KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Laraba 7 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Tsallake Bidiyo ka ci gaba
  • Hoton Jirgi
  • Sheikh Daurawa
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Kwamishinan yansandan Kano
  • Rabi'atu Runka
  • Hoto
  • Hoto
  • Yusuf Buhari
  • Mansura Isah
  • Tinubu da Shettima
  • Mahajjata
  • Taron UNGA
  • Mayakan Houthi
  • Wani da ya tsira daga hannun NSCDC ya bayyana mummunan halin da suka shiga a lokacin da suke tsare.
  • Abin da ya janyo mutuwar matasa 37 a Neja - Bago
  • Aisha Aliyu Ja'afar
  • Tsadar farashin mai

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba

  1. Mene ne ke ruruta wutar rikici a jam'iyyar APC a Kano?

    ..

    Jam'iyyar APC da ke mulki a Najeriya, na neman faɗawa cikin cikin gida a Jihar Kano da ke Arewacin ƙasar, ɗaya daga cikin jihohin da jam'iyyar ke fatan samun ƙuri'u maso yawa a zaɓen da ke tafe.

    Takun saƙa da gugar zana da kuma shaguɓe na neman dabaibaye siyasar jihar, ko da yake rikici ne da ake yi a cikin duhu.

    Rikici ne da yake neman girmama tsakamin mataimakin shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin da Ɗan Majalisar Tarayya na yankin Bichi, Abubakar Kabir Abba Bichi.

    Rahotanni sun ambato cewa, duk da cewa akwai wata jiƙaƙƙiya a ƙasa tsakanin jiga-jigan siyasar biyu, amma lamarin ya ƙara tsami ne bayan da mataimakin gwamnan jihar Murtala Sule Garo ya yi wasu kalamai masu kama da jirwaye da kamar wanka a wani taro da ya gudana a Bichi.

    Garo ya bayyana a wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake cewa duk wanda ya taɓa Abba Bichi sai ya ji su "ba a Bichi ba ko a Kabo ne".

    Wannan zance ya haifar da maida martani daga ɓangaren magoya bayan Sanata Barau Jibrin.

    A wani bidiyo na daban kuma an ga shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen Sanata Barau, Injiniya Rabi'u Sulaiman Bichi na mayar da martani cikin kan masu ingiza rikicin da yake tsakaninsa da Sanatan.

    Ku shiga nan domin karanta labarin.

  2. Dole Iran ta rage inganta Uranium ɗinta don kawo ƙarshen yaƙi - JD Vance

    ..

    Mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa Washington na ci gaba da tattaunawa da shugaban Iran da kuma ministan harkokin wajen ƙasar.

    Vance ya ce kawo ƙarshen yaƙin na buƙatar Iran ta rage yawan sinadarin uranium da take tacewa sosai, maimakon kawai ta yi alƙawarin rage shi nan gaba.

    A wata hira da Reuters bayan halartar taron yaƙin neman zaɓe na jam'iyyar Republican a Alaska, Vance ya ce Washington ba ta da tabbacin yadda Tehran za ta ɗauki matsaya a tattaunawar da ake yi kan shirinta na nukiliya.

    A cewar mataimakin shugaban Amurkan, babban makasudin yaƙin shi ne hana yaɗuwar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya.

    Vance ya kuma yi watsi da rade-radin cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2028, yana mai cewa a yanzu hankalinsa yana kan ganin jam'iyyar Republican ta yi nasara a zaɓukan tsakiyar wa'adi.

  3. An daƙile harin makami mai linzami da Houthi ta harba birnin Riyadh

    Ƙawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin da ake yi da mayaƙan Houthi a Yemen, ya ce sun dakile wani makami mai linzami da ƙungiyar, wadda Iran ke marawa baya, ta harba zuwa birnin Riyadh.

    Ƙungiyar Houthi ta ce ta kai hare-hare kan filayen jiragen sama biyu na Saudiyya da kuma wani sansanin sojin sama.

    Kazalika, ta ce ta kai hari kan filin jirgin saman birnin Aden da ke Yemen.

    Gwamnatin Yemen da ƙasashen duniya suka amince da ita, ta ce wani makami mai linzami ya faɗa kan titin saukar jiragen sama na filin jirgin, jim kaɗan kafin wani jirgin sama daga Masar ya sauka.

  4. An kwashe ma’aikatan jirgin ruwa 10 da suka jikkata a mashigar Hormuz

    Rundunar sojin saman Oman ta kwashe ma’aikatan wani jirgin dakon mai su 10 da suka jikkata, bayan da aka kai wa jirgin mai tutar Panama hari a mashigar Hormuz.

    A cewar Ma’aikatar Tsaron Oman, an kai wa jirgin ruwan mai suna On Peace hari ne ranar Talata, kimanin kilomita 17 daga tashar ruwan Lima da ke Oman.

    Harin ya haddasa gobara a saman jirgin.

    Ma’aikatar Tsaron Oman ta ce an kwashe ma’aikatan jirgin zuwa wani asibiti a Khasab, inda ake kula da su.

  5. Ana ci gaba da aikin gano gawawwakin sojin Najeriya 25 da suka mutu a hatsarin jirgi

    ..

