Hanyoyin ruwa guda 8 masu muhimmanci a duniya

    • Marubuci, Walid Badran
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 7

Mashigar tekuna da hanyoyin ruwa na da matuƙar muhimmanci ga fannin kasuwanci da alaƙar ƙasa da ƙasa a duniya. Ta waɗannan hanyoyin ne jiragen ruwa da dama ke zirga-zirga, musamman na makamashi tsakanin nahiyoyi.

Saboda yawan dogaro da ake yi da hanyoyin ruwa wajen kasuwanci da safarar kayayyaki, shi ya sa tasirin waɗannan hanyoyin ya ƙaru, la'akari da muhimmancinsu ga tattalin arzikin duniya.

Waɗannan hanyoyin ruwan suna taka muhimmiyar rawa wajen haɗa tekuna da dama, kuma suna rage tazarar tafiya da kuma kashe kuɗi. A madadin shataletale a tsakanin nahiyoyi, waɗannan mashigar ruwan da ƙananan hanyoyin yanke suna taimakawa wajen rage farashin kayayyaki, saboda sauƙin safararsu.

Shi ya sa duk wani tsaiko da za a samu a waɗannan hanyoyin ruwan, zai iya kawo babban tsaiko ga kasuwannin duniya.

Muhimmancin waɗannan hanyoyin ba ga iya tattalin arziki ya tsaya ba, suna nuna ƙarfin ikon siyasa da na soji, kuma an sha yin yaƙe-yaƙe saboda waɗannan hanyoyin.

Mashigin Hormuz

Mashigin Hormuz da ke tsakanin Iran da Daular Oman na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin teku a duniya saboda yanayin wurin da ya haɗa Tekun Fasha da Tekun Indiya. Wannan yanki yana da mahimmanci wajen jigilar jiragen ruwa daga ƙasashen Gulf zuwa kasuwannin duniya.

Muhimmancin hanyar na da alaƙa da yadda sama da kashi 20 cikin 100 na albarkatun mai a duniya ke wucewa ta cikinsa. Kuma duk wani cikas da ya faru zai iya haifar da matsala ga farashin mai a duniya.

A baya-bayan nan ne Dakarun juyin juya halin Musulunci na Iran suka sanar da rufe mashigar ruwan, musamman ga waɗanda ke da alaƙa da Amurka da Isra'ila, a matsayin martani kan hare-haren soji da suke kaiwa kan Iran da aka fara a watan Fabrairun 2026.

Mashigin ruwan Suez

Mashigin ruwa na Suez da ke Masar na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin ruwa a duniya, domin ya haɗa tekun Bahar Maliya da Tekun Mediterrenean, kuma shi ne mashigin tekun da ke tsakanin Turai da Asiya ba tare da ya zagaya nahiyar Afirka ba.

Mashigin na taka muhimmiyar rawa a harkokin kasuwancin ƙasa da ƙasa, musamman jigilar man fetur da iskar gas, kuma babbar hanyar samun kuɗaɗen shiga ne ga Masar.

An fara aikin mashigar ruwa ta Suez ne a shekarar 1859 a lokacin mulkin gwamnan Masar, Said Pasha, wanda ya ba da izinin aikin tonon, ga wani kamfanin Faransa ƙarƙashin jagorancin Ferdinand de Lesseps.

An gudanar da aikin na tsawon shekaru kusan 10 inda a 17 ga watan Nuwamban shekarar 1869 aka bude mashigar a hukumance, a lokacin mulkin Khedive Ismail, a wani babban bikin da ya haɗa tekun Bahar Maliya da Bahar Rum.

Matakin da shugaban ƙasar Masar Gamal Abdel Nasser ya dauka a shekara ta 1956 na mayar da magudanar ruwa ƙarƙashin ikon ƙasar, ya kai ga an ƙaddamar da mamaya kan Masar a shekarar 1956, inda Biritaniya, Faransa da Isra'ila suka shiga, a ƙoƙarinu na sarrafa magudanar ruwan.

Rikicin ya zo ƙarhe ne bayan janyewar sojojin Isra'ila, Birtaniya, da Faransa bayan matsin lamba daga ƙasashen duniya, yayin da magudanar ruwar ke ci gaba da kasancewa ƙarkashin ikon Masar.

Daga baya aka rufe magudanar ruwar saboda rikicin Larabawa da Isra'ila, a lokacin yaƙin 1967, kuma ya kasance a rufe tsawon shekaru, kafin a sake buɗe shi a shekarar 1975 bayan kawo karshen yaƙin a watan Oktoban 1973.

