Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Ƙasashen da al'umma suka fi farin ciki a duniya cikin shekara 2026
Yayin da ƙasashen yankin arewacin Turai da ake wa laƙabi da 'Nordic' suka daɗe suna mamaye Rahoton Farin Ciki na Duniya, sai dai an samu sauyi a rahoton 2026 .
A karon farko a cikin shekaru 14 da aka ɗauka ana fitar da rahoton, wata ƙasa daga yankin Latin Amurka ta shiga jerin ƙasashe biyar na farko da suka kasance wurare mafi farin ciki a duniya - yayin da Costa Rica ta ci gaba da haura wa zuwa sama, inda ta yi tsalle daga na 23 a shekarar 2023 zuwa na huɗu a 2026.
Jerin wanda cibiyar nazarin lafiya ta Oxford ke fitarwa tare da haɗin gwiwar hukumar ci gaba mai ɗorewa ta Majalisar Ɗinkin Duniya, na la'akari ne da yanayin ƙarfin tattalin arziki, da tallafin zamantakewa, da tsawon rayuwa, da ƴancin walwala a ƙasashe 140 na duniya.
A cikin shekara biyu a jere, babu wata ƙasar Turai da ta shiga jeri na 10, inda Australiya ke na 15, Amurka na 23, Canada 25 sannan Birtaniya a matsayi na 29.
Wannan shekara, ƙasashen da ke sama guda biyar, dukkansu suna da abubuwa masu muhimmanci da suka taimaka wajen samar musu da farin ciki.
Mun tattauna da mazauna waɗannan ƙasashe domin gano abin da ya taimaka wajen samar musu da farin ciki na tsawon lokaci - da kuma yadda matafiya za su ɗanɗani irin farin cikin da suka samu idan suka kai ziyara.
1. Finland
Finland ta sake zama ta ɗaya a matsayin ƙasa mafi farin ciki a duniya. Kuma shi ne karo na tara cikin shekara goma da take zuwa matsayin.
Ta samu maki ne saboda ƙarancin cin hanci da rashawa a ƙasar ga kuma tallafin zamantakewa, inda mazauna suka yi farin ciki da irin tallafin da suke samu - ciki har da na ilimi da kiwon lafiya - wanda ya taimaka wajen samar musu da tsananin farin ciki.
"Ina jin daɗin cewa Finland na cikin kariya kuma zan yar da da kowa a nan," in ji wani mai suna Olli Salo. "Yara na tafiya makaranta daga shekara bakwai, ba za ka ji fargabar wani abu ba yayin da kake komawa gida, sannan in wani ya yi maka alkawari zai cika."
Sai dai ƴan ƙasar ba su damu da yawan harajin da suke biya ba saboda irin yanayin ingantaccen rayuwa da suke yi. "Ana tallafawa abubuwa masu muhimmanci kamar lafiya, ilimi da kuma sufuri , don haka me ya sa ka ba za ka biya haraji don jin daɗi ba?" in ji Salo.
Farin ciki na zuwa ne salon rayuwa mai kyau, in ji magajin birnin Helsinki, Daniel Sazonov. "Samun damar fita waje, sannan ka isa bakin teku, ko wurin shakaatwa ko kuma gandun daji cikin mintoci kaɗan abu ne mai muhimmanci.
2. Iceland
Iceland ta wuce Denmark zuwa matsayi na biyu karon farko tun 2024, ƙasar mai mutum 400,000 an bayyana ta ta farko wajen ba da tallafin zamantakewa.
An kuma saka ta cikin jeri na 10 na arzikin cikin gida na ƙasa, ga kyautatuwar yanayin lafiya da kuma karamci.
"Tsawon ƙarni, babu wani taimako daga waje da muka samu. Mu kaɗai ke abin mu, kuma dole ne ta sa muka tsaya da juna," in ji Ingibjörg Friðriksdóttir, wani mazaunin ƙasar. "Wannan ya haifar al'adar taimakon juna."
