Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 16/10/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na ranar Juma'a 16 ga watan Oktoban 2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Isiyaku Muhammed da Badriyya Kalarawi

  1. Biya ya naɗa sabon shugaban majalisar tsarin mulkin Kamaru

    Shugaban ƙasar Kamaru, wanda ya daɗe yana mulki, Paul Biya, ya naɗa sabon shugaban Majalisar Tsarin Mulkin ƙasar, bayan rasuwar tsohon shugaban wannan muhimmiyar hukuma.

    An naɗa Rémy Nama, wanda aka bayyana a matsayin gogaggen alƙali, domin jagorantar majalisar mai mambobi goma sha ɗaya wadda ke da alhakin duba ko dokoki sun yi daidai da kundin tsarin mulkin ƙasa, da kuma yanke hukunci kan sahihancin zaɓe da kuri'un raba gardama.

    Kafin wannan naɗi, Rémy Nama yana aiki ne a Babban Sakatariyar Fadar Shugaban Ƙasa.

    Da yake magana ta tashar talabijin ta PRCTV, wadda ke watsa shirye-shirye daga Fadar Shugaban Ƙasa, Nama ya ce:

    "Ina cike da godiya da jin daɗin wannan amana, kuma zan iya tabbatar masa (Shugaba Biya) cewa zan yi duk mai yiwuwa domin cika amincewar da ya nuna gare ni."

    Ya maye gurbin Clement Atangana, mai shekaru 85, wanda ya rasu a ranar 4 ga Oktoba 2026 a birnin Paris bayan fama da jinya.

    Majalisar Tsarin Mulkin Kamaru na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bin kundin tsarin mulki da kuma sa ido kan sahihancin zaɓuɓɓuka da sauran muhimman matakan dimokraɗiyya a ƙasar.

  2. An dakatar da DPO bisa zargin barin ƴan ƙungiyar asiri su gyara ofishin ƴansanda

    Rundunar ƴanSandan Najeriya, reshen Jihar Rivers, ta cire manyan jami’anta biyu masu kula da yankin Abuloma bayan sun bari wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun gyara wani ofishin ‘yan sanda na yankin.

    Hakan ya biyo bayan wani bidiyo da ya bazu a shafukan sada zumunta, inda aka ga wasu matasa da ake zargin mambobin wata ƙungiyar asiri ne a gaban ofishin ƴansanda da suka yi wa gyara.

    A cikin wata sanarwa da jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar ‘yan sandan jihar, Grace Iringe-Koko, ta fitar, ta ce rundunar ta bayyana bidiyon a matsayin abin damuwa da tayar da hankali.

    "Bidiyon ya taɓa mutunci, da ɗa’a da ƙa’idojin aikin Rundunar ƴansandan Najeriya, ko kuma ya ba kungiyoyin asiri da ake zargi ko wasu ƙungiyoyi masu aikata laifi wata irin karɓuwa ko halaccin da ba su dace da shi ba."

    Sanarwar ta ƙara da cewa: ''Ofisoshin ƴansanda cibiyoyin gwamnati ne na kare rayuka da dukiyoyin al’umma da tabbatar da bin doka da oda, don haka bai kamata su zama wuraren da ƙungiyoyin masu aikata laifi za su yi amfani da su wajen neman karɓuwa ko tasiri a idon jama’a ba."

    An yi wa DPO mai kula da sashen ƴansandan Abuloma da kuma jami’in da ke kula da ofishin da abin ya shafa tambayoyi, an ɗauki matakin ladabtarwa hakan ya kai ga an cire su daga mukamansu har sai an kammala bincike.

    A cikin bidiyon, an ga mutanen suna sanye da hula da riguna masu launin Ja, yayin da wasu ke sanye da fararen riguna da baƙaƙen wando, tare da ɗaura jan mayafi a kai.

    Ana kuma jin suna furta kalmomi da taken da mutane da dama ke dangantawa da yarukan ƙungiyoyin asiri.

    Bidiyon ya kuma nuna yadda mutanen da wasu jami’an ƴansanda masu sanye da kayan aiki suka ɗauki hotuna tare, kafin daga bisani su shiga cikin ofishin ƴansandan da aka gyara domin duba aikin da aka yi.

