Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a faɗin duniya, 06/03/2026

Taƙaitattu

  • An gano gawa biyu a Isra'ila bayan harin Iran kan wani gida
  • 'Za mu buɗe mashigar Hormuz idan jiragen sun amince su biya ɓarnar yaƙin
  • IRGC ta ce Amurka da Isra'ila sun kashe shugaban sashen leƙen asirinta'
  • Isra'ila ta ɗauki alhakin kisan shugaban leƙen asirin IGRC
  • Harin Iran ya kashe mutum huɗu a Haifa na Isra'ila
  • Isra'ila ta ce ta kai hari kan muhimmiyar cibiyar tace mai ta Iran

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza

  1. Isra'ila ce ba ta son zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya - Erdogan

    Shugaban Turkiye, Recep Tayyip Erdogan ya zargi Isra'ila da yin zagon ƙasa ga dukkan wasu shirye-shiryen kawo ƙarshen rikicin da Gabas ta Tsakiya ke ciki.

    Erdogan ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da aiki wajen ganin an cimma tsagaita wuta duk da halin na Isra'ila.

    "Burinmu shi ne wannan yakin maras halasci na rashin hankali kuma mai tsada ga dukkannin ƴan adam ya zo ƙarshe," in ji Erdogan yayin wani taron ministocinsa na mako-mako a birnin Ankara.

    Ergogan ya kuma ce Turkiyya tana bin dukkan hanyoyin diflomasiyya wajen kawo ƙarshen yaƙin, "kasancewar idan har yakin ya ci gaba to zai warwatsu ga sauran ƙasashe."

    Turkiye ta yi yunƙurin ganin an kawo ƙarshen wannan yaƙi ta hanyar haɗa hannu da sauran masu shiga tsakani da suka hada da Pakistan da Egypt.

  2. Faɗa tsakanin Hamas da ƙunyiyoyi masu ɗauke da makamai ya janyo mutuwar mutum 10

    An kashe Falasdinawa 10 a Gaza bayan fada ya barke tsakanin mambobin Hamas da kuma masu dauke da makamai da ke goyon bayan Isra'ila kafin Isra'ila ta kaddamar da hare hare.

    Babu wani cikakken bayani akan fadan da aka yi a sansanin 'yan gudun hijirah da ke Maghazi.

    Wannan rikici na baya bayannan ya kasance kalubale ga yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Hamas da Isra'ila.

    Jami'an lafiya a Gaza sun ce an kashe Falasdinawa fiye da 700 tun bayan cimma yarjejeniyar.

  3. 'Mu ne ya kamata mu karɓi haraji a Hormuz tunda mu muka yi nasara'

    Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce Amurka ce ya kamata ta rinƙa karɓar ladan wucewa ta mashigar Hormuz ba Iran ba.

    Trump ya faɗi hakan ne yayin da aka tambaye shi ko zai iya kammala yaƙin sannan kuma ya bar Iran a kan bakanta na karɓar ladan shigewa ta mashigar?

    "Mu ne muka yi nasara," in ji shi. "An ci galaba a kansu... muna da tunanin inda muke son karɓar haraji."

    Trump ya faɗi hakan ne domin cimma wa'adinsa na awa 48 da ya sanya na ko dai Iran ta buɗe mashigar Hormuz ko kuma ta gane kuranta wanda zai kawo ƙarshe da misalin ƙarfe 20:00 na ranar Talata wanda ya yi daidai da ƙarfe 0100 na ranar Laraba.

    Trump ya ce akwai buƙatar cimma yarjejeniyar da Iran - na amince da hakan, yana mai cewa "wani tsagi na yarjejeniyar shi ne muna son a samu sufurin mai ba tare da matsala ba."

  4. Israel Kartz ya ce sun kai hari kan masana'antar albarkatun mai na Iran

    Ministan tsaron Isra'ila ya ce sojojin kasar sun kai hari kan babbar masana'antar sarrafa albarkatun man fetur da dangoginsa da ke Asaluyeh.

    Israel Katz, ya ce a yanzu masana'antar tare da wata da ke kusa da ita, wadda ita ma aka kai mata hari sun daina aiki.

    Ya ce masana'ntun biyu su ne ke samar da kashi 85 cikin dari na kayayyakin da ake samarwa daga man fetur, wadanda Iran ke fitarwa kasashen waje.

    Iran din dai ba ta fito fili ta tabbatar da cewa masana'antun sun daina aiki ba. Tun da farko mataimakin ministan harkokin wajen Iran, ya ce barazanar da Trump ya yi ta cewa za su kai hari kan kayayyakin da ba na soji ba, da suka hada da gadoji da tashoshin samar da lantarki, ka iya zama laifin yaki.

