Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙarancin mai da aka shiga a 1970, ko mun doshi ganin mafi muni a yanzu?
- Marubuci, Rachel Clun
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporter
- Lokacin karatu: Minti 3
Rufe wata hanyar ruwa mai muhimmanci wadda ake amfani da ita wajen kai mai a faɗin duniya ya janyo fargabar cewa duniya na iya shiga matsalar ƙarancin mai fiye da wadda aka taɓa gani a shekarun 1970.
Lars Jensen, wani ƙwararre kan jigilar kayayyaki ta ruwa, ya faɗa wa BBC cewa tasirin yaƙin Amurka da Isra'ila kan Iran zai iya yin yawa fiye da na ruɗanin tattalin arziki da aka gani a 1970.
Kalamansa na zuwa ne bayan gargaɗin da shugaban hukumar makamshi ta duniya Fatih Birol ya yi a farkon wannan wata cewa duniya na "babbar barazanar ƙarancin makamashi a tarihi".
"Lamarin zai fi wanda muka taɓa gani a 1970, farashin mai ya yi mugun tashi. Kuma ya fi na ƙaruwar farashin iskar gas da muka fuskanta bayan mamayar Rasha a Ukraine," kamar yadda ya faɗa wa BBC.
Sai dai yayin da rufe mashigar Hormuz ya kawo cikas a ɓangaren samar da mai a duniya, wasu sun kalubalanci cewa duniya ta fi juriya a yanzu.
Wane irin matsalar mai aka shiga a 1970?
Matsalar mai da aka fuskanta a shekarun 1970 ya sha bambab da wannan da ake gani a yau, saboda na wancan lokaci ya faru ne sakamakon wasu tsare-tsare da aka aiwatar dagan-gan," a cewar masaniya kan tattalin arzkiki Dr Carol Nakhle, ta faɗa wa BBC.
A watan Oktoban 1973, masu samar da mai daga ƙasashen Larabawa sun sanya takunkumi kan wasu ƙasashe karkashin jagorancin Amurka bisa goyon baya da suka bai wa Isra'ila a lokacin yaƙin Yom Kippur. Tsarin ya zo haɗe da batun rage samar da mai.
"Sakamakon haka ne farashin mai ya kusa ninƙawa sau huɗu a watannin farko na yaƙin," in ji Nakhle.
Wannan ya haifar da tashin farashin man fetur a manyan kasashen da ke mu'amala da mai, kuma Nakhle ya ce hakan ya haifar da "matsalar tattalin arziki da kuma na kuɗi a duniya".
Dakta Tiarnán Heaney, wani mai bincike a jami'ar Queen da ke Belfast, ya ce ƙaruwar farashin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki a faɗin duniya, "ma'ana kasuwanni sun durkushe kuma rashin aikin yi ya karu".
"Wannan ya yi tasiri sosai da kuma lalata masana'antun musamman na ɗinki a ƙasashe da dama da suka fuskanci yajin aiki, tashe-tashen hankula, da ƙaruwar talauci, inda magidanta da dama suka shiga matsi na abin da za su kai bakin salati," in ji shi.
Amurka da Birtaniya sun samu tawayar tattalin arziki wanda ya daɗe daga 1973 zuwa 1975, tare da rikicin da ya janyo faduwar gwamnatin Ted Heath a 1974.
Me ke faruwa a matsalar mai da ake ciki yanzu?
Tun bayan da Amurka da Isra'ila suka kaddamar da yaƙi kan Iran a watan da ya gabata, an rufe mashigar Hormuz mai muhimmanci wajen kai kayayyaki a faɗin duniya.
Lamarin ya janyo cikas wajen fitar da mai, iskar gas da kuma sauran kayayyaki na buƙatu a faɗin ƙasashen yankin Gulf, wanda ya saba fitar da kashi biyar na mai da ake amfani da shi a duniya.
Shugaban Amurka Donald Trump ya yi amfani da dabaru da dama don ganin an fita daga matsalar, ciki har da kira ga ƙawayen ƙasar su tura jiragen ruwa na yaƙi da za su yi rakiya, da kuma barazanar ci gaba da kai hare-hare Iran idan ba su bar jiragen ruwa suka wuce cikin aminci ba ta mashigar.
Sai dai Jensen, wani ƙwararre kan jigilar kayayyaki ta ruwa, ya shaida wa BBC cewa yawancin mai da ya bar yankin Gulf a watan da ya gabata na ci gaba da isa matatun mai a faɗin duniya, kuma nan ba da jimawa za a dakatar da jigila.
"Matsalar ƙarancin mai da muke gani za ta ƙara yin muni, ko da gobe za a buɗe mashigar Hormuz," in ji shi.
"Za mu fuskanci gagarumin matsalar makamashi - ba wai idan wannan yaƙi ya ci gaba ba, illa har na tsawon watanni shida zuwa 12 idan yaƙin ya kare."
Shin matsalar mai ta yanzu za ta iya fin na 1970 muni?
Nakhle, wadda ita ce sakatare-janar na ƙungiyar makamashi ta Larabawa, ta ce kasuwar mai ta yanzu ta bambanta da ta shekarun 1970, yayin da yawan kuɗi da ake zuba wa ma ya ragu.
Ta yi imanin cewa yayin da farashi ya haura, amma matsalar da ake ciki yanzu ba ta kai ta da muni ba.
"Yayin da yawan mai da ake fitarwa ya ragu - wanda an daɗe ba a ga haka ba - amma kasuwannin yanzu sun fi juriya fiye da na shekarun 1970," in ji ta.
Sai dai Joel Hancock, darektan bincike kan farashin mai a wata cibiya, ya ce wani abin bambanci shi ne matsalar ƙarancin mai ta 1970 ta ta'allaka ne kan ƙasashen da suka cigaba, waɗanda ke da kuɗi da kuma "ƙarfin siyasa" wajen shawo kanta.
Matsalar yanzu ta fi shafar ƙasashe masu tasowa, "waɗanda ba su da kuɗi da hukumomin da za su iya fita daga matsalar," in ji shi.
Hancock ya ce matsalar da ake ciki a yanzu za ta kare "da zarar an kawo karshen yaƙi."