Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na 21/05/2026

Rahoto kai-tsaye

Nabeela Mukhtar Uba da Usman MINJIBIR

  1. Saliyo ta karɓi rukunin farko na ƴan Afirka da aka kora daga Amurka

    Saliyo ta zama ƙasa ta baya-bayan nan da ta karɓi ƴan ci rani na Afirka ta Yamma da aka kwaso daga Amurka.

    Wani jirgi ɗauke da ƴan ci rani tara har da maza bakwai da mata biyu daga Ghana da Senegal da Guinea da Najeriya sun isa birnin Freetown ranar Laraba.

    Saliyo ta amince ta karɓi ƴan ci-rani 300 duk shekara inda a kowane wata za a rika samun mutum 25 da za su isa ƙasar bisa yarjejeniyar tallafin dala miliyan 1.5 daga gwamnatin Amurka.

    Hukumomi sun bai wa mutanen wurin kwana na tsawon mako biyu kuma za su iya zama har tsawon kwana 30 domin bai wa hukumomi damar shirya mayar da su ƙasashensu na asali.

    Akasarin ƴan ci-ranin sun bayyana sha'awar zuwa gida. Amurka ta ƙulla makamanciyar yarjejeniyar da Ghana da sauran ƙasashen Afirka inda aka tusa ƙeyar baƙin duk da kotu ta umarci a basu kariya.

    Ma'aikatar harkokin wajen Saliyo ta ce ƙasar tana karɓar baƙi daga ƙasashe 12 mambobin ECOWAS da mutanen da ba a taɓa samun su da aikata miyagun laifuka ba.

    Su ma za a duba lafiyarsu sannan ma'aikatar bai wa ƴan ƙasashen ECOWAS damar zama na tsawon kwanaki 90.

  2. An kafa sabuwar Jam'iyyar Kyankyasai a Indiya

    Wata jam'iyyar barkwanci a Indiya mai suna Jam'iyyar Kyankyasai ta samu fiye da mabiya miliyan 15 a shafin Instagram.

    An kafa jam'iyyar ne bayan da ake zargin babban ministan shari'a na Indiya ya kwatanta matasan da ba su da aikin yi da kyankyasai da ƙwari.

    Daga baya ya yi ƙarin haske cewa yana magana ne kan masu digirin bogi.

    Ƙa'idojin zama mamba a jam'iyyar su ne zama cima zaune da rashin aikin yi da kuma shagala a shafukan intanet.

    Wani hoto da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Instagram don murnar nasarar da ta yi ya ce "A kwana huɗu kacal muka samu wannan nasara. A daina raina ƙarfin tasirin matasa".

  3. An jinkirta aikin kwashe ƴan Ghana daga Afirka ta Kudu

    Ma'aikatar harkokin waje ta Ghana ta jinkirta tashin jirgin da aka tsara kwashe ƴan ƙasar da ke Afirka ta Kudu sakamakon ƙaruwar zanga-zangar ƙyamar baƙin haure a Afirka ta Kudun.

    A wata sanarwa, ministan harkokin wajen Ghana Sam Okudzeto Ablakwa ya ce an ɗage shirin da wasu kwanaki saboda wasu dalilai.

    Hakan na zuwa ne sakamakon wasu rahotanni daga kafafen yaɗa labarai a Afirka ta Kudu da ke cewa ɗan Ghana guda aka gani ya je inda jirgin zai kwashi ƴan ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta ce 800 cikin jama'arta sun nuna sha'awar komawa gida, an samu ƙari ke nan daga 300 da aka samu a farkon makonnan.

    Ta ƙara da cewa an jinkirta tashin jirgin ne saboda adadin mutanen da aka samu sun ƙaru.

    Ma'aikatar ta kuma ce buƙatar a bi wasu ƙa'idoji na shari'a har da tantance fasinjoji na daga cikin dalilan da suka janyo tsaikon.

    Sai dai babu ƙarin bayani kan mutum nawa ne cikin 800 ɗin za su fice daga Afirka ta Kudu kaancewar kafafen yaɗa labaran ƙasar na ruwaito cewa babu fasinjoji a filin jirgin saman.

