Abubuwan da yarjejeniyar nukiliyar Amurka da Saudiyya ta ƙunsa

Asalin hoton, Win McNamee/Getty Images
Amurka da Saudiyya sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya da za ta bai wa masarautar Saudiyya damar bunƙasa shirinta na makamashin nukiliya.
Rahotanni sun ce yarjejeniyar za ta ba kamfanonin Amurka damar gina da kuma gudanar da tashoshin samar da makamashin nukiliya a cikin Saudiyya domin amfanin al'umma.
Haka kuma, ana ganin yarjejeniyar na iya bai wa Saudiyya damar tace sinadarin nukiliya da kanta domin amfani a injinan samar da makamashin nukiliya.
Sai dai wasu masana harkokin nukiliya da kuma tsoffin jami'ai a Isra'ila, babbar ƙawar Amurka a Gabas ta Tsakiya, sun nuna damuwa kan cewa irin wannan yarjejeniya na iya bai wa Saudiyya damar ƙera makamin nukiliya nan gaba.
Jaridar Wall Street Journal, wadda ita ce ta fara wallafa labarin, inda ta ce ana sa ran yarjejeniyar za ta ɗauki tsawon shekara 30.
Me ke cikin yarjejeniyar?

Asalin hoton, Bloomberg via Getty Images
- Yarjejeniyar nukiliyar da Amurka da Saudiyya suka cimma, yarjejeniya ce ta kasuwanci da za ta bai wa kamfanonin Amurka damar ginawa da kuma gudanar da tashoshin samar da makamashin nukiliya a Saudiyya, maimakon miƙa fasahar ga ƙasar.
- An shafe shekaru ana tattaunawa kan wannan yarjejeniya, inda tun farko ake kallonta a matsayin wani ɓangare na faɗaɗa dangantaka tsakanin Saudiyya da Isra'ila.
- Sai dai rahotanni sun ce Shugaban Amurka Donald Trump bai sanya amincewar Saudiyya da Isra'ila a matsayin sharadi ba a farkon yarjejeniyar, duk da cewa daga baya ya ce hakan zai zama dole kafin a tabbatar da ita.
- Rahotanni sun kuma ce Trump ya amince a bai wa Saudiyya damar tace sinadarin uranium a cikin ƙasarta, tare da karɓar wasu sharuɗɗan da za su iya takaita damar masu sa ido na ƙasa da ƙasa wajen binciken cibiyoyin nukiliyar ƙasar.
- Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce Amurka ba za ta ƙulla wata yarjejeniya da za ta ƙara haɗarin yaɗuwar makaman nukiliya ba. "Amurka ba za ta cimma yarjejeniya da kowace ƙasa ba wadda za ta iya haifar da haɗarin yaɗuwar makaman nukiliya," in ji shi.
- Ana kwatanta yarjejeniyar da wadda Amurka ta ƙulla da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) a shekarar 2009, wadda ta ƙunshi tsauraran bincike da kuma hana ƙasar samar da nata makamashin nukiliya.
- Ana sa ran Majalisar Dokokin Amurka za ta yi muhawara kan yarjejeniyar, sai dai ana ganin masu adawa da ita ba za su samu isassun ƙuri'u da za su hana ta wucewa ba.
- Yarima Mohammed bin Salman, ya taɓa cewa idan Iran ta mallaki makamin nukiliya, to Saudiyya ma za ta nemi mallakar irin wannan makami.
- CBS News ta ruwaito cewa, yarjejeniyar ta fi mayar da hankali ne kan samar da makamashin lantarki ta hanyar nukiliya.
- Bayanan Hukumar Makamashi ta Amurka (EIA) sun nuna cewa Saudiyya ta samar da kimanin terawatt awa 453 na wutar lantarki a shekarar 2023, inda kashi 62 ya fito daga iskar gas, kashi 38 daga man fetur.
- A halin yanzu Saudiyya ba ta da wata tashar samar da makamashin nukiliya, amma a watan Satumban 2023 ministan makamashin ƙasar ya bayyana aniyar gwamnati ta gina ta.
Dole Saudiyya ta amince da Isra'ila kafin yarjejeniyar nukiliya ta tabbata – Trump
Shugaban Amurka Donald Trump ya ce yarjejeniyar makamashin nukiliya da ƙasarsa ta ƙulla da Saudiyya ba za ta tabbata ba sai idan Riyadh ta amince da ƙasar Isra'ila ta hanyar shiga yarjejeniyar Abraham.
A wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Truth Social, Trump ya ce: "Yarjejeniyar makamashin nukiliya (ban da tace sinadaran nukiliya!)... ba kuma don amfanin soji ba, za ta samu sahalaewa ne kawai idan Saudiyya ta shiga yarjejeniyar Abraham."
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kalaman na Trump na zuwa ne bayan wasu masu sharhi sun nuna damuwa cewa yarjejeniyar na iya ƙara haɗarin yaɗuwar fasahar nukiliya a yankin Gabas ta Tsakiya, wanda tuni ke fama da rashin zaman lafiya.
Saudiyya dai ta sha bayyana cewa ba za ta shiga Yarjejeniyar Abraham ba, har sai an samar da tsari na dindin-din na kafa ƙasar Falasɗinu.
Ya zuwa yanzu, Saudiyya ba ta mayar da martani kan kalaman na Trump ba.
Mista Trump ya kuma ce yarjejeniyar ba za ta bai wa Saudiyya damar tace sinadarin uranium domin ƙera makaman nukiliya ba, saboda fargabar ƙarin yaɗuwar irin waɗannan makamai a Gabas ta Tsakiya.
Batun nukiliya na daga cikin manyan batutuwan da aka tattauna a rikicin da ya ɗauki watanni ana yi tsakanin Amurka da Isra'ila.
A shekarar 2020 ne Trump ya jagoranci ƙulla yarjejeniyar Abraham, wadda ta daidaita hulɗar diflomasiyya tsakanin Isra'ila da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Bahrain.
Daga baya kuma Sudan da Maroko su ma sun daidaita alaƙarsu da Isra'ila.
Abin da Amurkawa ke cewa
Wakilin jam'iyyar Democrat daga jihar California, Brad Sherman, ya ce ya kamata Amurka ta amince da yarjejeniyar ne kawai idan ta ƙunshi "irin tsauraran matakan kariya da aka sanya wa UAE".
A ƙarƙashin waccan yarjejeniya a 2009, ba a ba UAE damar tace sinadarin uranium da kanta ba.
"Shugaban ƙasar da ke yaƙi domin hana yaɗuwar makaman nukiliya a Gabas ta Tsakiya bai kamata ya sauƙaƙa irin wannan yarjejeniya ba saboda kawai kamfanonin Amurka za su ci riba." Sherman ya wallafa a shafinsa na X.
Shi kuwa ɗan majalisar Republican, Marlin Stutzman, ya shaida wa CNN cewa a halin yanzu ba shi da wata damuwa kan yarjejeniyar, amma yana son "ƙarin bayanan sirri" kafin ya yanke hukunci.
Ya ce: "Saudiyya ce ginshiƙin daidaito a Gabas ta Tsakiya."
Ya kuma bayyana Yariman Saudiyya, Mohammed bin Salman, a matsayin "abokin ƙasashen Yamma da Amurka."
Sai dai ɗan majalisar Democrat John Garamendi ya soki yarjejeniyar, inda ya ce: "Wannan mummunar manufa ce. Bai kamata mu taɓa yin irin wannan yarjejeniya ba."
Ya ƙara da cewa idan aka ba ƙasa damar tace uranium, hakan na iya ba ta damar ƙera makaman nukiliya, kuma wannan "abu ne mai haɗari."
Ƙasashen da ke da makaman nukiliya
Yarjejeniyar da Amurka da Saudiyya ke shirin ƙullawa ta samar da makamashin nukiliya ne, ba ƙera makaman nukiliya ba.
A halin yanzu, ƙasashe tara ne kawai aka sani da mallakar makaman nukiliya. Su ne, Amurka, Rasha, China, Birtaniya, Faransa, India, Pakistan, Koriya ta Arewa da Isra'ila.
Game da Isra'ila kuwa, mutane da dama na ganin tana da makaman nukiliya, sai dai gwamnatin ƙasar ba ta taɓa tabbatar ko musanta hakan a hukumance ba.

