Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Yadda na riƙa wanke kaina da ɗanyen ƙwai domin neman haihuwa'
- Marubuci, Helen Richardson
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, North East and Cumbria
- Lokacin karatu: Minti 3
Lokacin da take fafutikar neman samun ciki, Barbora Gray, ta tuno yadda ta riƙa wanke gashin kanta da ɗanyen ƙwai bayan ganin wani abu da aka wallafa a shafin sada zumunta.
"Da farko, na shiga shafukan sada zumunta ne cikin zaƙuwar neman mafita" in ji ta.
"Wannan abu ne mai hatsari".
"Na fara abin ne a hankali, amma sai ga shi ina yarda da komai, tun daga abin da nake amfani da shi wajen wanke gashin kaina da kuma sabulun da nake amfani da shi wajen wanke kwanonin cin abinci."
Matar mai shekara 35 a duniya da ke zaune a garin Hebburn da ke yankin South Tyneside na ƙasar Birtaniya, a yanzu ta fara yin wani shiri na yaƙi da bayanan ƙarya kan lafiyar mata.
Shirin nata na mayar da hankali kan ɗaukewar jinin al'adar mata, da lafiyar ƙwaƙwalwa, da abubuwan da suka shafi al'adar wata-wata da neman haihuwa da kuma samar wa matan yankin da take wata dama da tattauna damuwoyinsu domin neman mafitar da ta dace.
Matar, wadda a yanzu take da ƴaƴa na fatan cewa shirin nata mai suna 'She Thrives' zai "kawo sauyi kan yadda mata ke tattaunawa game da lafiyarsu".
Ta ce ta samu ƙwarin gwiwar yin wani abu da zai kawo sauyi ne bayan karanta rahoto mai taken Matar Arewa (Woman of the North), wanda cibiyar nazari kan lafiyar mata ta Health Equity North ta fitar a shekarar 2024.
Rahoton ya gano cewa mata a arewacin Birtaniya sun fi yin ayyuka na lokaci mafi tsawo, sun fi shiga hatsarin kamuwa da rashin lafiya sannan sun fi shiga hatsarin fuskantar cin zarafi a cikin gidaje, fiye da sauran mata na yankunan ƙasar.
Barbora, wadda ke aiki a sashen bayanai kan kiwon lafiya, ta ce "ta san cewa akwai mutanen da za su iya samar da maslaha" kan matsalolin.
Shirin nata na samun goyon bayan Hukumar Lafiya ta Birtaniya ta yankin Arewa maso Gabas da kuma Areacin Cambria, da kuma gidauniyar Northern Health Science Alliance da kuma wasu gidauniyoyin da dama.
Haka nan akwai ƙungiyoyin masana lafiya da dama da ke tallafa wa shirin, wadanda suka damu da irin bayanai masu rauni da mata ke cin karo da su a shafukan sada zumunta game da kiwon lafiya.
Dakta Katherine Gilmore, babbar likitar mata da abubuwan da suka shafi jima'a a gidaauniyar kula da lafiya ta South Tyneside and Sunderland ta ce tana samun marasa lafiya "a kodayaushe" waɗanda suka ci karo da bayanan lafiya na ƙarya.
"Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke hana mata kula da lafiyarsu shi ne rashin lokaci," in ji ta. Ta ƙara da cewa "Saboda haka shafukan sada zumunta ne wuri mafi sauƙi da suke bibiya."
Sai dai ta ce babbar matsalar ita ce akwai bayanan ƙarya.
"Za ka iya gane waɗanda suke da sahihan bayanai kan kiwon lafiya, haka nan kuma za ka iya gane wadanda suka ci karo da labaran ƙanzon-kurege. Wannan abin damuwa ne sosai."
A yanzu mutanen yankin Arewa maso Gabas sun yi maraba da shirin na 'She Thrives'.
"A lokacin da nake cikin damuwa, babu wani shiri kaman wannan," in ji Kate Scott, wadda ke zaune a garin Hebburn. "Abin da Barbora ke yi zai taimaka wa ƴata da jikokina a nan gaba."
Ita ma Sarah McEwan daga garin Jarrow, tana goyon baya.
"Mata na aiki tuƙuru, wajen kula da iyali, da ayyuka a koda yaushe, saboda haka akwai buƙatar mu riƙa kulawa da kanmu," in ji ta.