Da gaske ne Tinubu zai rusa shari'ar musulunci a Najeriya?

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Asalin hoton, Facebook/Tinubu

Bayanan hoto, Shugaba Bola Ahmed Tinubu
An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Fadar shugaban Nijeriya ta musanta wani labari da ta ce na jabu ne, da ya yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu na yunƙurin yi wa tsarin mulkin Nijeriya gyaran fuska domin sauya sunan ƙasar da kuma rusa dokar shari'ar Musulunci.

Ta ce labarin wanda aka wallafa ba tare da ambatar majiyarsa ba, wani ɓangare ne maƙarƙashiyar wasu ƴan siyasa da idonsu ya rufe a ƙoƙarinsu na haddasa ƙiyayya da janyo rikicin siyasa da tunzuri gabanin babban zaɓen 2027.

Labarin dai ya bayyana ne a shafukan sada zumunta a makonnin da suka gabata kuma ya sake bayana a baya baya nan.

Abdul'aziz Abdul'ziz, mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya ya shaidawa BBC cewa an shirya labarin ƙarya ne domin shafawa shugaba Bola Ahmed Tinubu kashin kaji

''Mun ga labarin ƙarya yana yawo, kuma wani labari ne mara tushe akan cewa shugaban ƙasa zai kawo wasu sauye-sauye waɗanda su ka haɗa da hana shariar musulunci a wasu jihohi na arewacin ƙasar, da kuma canza wa ƙasar suna''

''Wannan magana ba haka take ba, kuma shi yasa mu ka fitar da wannan sanarwa domin ƙaryata wannan labari mara hujja, wanda dama an shirya shi ne domin kawo ce-ce ku -ce mara kyau tare da gogawa shi shugaban kasa kashin kaji'', in ji shi

Gwamnatin Nijeriya ta yi kira ga ƴan ƙasar da su yi watsi da labarin gaba ɗayansa saboda a cewarta masu yaɗa labarin bogin dillalai ne na kawo hargitsi da tashin-tashina.

Abdulaziz Abdulaziz ya kuma ce labarin na da alaƙa da siyasa

''Yanzu lokacin siyasa ne, ƴan adawa ba bu abinda ba za su iya ba , ba za mu iya cewa su waye suka haɗa wannan manaƙisa ba, domin sun yi ne a ɓoye''

''Amma dai aiki ne na waɗanda za a iya cewa maƙiya ko ƴan adawa ne waɗanda suna ƙoƙarin su ɓata sunan gwamnati da shugaban ƙasa'' in ji shi