    Ana fargabar cewa zanga-zangar baya-bayan nan a sassan Afirka ta Kudu na iya janyo dawowar rikicin ƙyamar baƙi.

    A 2019, aƙalla mutum 12 aka kashe sannan a 2008, baƙi 62 ne suka mutu a hare-haren da aka kai kan baƙi a sassan ƙasar.

  4. Philippines ta ce tana farautar Ronald Dela Rosa

    Ma'aikatar shari'a a ƙasar Philippines ta ce ta fara farautar Sanatan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ke nema ruwa a jallo dangane tuhume-tuhumen da ke da alaƙa da yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi a ƙasar.

    Ronald Dela Rosa ya ɓace ne makon jiya bayan wani harbi da aka yi a zadai ya bayyana ne na wani dan lokaci don tabbatar da cewa wani abokin tsohon mai gidansa, Rodrigo Duterte, ya yi nasarar zama shugaban majalisar dattawan kasar.

    Ana zargin Mista Dela Rosa ne da haɗa baki da Mista Duterte wajen kashe wasu mutum talatin da biyu masu ta'ammali da miyagun kwayoyi.

    Tuni dai aka riga aka cika hannu da Mista Duterte wanda ay ke tsare a halin yanzu.

  5. Columbia ta kori jakadan Bolivia

    Colombia ta kori jakadan Bolivia a wani mataki na sa-in-sa na diflomasiyya, sa'o'i kadan bayan da aka nemi ita ma jakadanta ya bar Bolivia.

    Takaddamar diflomasiyya ta samo asali ne daga kalaman shugaban Colombia Gustavo Petro na cewa zanga-zangar da aka yi a Bolivia na adawa da shugaba Rodrigo Paz ta yi nuni da rashin da farin jininsa.

    Shugaban na Bolivia ya bayana kalaman takwaransa na Colombia a matsayin katsalandan a cikin al'amuran kasarsa.

    Ana zaman dar-dar a Bolivia inda zanga-zangar da ake yi kan tsadar rayuwa ta ta rikide ta zama ta adawa da gwamnatin Mr Paz a fadin kasar.

  6. Tinubu ya nada ɗan shekara 39 a matsayin shugaban JAMB

    Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Farfesa Segun Aina a matsayin sabon shugaban hukumar da ke tsara jarrabawar shiga jami'a, JAMB.

    Aina wanda shekarunsa 39 ya maye gurbin Farfesa Is-haq Oloyede wanda wa'adinsa ke ƙarewa ranar 31 ga watan Yulin 2026.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya bayyana Aina a matsayin fitaccen masanin kuma ƙwararre da yake da gogayya a harkokin jarrabawa da intanet da kuma sauye-sauye a abubuwan da suka shafi al'umma.

  7. Ƙungiyar agaji ta zargi sojojin Isra'ila da azabtarwa

    Wata ƙungiyar ba da agaji ta Falasdinawa ta ce masu fafutuka da aka tsare daga wani jerin gwanon jiragen ruwan Gaza sun zargi sojojin Isra'ila da cin zarafi da kuma azabtarwa.

    An kai mutum uku daga cikinsu asibiti, ko da yake a halin yaznu an sallame su. Tun da farko dai Ministan Tsaron Isra'ila Itamar Ben Gvir ya sha suka bayan ya fitar da wani bidiyo inda ya ke yi wa masu fafutukar izgili yayin da ake tsare da su.

    Bidiyo ne na tsawon dakika talatin da takwas da ya nuna jerin wadanda aka tsare suna zaune a kasa a daure yayin da Ben Gvir ya ke musu dariya yana cewa maraba da zuwa Isra'ila mu ne masu iko a nan.

    Firaminista Benjamin Netanyahu ya ce abin da ministan aikata ya ci karo da dabi'un isra'ila.

  8. Al'ummar Diffa a Nijar na fuskantar barazanar ƙarancin abinci

    Manoma a jahar Diffa da ke jamhuriyar Nijar sun koka kan fuskantar wasu matsaloli guda da ke barazana ga samar da abinci a yankin.