    Sai dai sashen turancin buroka na BBC News Pidgin, ya ce bai samu tabbataccen bayani kan matasan mambobin wata ƙungiyar asiri ne ba.

  3. Shugaba Hassan na Somaliya ya kai ziyara inda ake haƙo man fetur

    A cikin wata sanarwa ta haɗin gwiwa da kuma hotuna da aka wallafa a shafin Facebook na Fadar Shugaban Ƙasar Somaliya, an bayyana cewa Shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya kai ziyara don duba jirgin haƙo mai na Turkiyya mai suna Çağrı Bey, wanda ke gudanar da ayyukan bincike da haƙo man fetur a ruwan Somaliya.

    Sanarwar ta ce: "Shugaban ƙasar ya saurari rahoto daga masana da jami'an da ke cikin jirgin kan aikin da aka gudanar, sakamakon da aka samu a ayyukan haƙo ɗanyen man fetur da kuma nasarorin farko da suka fara bayyana, tabbatar da albarkatun man fetur da ke cikin ruwan Somaliya."

    Jirgin Çağrı Bey ya isa Somaliya ne a tsakiyar wannan shekarar, domin fara ayyukan binciken mai a tekun ƙasar.

    A lokacin da jirgin ya iso, Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya ya bayyana zuwansa a matsayin "wani tarihi mai muhimmanci", yana mai cewa hakan ya nuna fara aikin haƙon mai a teku na farko da Turkiyya ke gudanarwa a ƙasashen waje.

    Wannan mataki na daga cikin aikin haɗin gwiwar tattalin arziki da makamashi tsakanin Somaliya da Turkiyya, yayin da Somaliyar ke ƙoƙarin ganowa da bunƙasa albarkatun man fetur da iskar gas da ke cikin yankunan ruwanta.

  4. Ƙudurin dokar ƴansandan jihohi na gab da isa majalisar dokokin Najeriya

    Fadar Shugaban Najeriya ta bayyana cewa ƙudirin dokar ƴansandan jihohi da ake shiryawa ya kusan kammaluwa, kuma ana dab da miƙa shi ga Majalisar Dokoki ta Ƙasar.

    Babban Shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa Femi Gbajabiamila ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, inda ya ce wani kwamitin aiki da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kafa ya kammala muhimmin ɓangaren aikin tsara dokar.

    Sai dai gyaran kundin tsarin mulkin da ake buƙata domin amincewa da kafa 'yansandan jihohi na fuskantar wani ƙalubalena daban.

    Rahotanni sun nuna cewa ƙananan majalisun dokokin jihohi ne kaɗai suka amince da gyaran kundin tsarin mulkin, alhali ana buƙatar aƙalla jihohi 24 su amince da shi kafin ya samu nasara kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

    Fadar Shugaban Ƙasa ta ce har yanzu ana ci gaba da tuntuɓa da gwamnonin jihohi domin samun goyon baya ga wannan gyara, yayin da kuma ake warware sauran batutuwan da suka rage a cikin ƙudirin dokar da ake shiryawa.

    Idan aka amince da gyaran kundin tsarin mulkin da kuma Ƙudirin dokar, hakan zai iya bai wa jihohi damar kafa nasu rundunonin ƴansanda domin taimakawa wajen inganta tsaro da magance matsalolin tsaro a matakin jiha da na ƙananan hukumomi.

  5. Ƙofar jirgi ta ɓalle yayin da yake sararin samaniya a Abuja

    Wani ƙaramin jirgin sama mai zaman kansa ya koma filin jirgin da ya tashi daga Abuja domin yin saukar gaggawa, bayan da ƙofarsa ta ɓalle yana cikin sararin samaniya.

    Matuƙin jirgin ne ya aika saƙon gaggawa ga hukumomin kula da zirga-zirgar jiragen sama, inda ya nemi izinin komawa domin sauka.

    Lamarin ya faru ne ranar Alhamis, 15 ga Oktoba, jim kaɗan bayan jirgin samfurin CL60 ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, a kan hanyarsa ta zuwa Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammed da ke Legas.

    Hukumar Binciken Haɗurra ta Najeriya (NSIB) ta ce ta fara bincike domin gano musabbabin lamarin, kuma ta gano ƙofar jirgin da ta faɗi.

