Man City ta amince da farashin Fernandez, Balde na son tafiya Man Utd

    • Marubuci, Muhammad Annur Muhammad
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
    • Aiko rahoto daga, BBC Hausa
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 2

Manchester City ta shirya biyan kudin da Chelsea ke nema domin sayen dan wasan tsakiya na Argentina, Enzo Fernandez, mai shekara 25. Chelsea na neman fam miliyan 120 kan dan wasan. (Football Insider)

Ana sa ran Liverpool da Brighton za su sake tattaunawa kan makomar dan wasan gefe na Gambia, Yankuba Minteh, mai shekara 22, yayin da Liverpool ke nazarin yiwuwar gabatar da tayi na uku. (Ben Jacobs via TeamTalk)

Dan wasan baya na hagu na Barcelona da Sifaniya, Alejandro Balde, mai shekara 22, ya amince wa wakilinsa Jorge Mendes ya fara tattaunawa kan yiwuwar komawarsa Manchester United. (Sport - in Spanish)

Aston Villa ta tuntubi kungiyar Club Brugge ta Belgium kan yiwuwar daukar dan bayan Ecuador, Joel Ordonez, mai shekara 22. (David Ornstein)

Brentford na shirin gabatar da sabon tayi na fam miliyan 37 domin sayen dan bayan Senegal na West Ham United, El Hadji Malick Diouf, mai shekara 21. (Football Insider)

Manchester United ta kuduri aniyar ba za ta sayar da dan wasanta na gaba na Netherlands, Joshua Zirkzee, mai shekara 25, a kan kasa da fam miliyan 40 ba. Juventus da Napoli da Aston Villa na cikin kungiyoyin da ake alakantawa da shi. (Sun)

Kocin Juventus, Luciano Spalletti, ya jaddada cewa kungiyar ba ta da niyyar sayar da dan wasan gaba na Turkiyya, Kenan Yildiz, mai shekara 21, ga Arsenal. (Metro)

Barcelona ta sa shakku a kan rahotannin da ke alakanta ta da neman dan bayan Portugal na Sporting, Goncalo Inacio, mai shekara 24, tana mai cewa babu wata yarjejeniya ko kuma wata tattaunawa da ta kusa kammala. (Fabrizio Romano)

Sai dai kocin Sporting, Rui Borges, bai yi watsi da yiwuwar Inacio ya koma Barcelona ko AC Milan ba, bayan da ya bar dan wasan daga cikin masu farawa a wasan da suka doke Alverca ranar Asabar. (Goal)

RB Leipzig ta cimma yarjejeniya ta baka da AC Milan kan dawo da dan wasan gaba na Faransa, Christopher Nkunku, mai shekara 28, a matsayin aro na kakar wasa guda tare da zabin sayensa a gaba. (Sky Sports Germany)