Mata na ƙorafi kan ɗabi'ar mazan Japan ta zuwa wurin aiki da gajeren wando

Asalin hoton, Getty Images
Yayin da ake ci gaba da fuskantar yanayin zafi, maza a Japan na ƙara rungumar ɗabi'ar amfani da gajeren wando fiye da kowane lokaci a baya.
Gwamnatin yankin Tokyo na ci gaba da karfafa wa ma'aikata gwiwa kan su jingine kayansu na zuwa aiki, irin su kwat da lakatayi, su riƙa amfani da kaya marasa nauyi kamar guntayen riguna da wanduna.
Gwamnar Tokyo, Yuriko Koike ta ƙaddamar da shrin sanya kaya marasa nauyi domin shan iska a watan Afurilu.
Yayin da aka kwashe kimanin wata huɗu ana ƙarfafa wa mutane gwiwa su riƙa amfani da guntun wando a ofis, ra'ayoyin mutane sun bambanta game da tsarin.
Yayin da wasu ke ganin cewa matakin ya dace domin mutane su riƙa shan iska, wasu na ganin cewa tsarin bai yi wa mata adalci ba.
Duk da cewa ba doka ba ce, amma a wuraren aiki akan so mata su sanya matsattsun dogayen wanduna a ciki, kafin dora wasu kayan a sama, domin gudun kada a riƙa ganin ƙafafunsu idan kayan da suka saka ya ɗaga.
Wasu daga cikin matan sun bayyana ɗabi'ar sanya gajerun wando da maza suka runguma a matsayin ana tursasa musu kallon ƙwaurin maza, cike da suma, wani abu da ake ta muhawara kansa a shafukan sada zumunta.