    Manyan matsalolin da suke ci musu tuwo a kwarya sun haɗa da rashin tsaro da ke da alaƙa da ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai, da sauyin yanayi, da hare-haren da kwari ke kai wa muhimman amfanin gona, lamarin da ya haifar da karancin albarkatun noma a kasuwanni.

    Tuni dai manoman suka koka da matsalar suna masu cewa lamarin ya jefa su cikin halin ha'u'la'i.

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da damuna ke ƙara ƙaratowa sannan kuma ake ta gyare-gyaren gonaki.

  9. Ana cece-kuce tsakanin Atiku da Amaechi kan takarar shugaban ƙasa a ADC

    A Najeriya takaddama ta kaure tsakanin manyan masu neman takarar shugabancin kasar a jama'iyyar ADC Rotimi Amaechi da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Atiku Abubakar.

    An dai jiyo wasu kalamai daga bakin Amaechin, inda ya ce Atiku Abubakar ba mutum ne da zai iya lashe zaɓe ba, ko da kuwa ya samu takara a jama'iyyar.

    Amaechi ya kafa hujja da zaɓukan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya tsaya a baya, kuma ya sha kaye, yana mai cewa a yanzu kamata ya yi jam’iyyarsu ta mayar da hankali ga wanda jama’a za su iya zaɓa, ba wanda ya saɓa takara ba.

    Sai dai kuma ɓangaren Atiku sun ce Kalaman na Amaechi na "tsoro ne" saboda sun san cewa Atiku ya fi ƙarfinsu sannan zai fi samun karɓuwa daga yan Najeriya.

    Tsohon mataimakin shugaban na Najeriya, Atiku Abubakar dai ya yi takarar shugaban ƙasa karo na huɗu kuma idan ya samu takarar a 2027, hakan zai kasance takararsa ta biyar kenan.

  10. Ƴan Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma gida

    A ranar Alhamis ɗin nan ne wata tawagar 'yan ci-rani 'yan asalin ƙasar Ghana da ke Afirka ta Kudu za su koma ƙasarsu.

    Suna tserewa ne daga zanga-zangar ƙin jinin baƙi a biranen Afirka ta Kudu, inda masu zanga-zangar ke zargin baƙi da asassa matsalar tabarbarewar tattalin arziki

    Gwamnatin Ghana dai ta ce yan kasarta guda dari uku ne da ke Afrika ta kudu suka mika bukatar komawa gida, masu zanga-zangar suna zargin bakin haure ne da ta'azzara matsalar karancin albashi da rashin aikin yi.

    Najeriya ma ta ce sama da ƴan kasarta 100 ne suka nemi a mayar da su gida. A na ta bangaren Gwamnatin Afirka ta Kudu ta yi Allah-wadai da duk wani cin zarafi da ake kai wa ƴan kasashen waje.

  11. Shugaban Cuba ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa Raul Castro

    Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi watsi da tuhumar da Amurka ta yi wa magabacinsa Raul Castro a matsayin bi-ta-da-ƙullin siyasa.

    Zarge-zargen da a ke yi wa tsohon shugaban na Cuba mai shekara 94 sun samo asali ne daga wani lamari da ya faru a shekarar 1996 inda jiragen yakin Cuban suka harbo jiragen sama guda biyu da wata kungiyar yan sa kai ta 'yan gudun hijirar Cuban ke amfani da su.

    Ana tuhumar Raul Castro da laifuffuka hudu na kisan kai, amma manazarta sun ce wani yunkuri ne na Washington na tabbatar da sauyin gwamnati a Havana.

    Takunkuman da Amurka ta kakabawa tsibirin ya durkusar da tattalin arzikinsa baki daya.

    Shugaba Trump ya bayyana tuhumar a matsayin lamari mai cike da tarihi amma ya yi watsi da yiwuwar daukar matakin soji

  12. Ana samun hauhawar hannun jari a Asia saboda tsagaita yakin Iran

    An sami hauhawar darajar hannun jari a kasuwannin Asiya, sakamakon bunƙasar kamfanonin fasaha da fatan da ake da shi cewa nan ba da jimawa ba za a warware rikicin Gabas ta Tsakiya.