Bab el-Mandeb

Mashigin Bab el-Mandeb ya haɗu da tekun Maliya da Tekun Aden, kuma yana tsakanin Yemen, Djibouti, da Eritrea ne. Nan ce hanyar kudanci zuwa mashigin Suez, kuma tana da matuƙar mahimmanci a kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Ta nan ne yawancin jiragen ruwa da ke tafiya tsakanin Asiya da Turai ke wucewa, abin da ya sa ya zama hanyar sufuri mai mahimmanci a duniya.

Sai dai wannan mashigar na fuskantar ƙalubalen tsaro saboda tashe-tashen hankula a yankin Afirka da Yemen, lamarin da ke ƙara jefa shi cikin haɗari. Don haka ƙasashe masu karfin faɗa a ji a duniya suna ƙoƙarin ganin wajen ya kasance a buɗe a ko da yaushe.

A baya dai, barazanar da 'yan Houthi a Yemen, ƙawayen Iran suka yi, ya haifar da cikas ga harkokin sufurin jiragen ruwa da kuma ƙarin kuɗin haraji a kan ruwa.

Dangane da wannan barazanar, ƙasashen Turai da dama sun ƙiƙiro rundunar sojin ruwa ta ƙasa da ƙasa da aka kira da Operation Aspidis, da nufin kare jigilar kayayyaki da tabbatar da 'yancin zirga-zirga a tekun Maliya da Bab al-Mandab.

Ayyukansu sun haɗa da raka jiragen ruwa, da sa ido da kuma mayar da martani ga duk wata barazana a ruwan, ta yadda za a inganta tsaron wannan yanki mai muhimmanci da kuma rage duk wata illa da za ta haifar da tarnaƙi ga kasuwancin ƙasa da ƙasa.

Mashigin Gibraltar

Mashigin Gibraltar yana tsakanin arewacin Maroko da kudancin Sifaniya ne, sai kuma yankin Gibraltar da Birtaniyya ke iko da shi ta bangaren Turai, wanda ke ba Birtaniya damar kasancewa masu iko da wannan muhimmiyar hanyar tekun da ta hada Tekun Bahar Rum da Tekun Atlantika.

Yana da muhimmanci ne saboda kasancewarsa babbar hanyar jigilar kayayyaki tsakanin Turai, Afirka da Amurka, inda ta kasance cibiyar kasuwancin kasa da kasa, da kuma bayar da gudummawar hada kasuwanni da dama ta hanyar teku guda ɗaya.

Mashigin kuma na da muhimmanci na soji da siyasa, saboda kusancinsa da nahiyar Turai. Daga cikin manyan tashe-tashen hankulan da aka gani akwai wadanda suka shafi gwagwarmayar mulkin mallaka na tsawon shekaru aru-aru tsakanin manyan ƙasashen Turai musamman Ingila da Sifaniya.

Ana samu ɗan saɓani na wani lokaci tsakanin Maroko da Sifaniya kan wasu kananan tsibiran da ke kusa da mashigin ruwan, kamar tsibirin Leila (Tora). Duk da cewa wadannan rigingimu ba su rikiɗe zuwa manyan faɗa a wannan lokacin ba.

Mashigin ruwan Panama

Mashigin ruwan Panama yana cikin ƙasar Panama ne kuma ya haɗa Tekun Caribbean (wanda shi ne Tekun Atlantika) da Tekun Pasifik, inda ya rage nisan da ke tsakanin gabas da yammacin duniya.

Ana ɗaukar wannan magudanar ruwar a matsayin ɗaya daga cikin manyan ayyukan da aka tsara su da kyau, saboda da ba da damar manyan jiragen ruwa su ratsa tsakanin tekunan biyu, kuma yana ba da gudummawa sosai wajen rage lokutan tafiye-tafiye a saman teku da farashin sufuri.

Wannan magudanar ruwa na taka muhimmiyar rawa a harkokin cinikayyar ƙasa da ƙasa, musamman a tsakanin ƙasashen Amurka da Asiya, kuma a baya-bayan nan an yi ta faɗaɗa ta domin kara karfinta a fannin cinikayyar ƙasa da ƙasa.

An fara aikin mashigar ruwan Panama ne a shekara ta 1881 a ƙarƙashin gwamnatin Faransa wanda Ferdinand de Lesseps ya jagoranta, a lokacin da Panama ke haɗe da Colombia. Sai dai, aikin ya tsaya cak, inda daga baya aka dakatar da shi, kafin Amurka ta ci gaba bayan da ta goyi bayan ballewar Panama daga Colombia a shekarar 1903.

