Villa na sa ido kan Endrick, Bournemouth ba za ta siyar da Scott ba

Endrick
Bayanan hoto, Endrick
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

A shirye Aston Villa suke su ɗauki ɗan wasan Brazil Endrick a matsayin ɗan wasan aro, bayan da ɗan wasan ya gaza burge Jose Mourinho Real Madrid J. (Cadena SER - in Spanish)

Paris St-Germain da Liverpool na harin ɗan wasan Rayan Cherki daga Manchester City, idan ɗan wasan ya zama mai zaman kansa.(Teamtalk)

Ɗan wasan Ajax Aaron Bouwman, na cikin jerin ƴan wasan da Newcastle ke sa ido a kansu, nan da kakar siyen ƴan wasa biyu da ke tafe. (Newcastle Chronicle)

Arsenal na cikin jerin ƙungioyin da ke son ɗaukar Gilberto Mora na Club Tijuana da gaske. (Teamtalk)

Bournemouth ba ta niyar siyar da Alex Scott, a Janairu ba, duk da cewar Chelsea da Real Madrid na son dan wasan. (Talksport)

Real Madrid ta sa ido kan wasannin uku da scouted Scott ya buga, yayin da Liverpool, da Arsenal, da AC Milan suma ke harin dan wasan. (4-4-2.ch - in German)

Da alama dai Antonio Rudiger, 33, ya fara shirye shiryen barin Real Madrid a ƙarshen kakar wasannin nan, sakamakon rashin sabun ta wa ɗan wasan kwantaraginsa ba. (Sports Mole)

Tottenham za ta siyi ɗan wasan gaba a kakar siyen ƴan wasa a Janairu idan an buɗe kakar ƴan wasa sai dai basa son kashe kuɗaɗe masu yawa. (Football Insider)

Real Madrid da Barcelona sun shirya wajen taya dan wasan Manchester United JJ Gabriel, 15, kan albashi da ladan wasa inda suka siye shi a matsayin ɗan wasan mai zaman kansa. (Florian Plettenberg)

Har yanzu Bayern Munich bata fitar da rai ba wajen ɗauko Gabriel ba, sai dai basu da niyyar amince da albashi mai mataki bakwa da Manchester United ta sanya kan dan wasan. (Times - subscription required)

Bayern na sa ido kan mai tsaron ragar Newcastle Nza ta ƙare a kaka mai zuwa. (Football Insider)