    Kasuwar Nikkei ta Japan ta tashi da sama da kashi uku cikin ɗari, yayin da hannayen jarin kamfanonin Koriya ta Kudu suka tashi da kusan kashi biyar cikin ɗari.

    Muhimmin cigaban da aka samu a kamfanin kera-keren fasaha na Amurka , (Nvidia), da shawarar da ma'aikatan Samsung suka yanke na kin shiga yajin aiki, da shirin da ake yi na sayar da hannayen jari a kamfanonin SpaceX da OpenAI sun taimaka wurin bunkasa darajar hannayen jarin kamfanonin fasaha.

  13. Muna ƙoƙarin samun maganin cutar Ebola - Jami'in Amurka

    Wani jami'in ma'aikatar lafiya ta Amurka ya ce wata hukumar gwamnati tana aiki tare da wani ƙaramin kamfanin sarrafa magunguna don sarrafa wani maganin gwaji na cutar Ebola.

    Asali dai an kirkiri maganin ne domin yaki da wani na'uin cutar amma bayan gwaje-gwaje sun nuna cewa zai iya yin tasiri a kan nau'in Bundibugyo wanda a halin yanzu ake fama da shi a gabashin Kongo.

    Wani jami'in hukumar lafiya ta duniya, ya ce ana kuma nazari kan wata allurar rigakafi ta daban.

    Ya ce "Wancan wani aikin hadin gwiwa ne tsakanin jami'ar Oxford da cibiyar sarrafa maguguna ta India, kuma ana kan sarrfata a halin yanzu amma babu isasun bayanai a kan tasirinta".

    Sama da mutane 130 ne ake tunanin cutar ta kashe a gabashin Kongo, inda ake zargin mutane 600 sun kamu da cutar a lardin Ituri mai iyaka da Uganda da Sudan ta Kudu.

  14. Kamfanin SpaceX na Elon Musk na son tallata hajarsa a kasuwar Nasdaq

    Kamfanin SpaceX na Elon Musk ya gabatar da takarda a hukumance a gaban masu kula da harkokin kuɗi na Amurka don neman izinin tallata hannun jarinsa a kasuwar hada-hadar hannayen jari ta Nasdaq.

    Yana daya daga cikin tallar hannun jari da ya fi jan hankali a tarihi, kuma kamfanin yana shirin zama kamfani na farko da zai fara kasuwancin hannun jari da darajar dala trillian ɗaya.

    Wakiliyar BBC ta ce Ko da bayan siyar da hannayen jarin, ana sa ran Elon Musk zai ci gaba da kasancewa mai cikakken iko, har yanzu dai kamfanin bai bayyana adadin hannun jarin da yake shirin sayarwa ba da kuma a kan wani farashi.

    Takardun da kamfanin ya gabatar sun tabbatar da cewa SpaceX yanzu ya kunshi kamfanin kirkirarriyar basira na Elon Musk (XAI), da kuma dandalin sada zumunta na X wanda a baya aka sani da Twitter

  15. Iran ta ce tana yin duban tsanaki kan sabbin buƙatun Amurka

    Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce tana nazari kan sabbin shawarwarin da Amurka ta gabatar kan kawo ƙarshen yaƙin da take da Iran ɗin.

    Ana tunanin Pakistan ce ta gabatar da sabon daftarin ga shugabancin Iran, bayan ministan harkokin wajenta ya ziyarci Tehran a jiya Laraba.

    Shugaba Trump ya ce zai jira na kwanaki domin samun martanin Iran, amma ya sake yin barazanar ɗaukar matakin soji idan har Iran ba ta amince da daftarin ba.

    Tehran ta ɗauki wani mataki na ƙara tabbatar da ikonta a mashigar Hormuz inda ta buƙaci jiragen ruwa su yi aiki tare da wata sabuwar hukumar kula da mashigar da aka ƙirƙira.

  16. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiya da fatan kun wayi gari lafiya. Yau Alhamis, kuma kamar kowace rana mun dawo domin ci gaba a inda muka tsaya a shafinmu na kai tsaye da ke kawo muku wainar da ake toyawa dangane da yaƙin da Amurka da Isra'ila ke yi da ƙasar Iran.

    Har wayau, shafin yana kuma kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da ma sauran sassan duniya.