Ƙasashe bakwai da suka fi fama da ƙarancin ruwan sama a duniya

s

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 6

Damina ta fara sauka a wasu sassan Najeriya da ƙasashen yammacin Afirka, inda mutane ke shirin komawa gona.

Hukumomin hasashen yanayi a Najeriya da Jamhuriyar Nijar sun yi gargaɗi game da yiwuwar samun ambaliya musamman a farko-farkon damina.

A shekarun baya akan samu munanan ambaliya da ke haifar da asarar rayuka da dukiya.

A gabashin Afirka ma yanzu haka ƙasashe da dama na fuskantar mamakon ruwan sama bayan faɗuwar damina a watan Maris.

To sai dai yayin da wasu ƙasashe ke samun isasshen ruwan sama, ko ma ruwan sama fiye da kima a duk shekara, akwai ƙasashen da ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da suke fuskanta shi ne rashin samun ruwan sama baki ɗaya.

Wasu al'umma kan shafe tsawon rayuwarsu ba tare da ganin an yi ruwan sama mai ƙarfi ba a garuruwansu.

A irin waɗannan ƙasashe ruwan sama na da matuƙar daraja, tamkar zinare.

Ala tilas irin waɗannan ƙasashe ke nemo wasu dabarun zamani domin samar da ruwa mai tsafta na amfanin yau da kullum, ciki har da amfani da fasahar zamani wajen cure giragizai wuri ɗaya domin samun ruwan sama.

Masana sun ce yawancin ƙasashen da ke fama da irin wannan yanayi na ƙarancin ruwan sama suna a yankuna ne na rairayin hamada, kamar Sahara a Afirka da kuma yankunan rairayi na Gabas ta Tsakiya.

Yanayin waɗannan yankuna na hana haɗuwar isasshen hadarin da zai iya samar da ruwan sama a tsawon shekara.

Wannan labarin ya duba ƙasashe bakwai waɗanda suka fi fama da ƙarancin ruwa a duk shekara.

Jerin ƙasashen ya dogara ne kan gwargwadon yawan ruwan sama da ƙasa ke samu a kowace shekara, kamar yadda aka yi nazari a tsawon shekaru.

Ana auna yawan ruwan sama ne ta hanyar amfani da wani gwangwani da ake kira 'rain gauge' a turance domin gwada yawan ruwan sama da ke faɗuwa a gari ko ƙasa tsawon lokaci.

7. Jordan

s

Asalin hoton, Getty Images

Jordan na cikin ƙasashen da suka fi fama da ƙamfar ruwan sama a doron ƙasa. Ƙasar na samun kimanin milimita 111 na ruwan sama a ma'auni, duk shekara, wanda hakan ya yi ƙaranci sosai idan aka kwatanta da gwargwadon ruwan sama da sauran ƙasashen duniya ke samu.

Akasarin ƙasar Jordan na da yanayi ne na rairayin hamada, inda wasu wuraren ke fama da tsananin zafi da ƙamfar ruwan sama na lokaci mai tsawo.

Ana samun ruwan sama ne a wani ɗan lokaci ƙalilan a lokacin hunturu.

Ƙaruwar al'umma da kuma ƴan gudun hijira da ke kwarar cikin ƙasar daga ƙasashe masu maƙwaftaka na tsananta matsalar ƙarancin ruwa a ƙasar.

A sanadiyyar haka ne gwamnati ke kashe miliyoyin daloli wajen alkinta ruwa da bunƙasa hanyoyin noman rani na zamani domin sassauta illar fari.

6. Namibia

s

Asalin hoton, Getty Images

Namibia ma na cikin ƙasashe mafiya ƙamfar ruwa a nahiyar Afirka. Ƙasar na samun ruwan sama da ya kai yawan milimita 85 a shekara.

Ƙasar ce ke da rairayin hamadar Namib Desert, wadda aka bayyana a matsayin mafi daɗewa a duniya.

Akwai wasu yankunan ƙasar da ke shafe shekaru masu yawa ba tare da samun ruwan sama ba.

Sai dai duk da farin da ƙasar ke fama da shi ta samu damar bunƙasa harkar yawon buɗe ido sanadiyyar rairayin hamada da kuma dabbobin daji da take da su.

Amma samun ruwa babban ƙalubale ne ga al'umma da dama na ƙasar, musamman a yankunan karkara.