Asalin hoton, SIPRI Yearbook 2026/BBC
Yaushe aka fara tattaunawar nukilyar Saudiyya?
Tattaunawar tsakanin Amurka da Saudiyya kan samar da makamashin nukiliya na ta fara tun a shekarar 2008.
A zamanin shugaba George W. Bush, ƙasashen biyu sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya. A ƙarƙashinta, Amurka ta amince za ta taimaka wa Saudiyya wajen bunƙasa makamashin nukiliya, yayin da Saudiyya ta bayyana cewa za ta riƙa shigo da makamashin nukiliya daga waje, kuma ba za ta nemi mallakar fasahohin da ke da alaƙa da ƙera makaman nukiliya ba.
Tun daga lokacin, abubuwa da dama sun faru:
2017 zuwa 2019: Gwamnatin Amurka ta bai wa kamfanoni bakwai na Amurka izinin tattaunawa da Saudiyya kan ayyukan makamashin nukiliya.
2020: Hukumar Binciken Gwamnati ta Amurka (GAO) ta bayyana cewa ba a samu wani ci gaba tsakanin ƙasashen biyu ba saboda saɓanin ra'ayi kan wasu sharuɗɗa, ciki har da batun tace sinadarin uranium.
2022: Amurka da Saudiyya sun rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniyar fahimtar juna domin musayar bayanan fasaha da haɗin gwiwa kan tsaron makamashin nukiliya.
2023: Jaridar Wall Street Journal ta ruwaito cewa Amurka na nazarin yiwuwar kafa cibiyar tace uranium da kamfanonin Amurka za su gudanar a cikin Saudiyya.
Nuwamban 2025: Gwamnatin Donald Trump da Saudiyya sun sanya hannu kan wata sanarwar haɗin gwiwa da gwamnatin Amurka ta ce za ta shimfiɗa tubalin haɗin gwiwa na shekaru masu yawa kan makamashin nukiliya, wanda darajarsa za ta kai biliyoyin daloli.











