Azumin Ramadan a Libya da bikin fitowar jagoran adawa a Senegal cikin hotunan Afrika

.
Bayanan hoto, Jama'a na zirga-zirga ƙarƙashin hasken fitilu masu siffar taurari, waɗanda aka rataye a titunan Tripoli babban birnin ƙasar Libya a watan Ramadan ranar Talata.
An wallafa
.
Bayanan hoto, A ranar ne kuma masu tseren kekuna suka kewaya yankin Winelands na Afrika ta Kudu.
.
Bayanan hoto, Wata yarinya ɗauke da biredi sa'o'i ƙalilan gabanin buɗe baki ranar Talata a ƙasar Senegal.
.
Bayanan hoto, A ranar Juma'a ne kuma magoya bayan jagoran Adawa a Senegal, Ousmane Sonko suka yi bikin fitowarsa daga kurkuku a titunan Dakar babban birnin ƙasar.
.
Bayanan hoto, Sheikh Mussa Ahmad Mabange a ƙofar wani Masallacin a birnin Goma da ke Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Congo ranar Laraba.
.
Bayanan hoto, ƙungiyar mawaƙan Black metal ya yin wata gasa a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya ranar Asabar.
.
Bayanan hoto, ƴankallo na amshi cikin farin ciki
.
Bayanan hoto, A ranar ne kuma, membobin ƙungiyar Chouyoukh Salatin Tarab daga Siriya suka gudanar da waƙoki da raye-raye a Tunisia