    Iran din ta yi gargadin cewa muddin aka kai mata wannan hari, to kuwa za ta mayar da mummunan martani mai girman gaske.

  5. Da gaske ne sha'awar ma'aurata na dakushewa?

    A shekara ta 1990 Alan Reeves yakan yi rawa tsirara a gaban dubban mutane yayin da yake mamba a ƙungiyar Dreamboys. Ya yi farin jini sosai inda ake neman sa a lokuta da dama tare da abokansa masu rawa, sun taɓa fitowa a fim ɗin Spice Girls mai suna Spice World.

    A wancan lokaci ya na da shekara 24 da haihuwa.

    Amma da ya kai shekara 30, sai ya tsinci kansa a mawuyaci hali- sha'awarsa ta ragu ƙwarai.

    "Ba na jin daɗin jikina," in ji shi.

    Reeves mai shekaru 52 a yanzu ya ce rashin sha'awa ya zamar masa ƙalubale a alaƙarsa.

  6. Ina ne mashigar Hormuz, kuma me ya sa take da muhimmanci?

    Tun bayan da yaƙin Amurka da Isra'ila a Iran ya ɓarke, sai maganar mashigar Hormuz ta fara faɗaɗa da jan hankali, inda mutane suke ta tambayar ina ne mashigar, kuma ma ya sa take da matuƙar muhimmanci.

    Duk da cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa yana samun nasara sosai a yaƙin, wani abu da ake ganin tamkar ya tsaya masa a wuya shi ne batun datse mashigar ta Hormuz.

    Trump ya sha nanata cewa zai tura sojojin ruwan Amurka, sannan ya nemi taimakon wasu ƙasashen domin tabbatar da cewa an buɗe mashigar domin a ci gaba da tafiyar da ɗanyen mai

    Kusan kashi biyar na ɗanyen man da ake amfani da shi a duniya yana bi ta mashigar ne mai girman kilomita 40.

    Tsohon shugaban hukumar leƙen asirin Birtaniya wato M16, Sir Alex Younger ya shaida wa BBC cewa daga cikin manyan matsalolin da yaƙin zai haifar akwai datse tekun. "Datse tekun zai haifar da matsalar tattalin arziki mai girma saboda yadda zai shafi farashin man fetur."

  7. Harin ƴanbindiga ya kashe mutum 10 a Kebbi

    Rahotanni daga jihar Kebbi da ke rewacin Najeriya na cewa ƴanbindiga sun shiga wasu ƙauyuka a yankin ƙaramar hukumar Shanga tare da kashe aƙalla sama da mutum 10.

    Ƴanbindigar waɗanda ake kyautata zaton cewa ƴanmahmuda ne sun shiga garuruwan yankin da dama ciki har da garin Kawara lamarin da ya sa jama’ar garin da dama fantsama a cikin daji domin tsira da rayukansu.

    Wani mutumin da BBC ta zanta da shi daga cikin dajin ya ce yanzu haka yaransu na kukan yunwa da kishi yayin da suke ɓuya a cikin dajin.

    Shi ma wani mazaunin garin da BBC ta zanta da shi ya ce maharan sun shiga garin ne daga jihar Neja.

    Ya ci gaba da cewa maharan sun ƙona gidaje masu yawa, kuma maharan na nemn mafaka a wani dutse da ke kusa da garin na Kawara.

    BBC ta tuntuɓi shugaban ƙaramar hukumar Shanga, wanda ya tabbatar d aharin, sai dai ya ce zuwa yanzu ƙaramar hukumar ta aika wani kwamiti zuwa yankin kasancewarsa ƙetaren ruwa ne mai wuyar shiga.

  8. Iran ta yi watsi da tsagaita wuta

    Kamfanin dillancin labaran mallakar gwamnatin Iran ya rawaito cewa Iran ta aike da martaninta ga daftarin dakatar da yaƙi da Amurka ta fitar.

    Kamfanin ya rawaito wasu buƙatu guda 10 a matsayin martanin na Iran da suka hada da yin watsi da tsagaita wuta, inda ta ce dakatar da yaƙi suke buƙata ba tsagaita wuta.

  9. An yanke wa tsohon gwamna hukuncin ɗaurin shekara 14 a Rasha

    Wata kotu a Rasha ta yanke wa tsohon gwamnan yankin Kursk hukuncin ɗaurin shekara 14 saboda samunsa da laifin cin hanci.

    An samu Alexei Smirnov da laifin ɓarnatar da kuɗin da aka ware domin gina ƙatuwar katangar tsaro a kan iyakar Rasha da Ukraine.

