Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

KAI TSAYE, Yaƙin Iran da muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 09/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

A'isha Babangida, Muslim Muhammad Yusuf

  1. Ana gangamin cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei

    Iraniyawa da dama suna gudanar da gangami a birane daban-daban na ƙasar don tunawa da cika kwana 40 da kisan jagoran Iran, Ayatollah Ali Khamenei kamar yadda gidan talabijin na gwamnatin ƙasar ya ruwaito.

    A cikin hotunan, za a ga ɗimbin magoya bayan gwamnati na nuna alhini a titunan biranen Hamedan da Yazd da Khorramabad da Shiraz da Yasuj da dai sauransu.

    An kashe Ali Khamenei ne a ranar farko ta yaƙin Amurka da Isra'ila da Iran a ranar 29 ga Maris kuma har yanzu ba a yi jana'izarsa ba a hukumance. make the first paragraph tally with the headline

  2. Amurka ta umarci jami'anta su fice daga Najeriya

    Amurka ta umarci jami'anta na diflomasiyya su fice daga Abuja, babban birnin Najeriya, yayin da tsaro ke ''ƙara taɓarɓarewa'' a ƙasar.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce ta umarci ma'aikatan gwamnatin Amurka a ofishin waɗanda aikinsu bai zama wajibi ba, da kuma iyalansu su bar ƙasar.

    Haka kuma gwamnatin Amurkar ta shawarci ƴan ƙasarta da ke so ko kuma suke shirin zuwa Najeriya da su sake shawara, saboda matsalar tsaro - wadda ta haɗa da satar mutane da ayyukan ƙungiyoyin ƴan bindiga.

    A jiya Laraba ne hukumomin Najeriyar suka fara shari'ar sama da mutum 500 da ake zargin su da hannu a hare-haren ƴan bindiga, da suka yi sanadiyyar mutuwar dubban jama'a musamman a arewacin ƙasar.

  3. Yarjejeniyar tsagaita wuta ta haɗa da Lebanon - Ƙasashen Turai

    Ƙasashen Turai sun ce wajibi ne Lebanon ta kasance cikin yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Iran.

    Ministan harkokin waje na Birtaniya Yvette Cooper ya bayyana hare-haren da Isra'ila ta kai kan Hezbollah a Lebanon a matsayin mummunan ɓarna - sannan ya ce ƙin amincewa da Lebanon a cikin yarjejeniyar zai iya dagula lamurra da kuma rikita yankin.

    Ma'aikatar lafiya ta Lebanon ta ce harin da aka kai ƙasar ya kashe sama da mutum 180 a ranar Laraba.

    Masu ceto na ci gaba da neman wadanda ke da sauran numfashi a ɓaraguzan gine-ginen da suka rushe.

    Isra'ila ta ce an yi wa Hezbollah mummunar illa.

  4. Amurka ta karya yarjejeniyar tsagaita wuta - Iran

    Iran ta zargi Amurka da karya yarjejeniyar tsagaita wuta bayan Isra'ila ci gaba da kai hare-hare kan Hezbollah a ƙasar Lebanon.

    Shugaban majalisar dokokin Iran Mohammed Bagher Ghalibar ya ce an karya tanade-tanaden sassa daban-daban na sharuddan yarjejeniyar da Iran ta gabatar.

    A matsayin martani, mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya nanata cewa babu Lebanon a cikin yarjejeniyar da aka cimma.

    Ya kuma ce bai kamata Iran ta bari yarjejeniyar ta lalace ba a sanadiyyar Lebanon.

  5. Sojojin Amurka za su ci gaba da kasancewa a kusa da Iran - Trump

    Shugaban Amurka Donald Trump ya ce sojojin ƙasarsa za su ci gaba da zama a kusa da Iran, yayin da ake nuna fargaba kan yuwuwar durkushewar yarjejeniyar zaman lafiya.

    Shugaban ya ce dakarun za su zauna a yankin har zuwa lokacin abin da ya kira bin yarjejeniyar sau da kafa.

    Ya ce muddin ba a yi haka ba to kuwa hakan ka iya sa Amurka ta koma kai hari - wanda a kalamansa ya bayyana da cewa - zai fi na baya girma da kuma illa.

    Iran ta ce, ci gaba da kai harin da Isra'ila ke yi a kan Hezbollah a Lebano saba wa yarjejeniyar ne, bayan sojin Isra'ila sun kashe ko raunata sama da mutum dubu daya a jiya Laraba.

    Wannan wani mawuyacin hali ne ga Iran, wadda ba za ta yi watsi da Hezbollah ba wadda ta shiga yakn domin mara mata baya Iran din ta ce za ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz.

    Amma kuma jami'an Amurka sun ce batun Lebanon ba ya cikin yarjejeniyar.

  6. Barka da warhaka!

    Barka da zuwa shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa, inda muke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da Amurka da Isra'ila da kuma muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya a wannan rana ta Alhamis 9 ga watan Afrilun 2026.

    Za ku iya yin sharhi kan labaran da muke sakawa a shafukanmu na sada zumunta: facebook, X, Instagram da kuma YouTube.

    Sannan ku shiga zaurenmu na BBC Hausa WhatsApp domin samun labarai da ɗumi-ɗumi.