  6. Kenya ta tabbatar da mutum na uku da ya kamu da Ebola

    Ƙasar Kenya ta tabbatar da samun mutum na uku da ya kamu da cutar Ebola, nau'in Bundibugyo.

    Sabuwar mai ɗauke da cutar wata mata ce mai shekaru 65, ta na daga cikin waɗanda suka yi mu'amala da mutane biyu da aka tabbatar sun kamu da cutar, kuma an killace ta tun kafin a tabbatar da ta kamu da cutar aka killace ta.

    Jami'an lafiya sun ce ana ci gaba da sanya ido kan duk mutanen da suka yi hulɗa da masu ɗauke da cutar domin hana yaɗuwarta.

    Tabbatar da wannan sabon lamari ya ƙara yawan waɗanda aka tabbatar sun kamu da Ebola nau'in Bundibugyo a Kenya zuwa mutum uku.

  7. Yahudawa sun kai wa Falasɗinawa hari a yammacin kogin Jordan

    Wasu yahudawa ƴan kama wuri zauna, a yamma da gaɓar kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, sun kai hari kan Falasɗinawa manoma da suka je gonakinsu domin girbe Zaitun.

    Yahudawan sanye da baƙaƙen kaya, sun rufe fuskokinsu, sun dinga dukan mazauna ƙauyen, suna jifansu da duwatsu, sannan suka ƙone wasu itatuwan zaitun a ƙauyen Abu Falah, kusa da Nablus.

    Mutum biyu ne suka jikkata, an kuma kai su asibiti ɗaya daga cikinsu wani ɗan jarida ne ɗan ƙasar Amurka, wanda ya je yankin domin ba da rahoto kan aikin girbin zaitun da manoman ke yi.

    A cikin 'yan makonnin nan, hare-haren da yahudawan ke kai wa Falasɗinawa ya ƙaru a yammacin kogin Jordan.

    A na ta bangaren, gwamnatin Isra'ila ta yi Allah wadai da waɗannan hare-hare, amma masu sukar gwamnati na cewa ba a ɗaukar isassun matakan taka mu su birki shi ya sa su ke cin karensu babu babbaka.

  8. Tinubu ya naɗa sabbin kwamishinonin hukumar zaɓe guda shida

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya naɗa sabbin Ƙwamishinonin Ƙasa huɗu da kuma sabbin Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi biyu domin cike guraben da ake da giɓinsu a cikin Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC).

    Mai Bai Wa Shugaban Shawara na Musamman kan harkokin yaɗa Labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma'a, ya ce naɗin nasu zai fara aiki ne bayan Majalisar Dattawa ta tantance da amincewa da su.

    An sake naɗa Dr. Bala Bila a matsayin Kwamishinan Ƙasa mai wakiltar yankin Arewa maso Gabas.

    Fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana sunayen sababbin Kwamishinonin Ƙasa kamar haka: Farfesa Mustapha Aliu, wanda zai maye gurbin Farfesa Abdullahi Zuru a matsayin wakilin yankin Arewa maso Yamma.

    Bashir Muhammed Umar, wanda zai maye gurbin Farfesa Muhammad Adamu a matsayin wakilin yankin Arewa ta Tsakiya.

    Haka kuma, Shugaba Tinubu ya zaɓi Misis Oluwatoyin Babalola, wadda ke matsayin Kwamishiniyar Zaɓe ta Jihar Osun, domin ta zama sabuwar Kwamishiniyar Ƙasa mai wakiltar yankin Kudu maso Yamma.

    Za ta maye gurbin Farfesa Cornelius Ajayi, wanda wa’adinsa zai ƙare a ranar 24 ga Oktoba 2026.

    Sabbin Kwamishinonin Zaɓe na Jihohi biyu kuwa su ne: Dr. Samuel Akinjide Akinleye, tsohon Babban Sakataren Gwamnati, wanda zai wakilci Jihar Ekiti.

    Zahradden Basiru Sanusi daga Jihar Jigawa, wanda zai maye gurbin Farfesa Saidu Ahmed Babura.

    Shugaba Tinubu ya buƙaci Majalisar Dattawa ta gaggauta tantancewa da amincewa da waɗannan mutane saboda shirye-shiryen da ake yi na zaɓukan gama gari da za a gudanar a watan Janairu mai zuwa.