    Mista Smirnov na ɗaya daga cikin mutanen Rasha da ake tuhuma kan abin da ake gani a matsayin babbar badaƙala a Rasha.

    Wanda ya gaje shi a matsayin gwamnan yankin, Roman Starovoit, harbe kansa ya yi a lokacin da ya ji ana bincikarsa kan alaƙa da badaƙalar.

  10. Ƴan'uwan masu ibadar da aka sace a Kaduna sun musanta iƙirarin sojoji na ceto su

    Mazauna garin Arikon da ke jihar Kaduna sun musanta iƙirarin sojojin ƙasar na kuɓutar da mutum 31 cikin masu ibadar da ƴanbindiga suka sace a garin.

    A ranar Lahadi ne wasu mahara suka auka wa Cocin Evangelica da ke garin Arikon na yankin ƙaramar hukumar Kachia a jihar Kaduna tare da sace masu ibada.

    Lamarin ya haifar da martani da suka a ƙasar da ke fama da matsalar tsaro.

    Cikin wata sanarwa da rundunar sojin ƙasar ta fitar, ta bayyana yadda dakarunta suka tilasta wa maharan guduwa su ''bar gomman mutanen da suka sacen''.

    To amma al'ummar garin sun musanta iƙirarin sojojin.

    Jaridar Daily Trust ta ambato shugabannin ƙungiyar al'ummar garin na cewa ƴan'uwan nasu na hannun maharan, inda ma tuni ƴanbindigar suka fara tuntuɓar iyalan wasu daga cikin mutanen domin neman kuɗin fansa.

  11. Sojojin Isra'ila sun kashe wani mutum bisa tunanin jami'in Hezbollah ne

    A wani yunƙuri na kisan wani jigon Hezbollah a Lebanon ranar Lahadi, sojojin Isra'ila sun kashe wani babban jigo a wata ƙungiyar siyasa wadda ba ta ga maciji da Hezbollah.

    Yayin da BBC ta tuntuɓi sojojin Isra'ilar, sun amince da kai harin, wanda suka ce ya yi kuskuren kan wurin da ba a nufa ba, da suka ce sun yi ''takaicin cutar'' da fararen hula.

    Rundunar sojin Lebanon, wadda Kiristoci suka fi yawa a ciki, ta ce hari kan wani gida ya kashe babban jami'in mai suna Pierre Mouawad tare da matarsa Flavia.

    Gidan nasu na yankin Ain Saadeh, wanda mafi yawan mazaunansa Kiristoci ne da ke gabashin Birnin Beirut.

  12. Iran da Amurka sun karɓi daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta daga Pakistan

    Iran da Amurka sun ce sun karɓi daftarin shawarar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ƙasashen biyu.

    Daftarin wanda Pakistan - Mai shiga tsakani - ta tsara shi an aika shi ne jami'an Washington da Tehran cikin daren da ya gabata.

    Yarjejeniyar ta ƙunshi matakai biyu, tsagaita wuta nan take da kuma buɗe mashigar Hormuz, wanda kashi 20 na man fetur da iskar gas na duniya ke bi ta wurin.

    Iran ta ce tana nazarin yarjejeniyar, amma ta ce ba za ta amince da buɗe mashigar Hormuz bisa sharaɗin tsagaita wuta na wucin gadi ba.

  13. Isra'ila ta ce ta kai hari kan muhimmiyar cibiyar sarrafa kayayyakin da ake samu daga man fetur

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz ya fitar da wata sanarwa da ke cewa dakarun ƙasar sun kai hari kan cibiyar sassara abubuwan da ake yi daga ɗanyen man fetur ta Iran, yayin da ya ce an umarni dakarun Isra'ila su ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin Iran ''da ƙarfin soji''.

    "Dakarun IDF sun kai hari kan babbar cibiyar tace mai da ke Asaluyeh, bayan makamancin harin da aka kai wa wata cibiyar a makon jiya'', a cewar Katz.

    Sanarwar ta ƙara da cewa "a yanzu duka cibiyoyin biyu, da ke tace kashi 85 na man da ƙasar ke fitarwa - sun daina aiki.''

    Mista Katz ya ci gaba da cewa cibiyar - wadda ke Asaluyeh na samar da kusan rabin man da Iran ke amfani da shi a cikin gida.

    Kamfanin dillancin labarai na Tasnim ya bayar da rahoton kai hare-hare kan kamfanonin man guda biyu.