    An ci gaba da zaman makoki na kwana uku a Najeriya bayan mutuwar mutum 25 a wani hatsarin jirgin sojin ƙasar. Tun daga ranar Litinin ake ci gaba da aikin gano jirgin da kuma gawarwakin waɗanda suka mutu.

    Hatsarin ya faru ne a Igbokoda, wani yanki mai ruwa da ke jihar Ondo, inda yanayin fadama ya sa isa wurin da jirgin ya faɗi ke da matuƙar wahala.

    Tawagar BBC da ta je wurin ba ta ga wata alama ta jirgin ko gawarwakin ba. Ana kyautata zaton cewa jirgin da gawarwakin sun nutse ne cikin fadamar.

    Sojoji sun kawo wata mota ta musamman domin taimakawa wajen fito da tarkacen jirgin.

    Sai dai kai kayan aikin daga titi har zuwa inda fadamar take ya kasance abu mai wahala. Rundunar sojin ta ce tana ƙoƙarin nemo hanyar da za ta kai ga wurin da jirgin ya faɗi.

    An hana ’yan jarida da mazauna yankin shiga cikin fadamar yayin da aikin ceto da fito da tarkacen ke gudana.

    Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa mutuwar mutanen ta girgiza su sosai, musamman ganin cewa waɗanda suka mutu jami’an soja ne da ke aikin kare ƙasar.

    Jirgin da hatsarin ya rutsa da shi samfurin ATR 42 ne, irin jirgin da wasu rundunonin soja ke amfani da shi wajen sintiri da sa ido a teku.

    Najeriya na dogaro da sintirin jiragen yaƙi a sama don lura da dogon gabar tekunta da ruwan da ke ƙarƙashin ikonta, da kuma tallafa wa ayyukan soji na yaƙi da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai.

    Rashin jirgin da ake amfani da shi wajen wannan aikin na iya janyo matsin lamba kan sauran jiragen rundunar, a daidai lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin tsaro a sassa daban-daban na ƙasar.

    Rundunar sojin saman Najeriyar na taka muhimmiyar rawa a ayyukan yaƙi da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da kuma sa ido kan iyakokin ƙasar da ruwanta.

  6. Messi ya buga wasansa na ƙarshe a tawagar Argentina

    ..

    Shahararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa na duniya, Lionel Messi, ya buga wasansa na ƙarshe a tawagar ƙasar Argentina.

    Messi ya ci kwallo daga bugun fenariti tare da taimakawa wajen zura sauran kwallaye biyu a wasan da Argentina ta doke Benin da ci 3-0 a wani filin wasa da ya cika maƙil da magoya baya a birnin Buenos Aires

    Da yake magana bayan wasan, Messi ya ce wakiltar Argentina ita ce mafi girman abin alfahari da zai iya samu a rayuwarsa ta wasanni.

    Tun da farko ya sanar da yin ritaya daga buga wa ƙasarsa wasa bayan Argentina ta sha kashi a hannun Spaniya a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya.

    Sai dai Messi ya ce zai ci gaba da taka leda a matakin ƙungiyoyi a ƙasar Amurka.

  7. Shekara uku da hare-haren Hamas na 7 ga Oktoban 2023 kan Isra'ila

    ...

    An yi shiru na tsawon minti guda a faɗin Isra’ila domin tunawa da cika shekaru uku da harin ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 1,100 a wani farmaki da ƙungiyar Hamas ta jagoranta daga Zirin Gaza.

    A yayin harin, an kuma yi garkuwa da mutum 251.

    Haka kuma ana gudanar da tarukan tunawa da waɗanda suka mutu a birane daban-daban na duniya.

    A martanin da Isra’ila ta mayar, sama da mutane 74,000 ne suka mutu a Gaza, yayin da hare-haren suka lalata manyan sassan Zirin Gaza da mayar da su kufai da baraguzan gine-gine.

  8. Matar da ta ƙi mutuwa bayan yi mata allurar kisa ta farfaɗo - Lauyoyinta

    Christa Pike

    Lauyoyin Christa Pike, Ba’amurkiyar da ta tsallake rijiya da baya bayan yunƙurin aiwatar da hukuncin kisa da ya ci tura a makon da ya gabata a kan ta, sun ce ta farfaɗo kuma tana iya magana.

    Sun ce tana karɓar kulawar likitoci na musamman, amma har yanzu hannayenta a daure suke duk da tana kwance a asibitin.

    Wakilin BBC ya ce har yanzu akwai tambayoyi da dama da ke buƙatar amsa a kan halin da ta ke ciki, to amma duk da haka sun ce samun sauƙinta sosai zai ɗauki lokaci.

    Lauyoyin sun sake kira da a sassauta hukuncin kisan da aka yanke mata.

    An dai yi yunƙurin yi mata allurar kisa har sau biyu, amma dukkan yunƙurin bai yi nasara ba.

  9. Assalamu alaikum

    Masu bin mu a wannan shafi barkan mu da safiyar wannan rana ta Laraba.

    Ku kasance da wannan shafi don sanin irin wainar da ake toyawa a sassan duniya, inda za mu fi mayar da hankali kan Najeriya da makwabtan ƙasashe.

    Kuna kuma iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawa a kan labaran da muke wallafawa.

    Ku biyo mu...