  9. Iran ta sanar da sabbin sharuɗɗan buɗe Mashigar Hormuz

    Mai magana da yawun rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya danganta sake buɗe mashigar Hormuz da ficewar Amurka daga yankin, da gargadin idan sojojin Amurka suka ci gaba da kasancewa a yankin, za a kore su.

    Akraminia ya wallafa sako a shafinsa na X inda ya ke cewa;

    "Idan Amurka ta fice daga yankin, za a buɗe mashigar Hormuz, za a kafa tsarin tsaro na bai ɗaya tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin, kuma tattalin arzikin duniya zai inganta. Ko da ba ta fice ba, za mu fitar da ita."

    Kakakin sojin na Iran ya kuma zargi Amurka da haddasa rashin tsaro a gabashin Hormuz. Ya bukaci masu jiragen ruwa su bi hanyar da rundunar sojin Iran ta tanada ga jiragen da ke son wucewa ta wannan hanyar.

    Ya yi ikirarin cewa jiragen da suka bi wannan hanya za su kasance cikin aminci.

    Wadannan kalamai na zuwa ne a daidai lokacin da hare-hare kan jiragen kasuwanci ke ƙaruwa a ciki da kewayen Hormuz, lamarin da ya janyo raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa a wannan muhimmin wuri.

    A ɓangare guda kuma, Amurka na ci gaba da ƙaƙaba takunkumin hana fitar da ɗanyen man fetur na Iran. Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, fitar da ɗanyen man Iran ta ruwa ya ragu a watan Oktoba, kamar yadda kamfanin samar da bayanai na Vortexa ya bayyana.

  10. An kuɓutar da masu shaye-shaye da ake azabtarwa a Afurka ta Kudu

    An kama wani limamin Coci da matarsa a Afirka ta Kudu bayan an gano mutane kusan 200, wasu daga cikinsu a ɗaure da sarƙoƙi, ana tsare da su a wani wurin gyaran halin masu ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da ake zargin ana tafiyarwa ba, bisa ƙa'ida ba a arewa maso gabashin ƙasar.

    An gano cibiyar, wadda ake gudanarwa daga wata coci a lardin Mpumalanga, a yayin wani samame da jami'an gwamnati suka kai yankin ranar Alhamis.

    Mahukunta sun ce sun tarar da mutanen cikin mummunan yanayi, an ɗaure su kamar dabbobi. An samu wasu daga cikin mutanen da ke wurin dauke da raunuka a jikinsu gaba ɗaya, yayin da wasu kuma aka same su a ɗaure da sarƙa manne da juna.

    Tun daga lokacin, ƴan sanda sun gurfanar da ma'auratan da ke gudanar da cibiyar kan zargin garkuwa da mutane, amma sun ce ana iya ƙara wasu tuhume-tuhume a kansu nan gaba.

    Kawo yanzu limamin Cocin da Maidakinsa ba su ce uffan kan zarge-zargen da akai mu su.

    Cikin waɗanda aka samu ɗaure har da ƴan mata ƙanana yara ƙasa da shekara 15 da 16.

    A cikin ƴan shekarun nan, cibiyoyin da ake kafawa da sunan na gyaran masu shaye-shaye ba bisa ƙa'ada ba na kara yawaita a Afirka ta Kudu, yayin da ita ma matsalar amfani da miyagun ƙwayoyi ke ƙaruwa a ƙasar.

  11. An kama jagoran ƙungiyar Cockroach Janta Party a India

    An kama wanda ya kafa Ƙungiyar zanga-zangar "Cockroach" a Indiya, Abhijeet Dipke, a birnin Delhi gabanin wata sabuwar zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a tsakiyar babban birnin ƙasar.

    Kamen nasa ya biyo bayan gargadin da ƴan sanda suka yi na hana gudanar da zanga-zangar ranar Juma'a, an jibge dubban jami'an tsaro a sassan birnin domin hana taruwar masu zanga-zangar.

    Ƙungiyar matasa ta Dipke mai suna Cockroach Janta Party (CJP) tana neman shugaban hukumar zaɓen Indiya ya yi murabus, kan zargin an yi maguɗi wajen tsara jerin sunayen masu kaɗa kuri'a. Sai dai Hukumar Zaɓe ta Indiya ta musanta wannan zargi.

    Kungiyar ta bukaci magoya bayanta su hallara a wani fili na shakatawa da ke Connaught Place, ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin kasuwanci mafi cunkoso a Delhi, domin ɗaga tutar Indiya.