  14. Harin Iran ya kashe mutum huɗu a Haifa na Isra'ila

    Bayanai daga Haifa na Isra'ila sun ce an gano gawarwaki huɗu daga cikin wani ginin gida da ya ruguje bayan harin makamin Iran mai linzami ya faɗa kan ginin a ranar Lahadi.

    Jami'an tsaro sun ce akwai bom da ya maƙale cikin ɓaraguzan da bai tashi ba, lamarin da ya sa aikin ceton ya zama mai sarƙaƙiya.

    Rahotonni sun ce sai da masu aikin ceton suka haƙa rami ta ƙarƙashin wani gida mai maƙwabtaka da ginin domin iya ceto mutanen huɗu da suka maƙale.

    Wani mazaunin yankin, Mor Barel ya ce duk da na'urorin kakkaɓo hare-hare da Isra'ila ke da su, har yanzu wasu ƴan ƙasar na rayuwa cikin fargabar hari a kowace rana.

    Ƙuri'ar jin ra'ayin jama'a ta nuna yadda ƴan ƙasar suka rage goyon bayan yaƙin da aka kwashe fiye da mako biyar ana yi.

    Isra'ila na iƙirarin samun nasarar kai hare-hare kan cibiyoyin ƙera makaman linzamin Iran da kisan shugabanninta, amma har yanzu ƙasar na harba makaman linzami zuwa Isra'ilar.

  15. Sojoji sun kashe ƴanbindiga 65 a Zamfara ciki har da ƴaƴan Ado Aleiro 3

    Rahotonni daga jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya sun bayyana cewa jami'an tsaron ƙasar sun yi nasarar kashe wasu manyan barayin daji 65 .

    Bayanai sun ce daga cikin waɗanda aka kashe har da ƴaƴan ƙasurgumin ɗanfashin daji Ado Aleiru uku waɗanda suka addabi yankin Tsafe.

    Mannir Sani Fura Girke ɗanjarida ne mai binciken ayyukan ƴanbindiga a arewa maso yammcin Najeriya ya kuma shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne lokacin da ƴanbindigar, ƙarƙashin jagorancin Ado Aleiro suka yi yunƙurin kai hari kan sabon sansanin jami'an tsaro da aka buɗe a garin ƙunshin Kalgo, inda kuma jami'an tsaron suka mayar da martani.

    ''Tun maraicen ranar Asabar ɓangarorin biyu suke musayar wuta tsakaninsu har zuwa wayewar garin Lahadi ake fafatawa'', in ji shi.

    Ya ci gaba da cewa fafatawar ta yi sanadin kisan ƴanbindigar kusan 65, ciki har da ƴaƴan Ado Aleiro.

    ''Daga ciki akwai ƴaƴan Ado Aliero na cikinsa har guda uku, ciki har da babban ɗansa, Sarki da Ahmadu da Iliya, duka ƴaƴansa ne na cikinsa, kuma an kashe su'', in ji ɗanjaridar.

    Mannir Girke ya ce baya da ƴaƴan Ado Aliero an kuma kashe manƴan kwamandojin tawagar tasa da suka haɗa da Kacalla Hukuma da Kacalla Dogo Burti da Kacalla Baƙin Sifindi da Kacalla Mani Mugu da Kacalla Iliya mai Rasha.

    ''Duka waɗannan su ne manyan jagororin tawagar da suka jagoranci wannan faɗan'', kamar yadda ya yi ƙarin haske.

    Mai bincike kan ayyukan ƴanfashin dajin ya ce ba a jima da buɗe sabon sansanin sojin a garin Ƙuncin Kalgo, wanda ke kusa da dajin Munhaye, da ya yi ƙaurin suna a matsayin mafakar ƴanbindiga.

    ''Duk ɓarayin da suka fito daga dajin Munhaye ta Ƙuncin Kalgo suke bi domin su je yammacin tsafe, ko su bu hanyar Gusau ko su je Faskari ko su shiga yankuna Bakori da Kankara'', in ji shi.

    Ya ce girka jami'an tsaro a wannan sabon sansanin ba ƙaramar nasara ba ce ga rundunar sojin Najeriya, musamman a wannan muri mai matuƙar muhimmanci ga ayyukan ƴanbindigar.

  16. Isra'ila ta ɗauki alhakin kisan shugaban leƙen asirin IGRC

    Ministan tsaron Isra'ila, Israel Katz da rundunar sojin ƙasar sun yi iƙirarin kashe shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar Juyin juya halin Iran, Majid Khademi.

    Cikin wani sako da rundunar sojin Isra'ila, IDF ta wallafa a shafinta na Telegram sun ce kisan nasa ''babban koma-baya'' ne ga rundunar juyin juya halin Iran.