Haka kuma sauyin yanayi na ci gaba da haifar da damuwa kan yiwuwar ƙazancewar fari, wanda hakan matsala ce ga harkar noma da kiwon dabbobi, waɗanda fannoni ne da al'umma da dama suka dogara da su wajen rayuwa.

5. Qatar

s

Asalin hoton, Getty Images

Qatar na daga cikin ƙasashe mafi ƙanƙanta a duniya, kuma ɗaya daga cikin wadanda ba sa samun ruwan sama sosai.

Ƙasar na samun ruwan sama ne da ya kai milimita 74 a shekara.

A mafi yawan lokuta akan samu ruwan sama ne a ƙasar a lokacin sanyi, amma a lokacin zafi akan yi fama da zafi mai tsanani.

Sanadiyyar rashin kogi ko tafkuna, ƙasar ta dogara ne ga fasahar zamani ta tace gishiri daga ruwan teku domin samar da ruwan sha da na amfanin al'umma.

Ƙaruwar yawan al'umma da ci gaban zamani ya sanya ƙasar ta zama a sahun gaba cikin jerin ƙasashen da ke amfani da fasahar zamani wajen samar da ruwa ga al'umma.

4. Saudiyya

s

Asalin hoton, Getty Images

Saudiyya na cikin ƙasashen da suka fi samun fari a doron ƙasa. A mafi yawan yankunan ƙasar ana samun ruwan sama kimanin milimita 59 ne a shekara.

Kasancewar ƙasar ba ta da rafuka, ta dogara ne kan ruwan ƙarƙashin ƙasa da kuma tace ruwan teku wajen samar da ruwan amfanin yau da kullum.

Haka nan ƙasar ta zuba biliyoyin daloli kan fasahar inganta ruwa.

Duk da wannan ƙalubale Saudiyya ta ci gaba da gina manyan birane da haɓɓaka masana'antu a faɗin ƙasar.

3. Algeria

s

Asalin hoton, Getty Images

Algeria ce ƙasa mafi yawan faɗin ƙasa a Afirka, sai dai akasarin ƙasar na mamaye ne da hamadar Sahara.

A mafi yawan yankunan ƙasar akan samu ruwan sama ne kimanin milimita 89 a shekara.

Ƙarancin ruwa ya sanya babu mutane sosai a yankuna da dama na kudancin ƙasar.

Fari ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da ke fuskantar ɓangaren noma, musamman sanadiyyar raguwar hanyoyin samun ruwa da kuma ƙaruwar yanayin zafi.

Sai dai duk da wannan hali ƙasar na ci gaba da dogaro sosai da ɗanyen man fetur da gas a matsayin ginshiƙin tattalin arziƙinta.

2. Libya

s

Asalin hoton, Getty Images

Libya na cikin ƙasashe mafiya fama da ƙarancin ruwa a duniya, inda take samun kimanin milimita 56 na ruwan sama a duk shekara.

Sama da kashi 90% na faɗin ƙasar na cikin hamadar Sahara, kuma a wasu yankunan ƙasar masu nisa cikin hamadar Sahara akan samu ruwan sama ne sau ɗaya kacal a cikin tsawon shekaru.

Ƙarancin ruwa da ƙasar ke fama da shi ya sanya ƙasar ta samar da manyan ayyukan samar da ruwa a biranen ƙasar.

Masana na hasashen cewa ɗumamar duniya za ta ƙara munana matsalar ruwa a ƙasar ta arewacin Afirka.

1. Masar

s

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Masar na daga cikin ƙasashe mafiya ƙarancin ruwan sama a duniya, inda take samun kimanin milimita 18 na ruwan sama a shekara.

Mafi yanan ƙasar rairayin hamada ne, inda mutane suka fi yin rayuwa a gaɓar kogin Nilu.

Kogin Nilu ne babbar hanyar samun abincin al'umma sama da miliyan 100 na ƙasar.

Da ƙyar a samu ruwan sama a wasu biranen ƙasar, wanda hakan ya sanya hatta gine-ginen ƙasar ba a tsara su ta yadda za su jure wa ruwan sama mai ƙarfi ba.

Sanadiyyar dogaron da ƙasar ke yi kan Kogin Nilu ne ya sanya duk wata barazana ga ruwan kogin yake zama mai matuƙar muhimmanci ga al'umma da hukumomin ƙasar.

Wannan labari ya tattaro bayaninsa ne daga hukumomi kamar: NASA, Alƙaluman yanayi na MDD, da sauran su.