Ƴan ƙasar sun kuma fuskanci manyan bala'oi na guguwa.
"Idan lokaci rani ya zo, ba za to ba tsammani muna samun hasken rana kusan dukan dare, kuma hakan na sa kowa na kara samun kuzari da farin ciki," in ji wani mazaunin ƙasar.
Kowane irin yanayi ake ciki, mazauna ƙasar na bai wa baki shawarar fita waje ba tare da la'akari da yanayin ba.
"Shakar iska, kallon wuraren ban sha'awa da kuma jin ƴanci na cikin abubuwan da suka ƙarawa ƙasar mu daɗin zama da zama babbar ƙasa," in ji Björnsdóttir.
3. Denmark
Denmark ba ta taɓa sauka zuwa kasan mataki na huɗu ba a tarihin rahoton, kuma a kowace shekara a jeri na sama take fitowa.
Ta zo na uku a wannan shekara, sannan tana matsayi na uku a duniya wajen ba da tallafin zamantakewa da kuma mai ƙaranci wajen aikata cin hanci da rashawa, sai na bakwai a ɓangaren tattalin arzikin cikin gida.
"Farin ciki ba wai murmushi a fuska ko dariya kaɗai bane a Denmark," in ji Laura Halla wata ƴar jarida. "idan aka ce farin ciki ana nufin yarda ko amana cikin al'umma sannan da jin cewwa kowa na aiki don samun nasara."
Hall na da 'ya'ya mata biyu a can kuma ta ce akwai dawwamammen tsaro. Har ila yau, ta cde tana son birnin Copenhagen, wanda ya sauya daga hanyar ruwa na masana'antu a shekarun 1990 zuwa wurin da mazauna ke iyo a duk shekara yanzu.
4. Costa Rica
Costa Rica da ta haura matsayi na huɗu a wannan shekara, ta kasance ƙasar ta farko daga Latin Amurka ta shiga jeri na biyar, inda ƴancin tofa albarkacin baki da tallafin zamantakewar ƙasar suka kusa ninƙawa tun 2021.
Mazauna ƙasar sun bayyana ƙaruwar ƴancin zaɓar yanayin rayuwa. Sun kuma rayuwarsu na cikin annashuwa da farin ciki, a cewar rahoton.
Da aka tambaya me ya sa Costa Rica ta zama wuri mai farin ciki, wani mazaunin ƙasar Adrian Hunt bai yi wata-wata ba ya ce "Al'umma, al'umma, al'umma," in ji shi. "Samun mutanen da ra'ayinku ya zo ɗaya na samun ingantaccen rayuwa abu ne da ba zai misaltu ba.
"Ina ganin Costa Rica ta fi kowace ƙasa yanayin salon rayuwa mai inganci a tsakiyar Amurka," in ji Hunt. "Akwai wani abu da mutanen ƙasar, wato ƴan asalin ƙasar da kuma ƴan waje saboda irin yanayin kuzari da suke da shi, wannan shi ya sa ƙasar ta zama ta musamman."
5. Sweden
Sweden ita ce ƙasa ta biyar da ta fi farin ciki a duniya. Ta tashi daga matsayi na goma a tsawon shekaru goma da suka wuce zuwa matsayi na biyar ɗin.
Sannan ita ce ta bakwai a duniya a ɓangaren ingantaccen lafiya, sai kuma na biyar na ƙarancin rashawa.
"Abin ya sa Sweden ta ci gaba da kasancewa saman jerin ƙasashe masu farin ciki shine saboda ita karamar ƙasa ce," a cewar Micael Dahlen, farfesa kan ɓangaren lafiya mai kyau, walwala da kuma farin ciki. "Mutane ba su nisa da juna, birane ba su da nisa, muna rayuwa mai daɗi da kuma rungumar sabbin ra'ayoyi da mutane."
"Ko kai wane irin mutum ne - mawaki ne, mai rubuce-rubuce, firaminista ko kuma farfesan farin ciki kamar ni, kai ne kai," in ji Dahlen.