dai ya shekara 10 a wannan mukami.

Alhaji Aminu Ado Bayero ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida, Hakimin Dala daga watan Janairun 2001 mukamin da ya rike har zuwa 2014.

An naɗa Aminu Ado Bayero a matsayin sarkin Kano cikin watan Maris 2020.

Majalisar dokokin jihar Kano ta rusa sabuwar dokar masarautar Kano a watan Mayun 2024, abin da ya rushe masarautu biyar na jihar.