    Iran ce dai ta fara bayyana kisan nasa, wanda ba haka aka saba gani ba a baya.

    An naɗa Khademi matsayin shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar IRGC kwana huɗu bayan Isra'ila ta kashe Mohammad Kazemi a ranar 15 ga watan Yunin 2025.

  17. An samu rahotonnin samun fashewa a Rasha

    An bayar da rahotannin samun wata fashewa birnin Novorossiysk na kudancin Rasha, wanda mai tashar jiragen ruwa, inda kafofin yaɗa labarai na ƙasar ke cewa harin jirgin sama maras matuƙi ne na Ukraine ya faɗa kan wata babbar tashar fitar da mai waje.

    Magajin garin, Andrei Kravchenko, ya ce tarkacen hari na jirgin sun samu wani ginin da mutane ke zaune.

    Ba a dai samu rahoton wanda harin ya jikkata ba Tun da farko, rahotanni sun ce an koma aikin loda ɗanyen mai a muhimmiyar tashar jirgin ruwa ta Rasha ta Ust-Luga, bayan da aka dakatar da aiki a tashar saboda hare-haren Ukraine a yankin.

  18. IRGC ta ce Amurka da Isra'ila sun kashe shugaban sashen leƙen asirinta

    Rundunar Juyin Juya Halin Iran (IRGC) ta tabbatar da mutuwar shugaban sashen tattara bayanan sirri na rundunar, Majid Khademi.

    Cikin wata sanarwa da rundunar IRGC ta fitar da safiyar yau Litinin ta zargi Isra'ila da Amurka da kai masa hari.

    BBC ta tuntuɓi rundunar sojin Isra'ila, wadda ta ce za ta ''duba'' rahoton.

    Khademi ne ya maye gurbin Mohammad Kazemi, wanda ya mutu a hare-haren Isra'ila ranar 15 ga watan Yunin 2025, lokacin yaƙin kwana 12 tsakanin Isra'ila da Iran.

    A watan Fabrairun da ya wuce lokacin zanga-zangar ƙasar, Khademi ya zargi Shugaba Trump na Amurka da tunzura abinda jami'an Iran suka bayyana da kitsa dabarar ''kashe mutane'', da nufin kafa hujjar far wa ƙasar daga ƙetare.

    A lokacin Khademi ya yi iƙirarin cewa fiye da jami'an leƙen asiri 10 daga ƙasashen waje, ciki har da sashen yaƙin Intanet na Isra'ila ne suka taka raw a kitsa zanga-zangar.

    Wani kamfanin dillancin labarai na Amurka da ke gwagwarmayar kare haƙƙin bil'adama, ya ce aƙalla mutum 7,000 ne aka kashe a lokacin zanga-zangar ta watan Janairu.

  19. Iran ta ce babu tabbas kan shigarta Gasar Kofin Duniya

    Iran ta ce babu tabbas ga me da shigar tawagar 'yan wasanta a gasar kwallon kafa ta Kofin Duniya mai zuwa, har sai Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, Fifa ta sauya wasannin da Iran ɗin za ta yi daga Amurka zuwa Mexico.

    Ministan wasanni na Iran Ahmad Donyamali ya ce ba shi da tabbacin samun tsaron lafiyar ƴanwasan Iran a Amurka.

    Fifa ta ƙi sauya wasannin Iran ɗin duk kuwa da cewa Shugaba Trump ɗin kansa ya ce, shigar tawagar Iran Amurka ka iya jefa su cikin hadari.

    Iran za ta kara da New Zealand da Belgium da kuma Masar a biranen California da Seattle.

  20. 'Za mu buɗe mashigar Hormuz idan jiragen sun amince su biya ɓarnar da yaƙin ya yi mana'

    Wani hadimin fadar shugaban Iran, Mahdi Tabatabaei ya ce za a sake buɗu mashigar Hormuz idan har ''jiragen da za su wuce ta mashigar sun amince su riƙa biyan harajin da za a yi amfani da shi don gyara ɓarnar da yaƙin ya yi wa ƙasar''.

    A baya jami'ai da ƴanmajalisar Iran sun bayyana yiwuwar sanya haraji kan duka jirgin da zai wuce ta mashigar.

    Yayin da yake mayar da martani da barazanar Trump ta baya-bayan nan, Tabatabaei ya ce shugaban na Amurka ''ya riga ya haifar da yaƙi a Gabas ta Tsakiya yanzu kuma yana sake wata barazana''

    Ya ce ''ɓaɓatu da hauragiyar'' da Trump ke yi alamu ne ya yadda ya ''kiɗime da ruɗewar'' da yake ciki.