An kammala mashigar kuma an buɗe ta a hukumance a ranar 15 ga watan Agusta, 1914, a lokacin shugabancin Woodrow Wilson. Shugaban Panama a lokacin shi ne Belisario Porras Barahona, tsakanin 1912 zuwa 1916.

Bayan da aka buɗe mashigar ruwar ta Panama, ta kasance karkashin kulawar Amurka tsawon shekaru, lamarin da ya haifar da tashe-tashen hankula a cikin gida da zanga-zanga a ƙasar Panama, musamman abubuwan da suka faru a shekarar 1964, inda aka yi ƙazamin fada tsakanin 'yan kasar ta Panama da sojojin Amurka.

A cikin shekarun 1970, an cimma yarjejeniyar ba Panama iko da mashigar, inda ta fara aiki a hukumance a shekarar 1999. Duk da kawo karshen taƙaddamar 'yancin kai, tashar ruwar na fuskantar ƙalubale na siyasa da na tattalin arziki, wanda a wasu lokuta ke shafar ayyukanta.

Shugaban Amurka Donald Trump ya soki yadda aka bai wa Panama iko da magudanar ruwar, yana mai cewa matakin da Amurkar ta ɗauka bai dace ba.

Mashigin Malacca

Mashigin Malacca da ke tsakanin Malaysia da Indonesiya, na ɗaya daga cikin manyan hanyoyin teku a duniya, wanda ya hada tekun Indiya da tekun Kudancin China. Mashigar ita ce babbar hanyar jigilar kayayyaki da kasuwanci tsakanin Gabas ta Tsakiya da Gabashin Asiya.

Ita ce hanya mafi gajarta ta jigilar man fetur da kayayyaki zuwa manyan ƙasashe irin su China da Japan, wanda hakan ya sa ya zama wuri mai muhimminci ga jigilar kayayyaki a duniya, kuma ƙasashe da dama sun dogara da wannan hanya wajen tabbatar da safarar albarkatun ƙasa da makamashi.

Duk da mahimmancinsa, mashigar Malacca na fuskantar ƙalubalen tsaro kamar fashin teku da cunkoso.

Mashigin Bosphorus da Dardanelles

Mashigin ruwa na Bosphorus yana Istanbul na ƙasar Turkiyya ne kuma ya raba nahiyoyin Asiya da Turai. Shi ya haɗa Tekun Maliya da Tekun Marmara.

Mashigin na taka muhimmiyar rawa wajen jigilar mai, iskar gas da kayayyaki daga Tekun Maliya zuwa kasuwannin duniya. Haka kuma, wata babbar hanya ce ta safarar kasuwanci da na soja, kuma Turkiyya ce ke da iko wajen gudanar da hada-hada a yankin bisa yarjejeniyar ƙasa da ƙasa.

Mashigin Dardanelles kuma yana cikin Turkiyya inda ya haɗa Tekun Aegean (wanda ke cikin Tekun Bahar Rum) da Tekun Marmara a Turkiyya.

Mashigin tekun Turkiyya ta fuskanci ƙalubale a lokacin yaƙin duniya na ɗaya, lokacin da dakarun kawance suka yi yunƙurin ƙwace mashigar.

Mashigin Kil

Kogin Kiel yana arewacin Jamus a jihar Schleswig-Holstein, kuma ya haɗu da Tekun Baltic da Tekun Arewaci, wanda kuma ɗan gajeren hanyar teku ne da jiragen ruwa na Turai ke bi.

Ana amfani da mashigin ruwar sosai wajen zirga-zirgar jiragen ruwa a nahiyar Turai, musamman tsakanin tashoshin jiragen ruwa da masana'antu, wanda hakan ya sa ya ke da muhimmanci wajen tallafawa tattalin arzikin Turai da kuma sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

An fara aikin gina mashigin ruwa na Kiel ne a shekarar 1887 a lokacin mulkin marigayi Kaiser Wilhelm na I, inda aka kammala shi kuma aka bude shi a hukumance a shekarar 1895 a zamanin Kaiser Wilhelm na biyu, wanda ya jagoranci ƙaddamar da aikin.

Magudanar tana da matuƙar muhimmanci ga sojoji a lokacin yaƙe-yaƙen duniya na biyu ga jiragen ruwan Jamus. Bayan yaƙin duniya na ɗaya, an sanya takunkumin ƙasa da kasa a kan mashigin karkashin yarjejeniyar Versailles.

Daga baya, magudanar ruwa ta samu cikakken 'yancin kai daga Jamus, amma ta ci gaba da zama ƙarƙashin ƙasashen Turai saboda muhimmancinta, musamman a lokacin yaƙin cacar baka.