    Sai dai adadin mutanen da suka halarci taron ya yi ƙasa da na zanga-zangar CJP da aka gudanar a baya, ko da yake ana ganin yawan masu zuwa na ƙaruwa a hankali.

    Wakilin BBC ya shaida cewa an kama wasu matasa masu zanga-zangar tare da tura su cikin motar ƴan sanda, ciki har da wasu mata da aka kama tun da farko.

  12. Gwamnatin Habasha ta kafa gwamnatin riko a yankin Tigray

    Gwamnatin Habasha, ta kafa gwamnatin riƙo a yankin Tigray da ke arewacin ƙasar, bayan maƙwannin da aka ƙwashe ana gwabza faɗa tsakanin sojojin gwamnati da dakarun ƴan tawaye.

    Wannan na zuwa ne maƙwanni biyu bayan da sojojin gwamnati suka sake ƙwace babban birnin yankin, Mekelle, ya yin da dakarun Eritrea suka kutsa yankin na Tigray.

    An ɗora wa sabuwar gwamnatin riƙon alhakin maido da tsaro, da sake gina kayayyakin more rayuwa da yaƙi ya lalata, da kuma shirya zaɓukan yankin.

    Yankin Tigray ne ya kasance cibiyar wani mummunan yaƙi tsakanin sojojin gwamnatin Habasha da mayaƙan 'yan tawayen yankin Tigray daga shekarar 2020 zuwa 2022.

    An kawo ƙarshen rikicin a hukumance ta hanyar yarjejeniyar zaman lafiya, amma har yanzu akwai saɓani kan ikon siyasa, da ƙwance damarar mayaƙa, da kuma dawowar mutanen da suka tsere daga muhallansu.

    Wa'adin watanni shida na sabuwar gwamnatin riƙon ya ɗisa alamar tambaya kan ko sauyin mulki ta hanyar zaɓe zai samu karɓuwa a wajen al'ummar Tigray.

    A halin yanzu kuma, rikice-rikicen da ke ƙaruwa tsakanin Habasha da maƙwabciyarta Eritrea na ƙara tayar da fargabar cewa sabon yaƙi ka iya ɓarkewa tsakanin Habasha da makofciyarta, hakan zai ƙara haddasa zaman doya da manja, da rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin kusurwar ta Afurka.

  13. Iraq ta yi asarar sama da biliyan 60 a yaƙin Gabas ta Tsakiya

    Ministan Harkokin Wajen Iraq, Fawad Hussein, ya ce asarar da ƙasarsa ta yi sakamakon yaƙin Gabas ta Tsakiya ta kai kusan dala biliyan 60.

    Ya ce yaƙin ya kuma haifar da Iran ta ƙaƙaba wa zirga-zirga takunkumi a Mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar makamashi a duniya.

    Ya bayyana hakan ne a yayin ziyararsa zuwa birnin Rome, inda ya gana da Ministan Harkokin Wajen Italiya, Antonio Tajani.

    Iraq, wacce mamba ce ta Ƙungiyar Ƙasashe Masu Fitar da Man Fetur (OPEC), tana samar da kusan ganga miliyan huɗu na man fetur a kowace rana kafin barkewar yaƙin.

    Daga cikin wannan adadi, ana fitar da kusan ganga miliyan 3.5 a rana zuwa ƙasashen waje.

    Mafi yawan waɗannan fitarwa na fitowa ne daga kudancin Iraki ta Mashigin Hormuz.

  14. Fasahar zamani ta taimaka wajen tsarawa da gudanar da aikin Hajji - NAHCON

    Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Najeriya (NAHCON), Ambasada Ismail Abba Yusuf, ya halarci taron ƙasa da ƙasa karo na takwas na Asusun Hajji (IHFF 2026) da aka gudanar a birnin Jakarta na ƙasar Indonesiya.

    Taron, wanda Hukumar Kula da Kuɗaɗen Hajji ta Indonesiya (BPKH) ta shirya, ya tattaro masu tsara manufofi, masana harkokin kuɗaɗen Musulunci da shugabannin hukumomi daga ƙasashe daban-daban domin tattauna hanyoyin inganta gudanar da kuɗaɗen Hajji.

