'Za mu lallashi 'yan takarar da aka sauya sunayensu'

Asalin hoton, APC
Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, ta tabbatar da sauya sunayen da dama daga cikin 'yan takararta inda ta maye gurbinsu da wadanda ta fi muradi.
Tuni dai APCn ta soma mika wa hukumar INEC sunayen 'yan takararta a matakai daban-daban.
Bayanai sun tabbatar da cewa APC ta tantance kimanin yantakara 2,500 da suka nemi kujeru daban-daban karkashin inuwarta.
Daraktan yada labarai na jam'iyyar, Malam Bala Ibrahim, ya shaida wa BBC cewa, tuni aka mikawa 'yan takarar da aka tace takardun shaidar takara, haka kuma ita ma hukumar INEC an mika mata nata sunayen domin ta fara wallafa a shafinta.
Ya ce," Ba wani abu bane sabo don an sauya sunan dan takara, dama idan aka ce an yi abu a wani wajen ba daidai ba, to adalci shi ne ya kamata ayi."
" Akwai kwamiti na sulhu da muka kafa da zai yi wa 'yan takarar da aka sauya sunayensu danne kirji ya lallashisu domin a nuna musu cewa tsari na dimokradiyya ba tsari ne da kowa ya ke samun abin da ya ke so ba." In ji.
Bala Ibrahim, ya ce," ''Muna sa ran duk wanda abun da za a yi bai masa dadi ba zai ci gaba da bayar da gudummawa da fatan idan an samu nasara za a iya waiwayar ka don ka ba da wata gudummawar, ƙila ma wadda za ta fi tasiri kan abun da kai ka so ka yi''
Tun da farko dai wasu 'ya'yan jam'iyyar sun bayyana rashin gamsuwa da abin da suka kira ci da karfin da APCn ta yi musu, duk kuwa da cewa su halastattun 'ya'yanta ne da suka bauta mata tsawon lokaci.
Kazalika ma, wasu daga cikin 'yan takarar APCn da aka sauya sunayensu, sun yi barazanar sauya sheka saboda rashin gamsuwa da abin da jam'iyyartasu ta yi.
Masana harkokin siyasa dai na ganin cewa duk lokacin da aka samu zargin sauya sunayen ƴan takara, akwai yiwuwar hakan ya haifar da matsaloli iri-iri.
Daga cikin irin waɗannan matsalolin akwai ƙarin ƙararraki a kotu, ƙorafe-ƙorafe ga shugabancin jam'iyya, da rashin gamsuwa daga magoya baya da kuma yiwuwar sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyu.
A wasu lokuta kuma, irin waɗannan saɓani kan shafi yadda jam'iyya ke gudanar da yaƙin neman zaɓe, musamman idan rikicin bai warware ba kafin fara kamfen.
Masanan sun kuma ce jam'iyya kan fi samun ƙarfi idan mambobinta sun amince da tsarin da aka bi wajen zaɓen ƴan takara, ko da kuwa ba kowa ne ya samu abin da yake so ba.












