APC na sake nazarin jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin sake nazarin kwamitin yaƙin neman zaɓen jam'iyyar APC na zaɓen shugaban ƙasa na 2027, ce-ce-ku-ce da suka biyo bayan fitar da jerin sunayen da aka fitar.
Wata majiya daga cikin masu ruwa da tsaki a jam'iyyar APC da ke cikin kwamitin ta tabbatar wa BBC cewa an umurci shugabannin jam'iyyar da fadar shugaban ƙasa da su sake duba jerin sunayen ne saboda kura-kuran da aka samu, ciki har da sanya sunayen wasu jami'an gwamnati da ake ganin bai dace su kasance cikin tsarin yaƙin neman zaɓen jam'iyya ba.
Matakin ya zo ne sa'o'i kaɗan bayan fadar shugaban ƙasa ta sanar da kwamitin mutum 223, inda aka naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdul'aziz Yari, a matsayin Darakta-Janar.
Daga cikin sunayen da suka janyo tambayoyi akwai Betta Edu, tsohuwar ministar jin ƙai da rage talauci, wadda aka dakatar daga mukaminta a 2024 bayan zargin badakalar kuɗi.
Akwai kuma wasu manyan ƴan jam'iyyar da ake ganin ya kamata su kasance cikin kwamitin ba a samu sunayensu ba ciki har da gwamnoni.
Daga cikinsu akwai tsohon gwamnan Filato, Simon Lalong, wanda ya jagoranci kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Haka kuma babu sunan Festus Keyamo, wanda yana ɗaya daga cikin masu magana da yawun kwamitin yaƙin neman zaɓen APC a 2023.
Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, wanda ya jagoranci ɓangaren hulɗa da masu ruwa da tsaki a kwamitin 2023, shi ma ba ya cikin jerin farko.
Sai dai majiyar ta shaida wa BBC cewa, duk da wannan umarnin, ba a janye naɗin Sanata Abdul'aziz Yari a matsayin Darakta-Janar ba, amma za a sake nazari domin yin gyare-gyare da sake fitar da sabon jerin sunayen.