    Da yake jawabi a wani zaman tattaunawa na manyan baƙi, Ambasada Ismail Abba Yusuf ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomi da kuma amfani da fasahar zamani wajen kare tsarin gudanar da Hajji daga matsalolin tattalin arzikin duniya.

    Ya ce makomar gudanar da aikin Hajji za ta dogara ne kan yadda hukumomi za su rungumi sababbin dabaru da fasahohi domin tabbatar da ingantaccen amfani da kuɗaɗen alhazai, ba kawai ga aikin Hajjin shekara mai zuwa ba, har ma domin amfanin alhazan nan gaba.

    Shugaban NAHCON ya kuma bayyana aniyar hukumar na ƙara zuba jari a muhimman sassa da suka shafi harkokin Hajji, kamar masauki da sufuri, domin rage kuɗaɗen da alhazai ke kashewa yayin gudanar da ibadar.

    Mahalarta taron sun yaba da rawar da Najeriya ke takawa da kuma ƙoƙarin ta na ƙarfafa haɗin gwiwa da sauran ƙasashen Musulmi domin amfani da fasahar kuɗi ta zamani wajen inganta tsarin gudanar da Hajji.

    NAHCON ta bayyana cewa halartar taron wata muhimmiyar hanya ce ta bunƙasa tsare-tsaren gudanar da Hajji da suka dogara da fasaha da kuma samar da anfani mai ɗorewa ga alhazan Najeriya.

  15. Sai sojojin Amurka sun bar Gabas ta Tsakiya kafin mu buɗe mashigar Hormuz - Iran

    Kakakin rundunar sojin Iran, Mohammad Akraminia, ya ce buɗe Mashigar Hormuz zai dogara ne da ficewar Amurka daga yankin Gabas ta Tsakiya, yana mai gargaɗin cewa idan dakarun Amurka suka ci gaba da kasancewa a yankin, za a tilasta musu ficewa.

    A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X ranar 14 ga Oktoba, Akraminia ya ce: "Idan Amurka ta bar yankin, za a buɗe Mashigar Hormuz, tsaro na bai ɗaya zai tabbata tare da haɗin gwiwar ƙasashen yankin, sannan tattalin arzikin duniya zai inganta. Idan kuma ba ta tafi ba, za mu fitar da ita."

    Ya kuma zargi Amurka da haddasa rashin tsaro a gabashin mashigar inda ya buƙaci masu jiragen ruwa su bi hanyar da sojojin Iran suka tanada domin zirga-zirga a wannan muhimmiyar hanyar ruwa. A cewarsa, jiragen da suka bi wannan hanya za su kasance cikin aminci.

    Wannan na zuwa ne yayin da hare-hare kan jiragen kasuwanci a Mashigin Hormuz da kewaye suka ƙaru, lamarin da ya jawo raguwar zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin.

    Bayanan kamfanin sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa na Kepler sun nuna cewa jiragen dakon kaya biyar ne kawai suka ratsa mashigin a ranar Asabar da ta gabata, yayin da babu ko guda a ranar Lahadi. A makon da ya gabace ta kuwa, jirage 31 ne suka bi ta wannan hanya.

  16. Kada ku zaɓi ƴansiyasa mayaudara - Wike

    Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya bukaci ƴan Najeriya su guji ƴan siyasar da ya kira da masu neman mulki ta hanyar yaudara da amfani da batun ƙabila ko wariya domin cimma burinsu.

    Ya ce ya kamata jama'a su zaɓi shugabanni bisa ƙwarewa, adalci da ayyukan da suka yi wa al'umma, ba bisa ƙabila ko yanki ba.

    Wike ya jaddada cewa adalci da daidaito ba wai kawai game da wanda ke riƙe da mulki ba ne, "har ma da irin ci gaban da jama'a ke samu ta fuskar ayyukan yi, ilimi, lafiya, tsaro da ababen more rayuwa."

    Ya kuma gargaɗin cewa neman wakilci a gwamnati bai kamata a yi watsi da ƙwarewa ba wajen neman shiga harkokin shugabanci, yana mai kira da a gina tsarin siyasa da zai yi wa dukkan ƴan Najeriya aiki ba tare da nuna bambanci ba.

