Real Madrid ta dage kan Quansah, Liverpool na sa ido kan Mora

Asalin hoton, Getty Image
Real Madrid na ci gaba da dagewa wajen ɗaukar ɗan wasan Bayern Leverkusen Jarell Quansah, da Arsenal ta yi wa wani babban tayi a kakar nan, sannan Chelsea na sha'awarsa. (Bild - in German)
Ɗan wasan Mexico Gilberto Mora, na cikin yan wasan da Liverpool ke bibiya sai dai Borussia Dortmund da Benfica suma na zawarcin ɗan wasan na Club Tijuana. (Teamtalk)
Ɗan wasan Barcelona Dani Olmo, na son ya yi riyata daga taka leda a Dinamo Zagreb. (Fichajes - in Spanish)
Ɗan wasan Canada Jonathan David, 26, ya fara wayar da kan Atletico Madrid da su mayar da kwantaragun sa na dan wasan aro ga Juventus, su siyar da shi ga Juventus kan Fam miliyan21. (Fichajes - in Spanish)
Inter Milan na son daukar ɗan wasan Alessandro Romano, da ke matsayin dan wasan aro a Calgliari daga Roma, idan har ɗan wasa Hakan Calhanoglu, ya yanke barin ƙungiyar a ƙarshen kwantaraginsa a kaka mai zuwa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Roma ta ga za yin nasara wajen ɗauka ɗan wasan Real Madrid Endrick, a matsayin aro, a kakar nan, sai dai suna son ɗaukar sa a watan janairu mai zuwa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Barcelona ta yi tuntuɓa kan ɗan wasan Croatia Josko Gvardiol a kakar da ta gabtaa, sai dai abun da bai futo fili ba shi ne ko dan wasan na son barin Manchester City. (Mundo Deportivo - in Spanish)
Barcelona da Inter Milan na sa ido kan dan wasan Stuttgart Finn Jeltsch, inda ɗan wasan na Jamus ɗin ke ɗaukar hankulan ƙungiyoyin da ke buga gasar ta Firimiya. (Sky Sports Germany)
Bologna ta amince da ɗaukar ɗan wasan Manchester United Matteo Darmian, a mastyin ɗan wasa mai zaman kansa, idan ɗan wasan na Italiyan ya bar Inter Milan, a ƙarshen kakkar wasannin. (Fabrizio Romano)



