  17. An dakatar da gasar Golf a Saudiya saboda hare-haren Houthi

    Mahukunta gasar Asian Golf Tour sun sanar da dakatar da gasar Saudi International Golf Tournament zuwa wani lokaci da ba a kayyade ba, bayan harin da mayaƙan Houthi na Yemen suka kai filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa na Riyadh, wanda ya yi sanadiyar asarar rayuka.

    A makonnin baya-bayan nan, Houthi sun ƙaddamar da hare-hare kan filayen jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa da kuma cibiyoyin mai na Saudiya ta amfani da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuƙa.

    Aƙalla mutum 12 ne suka mutu yayin da sama da 300 suka ji raunuka a harin da aka kai kan filin jirgin saman Riyadh a karshen makon da ya gabata.

    A cikin wata sanarwa, Asian Golf Tour ta ce an yanke shawarar dakatar da gasar ne bayan nazarin matsalolin gudanarwa da na shirye-shiryen da suka taso sakamakon halin da ake ciki, tare da nufin tabbatar da cewa gasar ta ci gaba da kasancewa bisa ƙa'idodin da ake bukata a matakin duniya.

    Gasar, wadda Asusun Zuba Jari na Jama'a na Saudiya (PIF) ke ɗaukar nauyi, tana da jimillar kyautar dala miliyan biyar, kuma an shirya gudanar da ita ne daga ranar 18 zuwa 21 ga watan Nuwamba a filin wasan golf na Riyadh Golf Club.

    Shugaban Asian Golf Tour, Cho Min Thant, ya bayyana fatansa na cewa 'yan wasa za su samu damar halartar gasar a Riyadh a nan gaba idan yanayi ya daidaita.

    Har yanzu ba a sanar da sabon ranar da za a gudanar da gasar ba.

  18. Ba za mu yi amfani da makamin nukiliya kan Iran ba - Trump

    Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ba zai yi amfani da makamin nukiliya kan Iran ba.

    A wata hira da tashar Newsmax, Trump ya kuma jaddada cewa ba ya tunanin aike da dakarun ƙasa na Amurka zuwa Iran.

    Ya ce: "Ba zan yi amfani da makamin nukiliya ba. Ba mu da buƙatar yin hakan."

    Ya kuma yi magana kan abin da ake kira “Uwar Dukkan Bama-bamai” (Mother of All Bombs), wadda rahotannin CNN suka ce ana iya la'akari da ita a wasu hare-hare. Trump ya bayyana cewa wannan makami yana da matuƙar ƙarfi amma ba makamin nukiliya ba ne.

    Ya ce: "bam ne mai ƙarfin gaske, amma ba ta nukiliya ba ce."Trump ya kuma bayyana cewa Amurka na iya kai wani sabon hari kan cibiyoyin nukiliyar Iran, ciki har da wurin da ya kira Koh Kalang.

    A wani ɓangare na hirar, ya ce Amurka na tattaunawa da Rasha da China kan batun rage yawan makaman nukiliya a duniya.

  19. Ƴar Arewan da ke buga wa Najeriya ƙwallo

    Mu ma za mu iya fitowa mu taka leda kamar kowa, in ji Farida Abdulwahab, 'yar arewan da ke buga ƙwallon ƙafa a ƙungiyar Super Falcons ta Mata ta Najeriya, yayin da suke wasannin samun cancantar zuwa Gasar Olympics ta Duniya a 2027.

  20. China ta gargaɗi Isra'ila kan kafa matsugunan Yahudawa a Yammacin Kogin Jordan

    Gwamnatin China ta shaida wa Isra’ila cewa dole ne ta dakatar da kafa matsugunan Yahudawa a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, sannan kuma ta janye matakan da ta riga ta ɗauka a yankin.

    Kalaman sun biyo bayan ganawar da ministan harkokin wajen China, Wang Yi, ya yi da shugaban Isra’ila, Isaac Herzog, a yayin wani taro a Azerbaijan.

    A cewar sanarwar da hukumomin China suka fitar bayan ganawar, Mista Wang ya bayyana abin da aka yi wa Falasɗinawa a matsayin babban rashin adalci a tarihin wannan ƙarni.

    Ya kuma ce babban abin da ya kamata a bawa fifiko a yanzu shi ne a bude hanyoyin shiga Zirin Gaza gaba daya, domin hana abin da ya kira dakile mummunan halin jin kan da ake ciki a yankin.